DSS ta sako Editan Jaridar Almizan, Ibrahim Musa

Hukumar tsaro ta DSS ta sako Editan Jaridar Almizan, Malam Ibrahim Musa, wanda da farko take tsare da shi.

Ɗan uwan Editan, Abdullahi Usman ne ya sanar da hakan cikin sanarwar da ya fitar ran Juma’a.

Manhaja ta rawaito jami’an DSS sun tsare Ibrahim Musa a Babban Filin Jirgin Saman Aminu Kano da ke Kano da safiyar Larabar da ta gabata a lokacin da yake ƙoƙarin tafiya Umara a Saudiyya.

Bayanai sun ce an sako Editan a ranar Alhamis, kuma an maida masa dukkan takardunsa na tafiya.

Usman ya ce lafiya ƙalau Editan ya koma cikin ahalinsa da ‘yan da abokan arziki.