‘Yan sanda sun kama wanda ya ƙirƙiri muryar Tinubu ta bogi bayan makonni

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Rundunar ‘Yan sanda ta ce ta cafke wani Ifechukwu Dennis, wanda aka bayyana a matsayin wanda ya ƙirƙiri murya ta fasahar AI da aka baza a kafafen sada zumunta da sunan cewa ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu ce.

Kakakin Shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ne ya bayyana haka a ranar Alhamis ta kafar X.

A cewar Onanuga, jami’an ‘yan sanda na musamman ne suka kama wanda ake zargin akan wata ɗauka ta murya da ta haddasa gagarumar cece-kuce a kafafen yaɗa labarai.

“Tawagar IGP ta ‘crack’ ta kama Ifechukwu Dennis wanda ya samar da muryar ta bogi da ya yaɗa wa waɗanda yake son ruɗarwa a matsayin muryar Shugaba Tinubu,” inji Onanuga.

Wannan kamen ya kawo ƙarshen tsawon mako guda na cece-kuce wanda aka faro a ranar 27 ga watan Mayu 2026 a lokacin da wani bidiyon ɗan Soshiyal Mediya mai suna Martins Vincent Otse da aka fi sani da VeryDarkMan ya karaɗe kafafen sada zumunta akan al’amarin.

A faifan, wanda aka ƙirƙira ta fasahar AI, an ji wata murya mai kama da ta Tinubu da yake wasu kalamai na tunzura al’umma.

Daga cikin waɗannan kalaman da aka jingina wa shugaban akwai iƙirarin cewa da gangan aka samar da rashin tsaro a yankin Kudu maso Gabashin Nijeriya, shugaban ya tursasa wa ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023, Peter Obi janyewa gabanin zaɓen da kuma cewa bai damu da halin matsin da ‘yan Nijeriya ke fuskanta ba.

By Babaji

Leave a Reply