Gwamnatin Tarayya na shirin gaggauta samar da gidaje yayin da Minista Darma ya ziyarci Kano

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Gwamnatin Tarayya ta sake jaddada aniyarta na hanzarta samar da gidaje ga al’ummar Nijeriya, yayin da Ministan Gidaje da Raya Birane, Injiniya Muttagha Rabe Darma, ya kai ziyarar duba aikin Kano Renewed Hope City Housing Project, inda ya bayyana aikin a matsayin abin koyi wajen samar da gidaje masu araha ta hanyar haɗin gwiwar gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu.

Darma ya ce aikin na nuna yadda kyakkyawar haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da masu zuba jari masu zaman kansu zai taimaka wajen rage gibin gidaje da ake fuskanta a Nijeriya, tare da bunƙasa harkokin tattalin arziki a matakin jihohi.

Ministan ya bayyana hakan ne yayin da yake duba aikin gina gidaje 1,500 a Jihar Kano, inda ya tantance yadda aikin ke gudana tare da tattaunawa da masu aiwatar da aikin da sauran masu ruwa da tsaki kan jadawalin kammala aikin da kuma ingancin gine-ginen.

Ya ce ziyarar na daga cikin rangadin da ma’aikatar ke yi a faɗin ƙasar domin sa ido kan ayyukan gidaje na Gwamnatin Tarayya, da nufin tabbatar da cewa ana kammala su a kan lokaci tare da bin ƙa’idojin da aka amince da su.

A cewarsa, ma’aikatar na ƙara tsaurara sa ido kan ayyukan gidaje a sassan ƙasar domin rage jinkirin da ya dade yana kawo cikas ga manyan ayyukan gidajen gwamnati.

“Burinmu mai sauƙi ne; mu tabbatar an kammala waɗannan ayyuka a kan lokaci kuma cikin ƙa’idojin da aka tsara. Muna son ‘yan Nijeriya su fara amfana da waɗannan tsare-tsaren gidaje cikin gaggawa,” inji Darma.

Ya bayyana cewa shirin Renewed Hope Housing Programme ya dogara ne kan tsarin haɗin gwiwar gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu (PPP), wanda aka tsara domin jawo jarin masu zaman kansu, ƙara inganci da kuma faɗaɗa damar mallakar gidaje masu kyau da araha ga ‘yan ƙasa.

Ministan ya ƙara da cewa baya ga samar da matsuguni, irin waɗannan manyan ayyukan na taimakawa tattalin arziki ta hanyar samar da ayyukan yi da kuma ƙara buƙatar kayayyaki da ayyukan cikin gida.

A cewarsa, masu sana’o’in hannu, ‘yan kwangila, masu sufuri da masu samar da kayayyaki na ci gaba da amfana daga ayyukan ginin da ake yi a wurin, lamarin da ke taimakawa wajen bunƙasa tattalin arzikin yankunan da ake gudanar da ayyukan.

“Wannan aiki ba wai samar da gidaje kaɗai yake yi ba. Har ila yau yana samar da ayyukan yi, yana ƙarfafa harkokin kasuwanci kuma yana taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban tattalin arziki da zamantakewa na yankin,” inji shi.

Darma ya bayyana cewa aikin Kano Renewed Hope City ya ƙunshi gidaje 1,500 masu tsari daban-daban, kuma ana sa ran zai samar da matsuguni ga sama da mutane 6,000 bayan an kammala shi.

Ya nuna gamsuwa da irin ci gaban da aka samu a wurin aikin, tare da yabawa masu zuba jari da masu aiwatar da aikin bisa jajircewarsu. Sai dai ya bukace su da su ci gaba da ƙara ƙaimi domin kammala aikin a lokacin da aka tsara.

Ministan ya sake tabbatar da kudirin Gwamnatin Tarayya na faɗaɗa damar mallakar gidaje ta hanyar sabbin hanyoyin samar da kuɗaɗe da kuma ƙarfafa haɗin gwiwa da kamfanoni masu zaman kansu, musamman a bangaren samar da ababen more rayuwa.

Ya ce dabarun gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na bangaren gidaje a ƙarƙashin Ajandar Renewed Hope na da nufin rage ƙarancin gidaje da ake fama da shi a ƙasar, inganta rayuwar jama’a da kuma haɓaka tattalin arziki ta hanyar ayyukan gine-gine.

Aikin Kano na daga cikin manyan shirye-shiryen gidaje da Ma’aikatar Gidaje da Raya Birane ta Tarayya ke aiwatarwa domin rage gibin gidaje da ake fuskanta a Nijeriya tare da ƙara wa ‘yan ƙasa damar mallakar gidajensu.

By ukarofi

Leave a Reply