Hon. Galadima ya bayyana goyon bayansa ga ’yan takarar NDC a Kumbotso

Spread the love

Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano

Tsohon ɗan takarar kujerar Majalisar Wakilai ta Tarayya a Karamar Hukumar Kumbotso ƙarƙashin jam’iyyar NDC, Hon. Aminu Ibrahim Galadima Na’ibawa, ya bayyana cikakken goyon bayansa ga ‘yan takarar da jam’iyyar ta tsayar domin fafatawa a zaɓe mai zuwa.

Hon. Galadima ya bayyana hakan ne yayin wani taro da ya shirya domin gode wa magoya bayansa bisa irin goyon bayan da suka ba shi lokacin neman tikitin takarar kujerar Majalisar Wakilai.

Ya ce duk wanda jagoran tafiyarsu, Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso, ya amince da shi, suna tare da shi kuma a shirye suke su bayar da duk wata gudunmawa domin tabbatar da nasarar jam’iyyar.

“Ba a yanke wannan hukunci ba tare da shawarar juna ba. Saboda haka muna goyon bayan duk waɗanda aka tsayar domin su wakilci jam’iyyar a zaɓe mai zuwa,” inji shi.

Ya kuma yi alƙawarin cewa duk wani ɗan jam’iyya da ya yi ƙoƙari wajen tabbatar da nasarar jam’iyyar a rumfarsa zai samu kyauta ta musamman.

Galadima ya soki yadda wasu zaɓaɓɓun shugabanni ke tafiyar da harkokin mulki, yana mai cewa al’umma na buƙatar shugabannin da za su kawo sauyi da ci gaba.

A nasa jawabin, ɗan takarar kujerar Majalisar Dattawa mai wakiltar Kano ta Kudu, Hon. Bataiya, ya yaba da yadda al’umma suka fito domin halartar taron.

Ya ce tafiyar Kwankwasiyya tsari ne da ya ginu a kan taimakon juna, zumunci da inganta rayuwar jama’a.

By ukarofi

Leave a Reply