Cigaban al’ummar Jahun da Miga ne burina – Hon. Naziru

Spread the love

Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano

Dan takarar kujerar Majalisar Wakilai ta Tarayya mai wakiltar ƙananan hukumomin Jahun da Miga na Jihar Jigawa a ƙarƙashin jam’iyyar ADC, Hon. Muhammad Naziru Jahun, ya ce babban burinsa shi ne samar da ci gaba da walwala ga al’ummar yankin.

Hon. Naziru ya bayyana haka ne yayin da yake ganawa da manema labarai a gidansa da ke Karamar Hukumar Jahun bayan karɓar baƙuncin magoya bayansa da suka kai masa ziyarar barka da Sallah.

Ya gode wa al’umma da ‘yan siyasa bisa irin goyon bayan da suke ba shi, yana mai cewa idan ya samu nasara zai tabbatar da cewa an amfana da wakilcinsa.

A cewarsa, daga cikin abubuwan da zai fi mayar da hankali a kansu akwai samar wa matasa ayyukan yi, tallafa wa mata, bunƙasa harkokin lafiya da ilimi, da kuma tallafa wa manoma domin ƙara yawan samar da abinci.

Ya ce duk da irin ayyukan da shugabanni suka gudanar a baya, akwai buƙatar matasa su shiga harkokin siyasa domin kawo sabbin dabaru da sauye-sauye masu anfani ga al’umma.

Hon. Naziru ya kuma yi amfani da damar wajen taya al’ummar Musulmi murnar Sallah tare da yi wa jam’iyyarsa ta ADC fatan samun nasara a zaɓe mai zuwa.

By ukarofi

Leave a Reply