Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Shugabar Matan Jam’iyyar APC ta ƙaramar Hukumar Bichi, Hajiya Rahana Idris, ta bayyana cewa matan yankin sun shirya tsaf domin tabbatar da nasarar jam’iyyar a zaɓen shekarar 2027.
Ta bayyana hakan ne a wani taron da aka gudanar bayan ƙaddamar da ‘yan takarar jam’iyyar APC a ƙaramar hukumar.
Jami’ar Yaɗa Labarai ta ƙaramar Hukumar Bichi ta rawaito cewa Hajiya Rahana ta ce matan yankin za su ci gaba da mara wa dukkan ‘yan takarar APC baya saboda irin ayyukan ci gaba da suka kawo wa al’umma.
Ta bayyana cewa tallafin da shugabannin APC, musamman ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Bichi, Alhaji Abubakar Kabir Abubakar, ke bayarwa a fannonin ilimi, lafiya, sana’o’i da walwalar al’umma ya taimaka matuƙa wajen inganta rayuwar jama’a.
“Mace idan aka tallafa wa ɗanta kamar an yi mata komai. Mutane da dama sun amfana da tallafin karatu, wasu har sun kammala digiri da digirgir ba tare da iyayensu sun kashe kuɗi ba. Saboda haka muna tabbatar da cewa APC za ta samu gagarumin goyon baya daga matan Bichi a zaɓe mai zuwa,” inji Hajiya Rahana.
Ta kuma yaba da shirye-shiryen tallafa wa mata da suka haɗa da rabon kuɗaɗe, kekunan ɗinki, injinan niƙa, kiwon kaji da na kifi, waɗanda ta ce sun taimaka wajen rage talauci da ƙarfafa tattalin arzikin mata a yankin.
A nata jawabin, mai ɗakin ɗan Majalisar Tarayya, Barista Maryam Abubakar Kabir Abubakar, ta gode wa al’ummar Bichi bisa irin goyon bayan da suke bai wa maigidanta.
Ta ce suna ci gaba da ƙoƙarin tallafa wa mata da matasa domin inganta rayuwarsu tare da bunƙasa ci gaban yankin.
“Muna addu’ar Allah Ya ci gaba da sanya albarka a cikin wannan hidima. Allah Ya ƙara wa shugabanninmu hikima da ikon ci gaba da yi wa al’umma aiki,” in ji ta.
Ta jaddada cewa za su ci gaba da tallafa wa mata da sauran al’umma domin tabbatar da ci gaba mai ɗorewa a ƙaramar Hukumar Bichi.
