An kusa kammala aikin kafa ‘yan sandan jihohi a dokance, inji Fadar Shugaban Ƙasa

Spread the love

Fadar Shugaban Ƙasa ta ce an samu gagarumin cigaba a tattaunawar kafa rundunar ’yan sandan jihohi, inda ake sa ran gabatar da gyaran kundin tsarin mulki nan ba da jimawa ba domin ba da damar aiwatar da shirin.

Shugaban ma’aikatan fadar, Femi Gbajabiamila, ne ya bayyana hakan bayan wata ganawa da aka yi a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja ranar Alhamis, wadda ta haɗa manyan jami’an gwamnati da shugabannin majalisun dokoki kan batun kafa ’yan sandan jihohi.

Gbajabiamila ya ce an fara nazari da tattaunawa kan yadda za a kafa rundunar tun watanni uku zuwa huɗu da suka gabata bisa umarnin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, kuma an samu ci gaba mai yawa a aikin.

Ya bayyana cewa kafa ’yan sandan jihohi ba abu ne da za a yi cikin gaggawa ba, domin akwai batutuwan kundin tsarin mulki da dokoki da dole ne a tantance su sosai kafin aiwatarwa.

A cewarsa, yanzu hankalin masu ruwa da tsaki ya karkata ne kan yadda za a yi gyaran kundin tsarin mulki, sannan daga baya a samar da dokokin da za su ba da cikakken iko da tsarin gudanar da rundunar.

Ya ƙara da cewa, mafi yawan ’yan Najeriya da masu ruwa da tsaki sun amince da bukatar kafa ’yan sandan jihohi, inda muhawarar yanzu ba ta kan ko a kafa su ko a’a ba, sai dai yadda za a samar da ingantaccen tsarin doka da gudanarwa domin su yi aiki yadda ya kamata.

Gbajabiamila ya ce, za a gabatar wa Shugaba Tinubu cikakken rahoto kan sakamakon ganawar domin ci gaba da matakan da suka dace.

Haka kuma ya ce, manufar kafa ’yan sandan jihohi ita ce ƙarfafa tsaron cikin gida, inganta tattara bayanan sirri daga matakin ƙasa da kuma bai wa gwamnatocin jihohi damar magance matsalolin tsaro cikin sauri da inganci.

Shugaba Tinubu ya sha bayyana cewa tsarin ’yan sandan jihohi na daga cikin hanyoyin da za su taimaka wajen fuskantar ƙalubalen tsaro da ke addabar ƙasar nan, tare da ƙara kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Ganawar ta samu halartar Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau I. Jibrin; Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai, Benjamin Kalu; Ministan Shari’a kuma Babban Lauyan Tarayya, Lateef Fagbemi; da Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Tunji Disu, tare da sauran manyan jami’an gwamnatin.

By Babaji

Leave a Reply