Tinubu ya amince da biliyan 46 domin gyaran filin jirgin saman Kano – Iliyasu Kwankwaso

Spread the love

Yayin da gwamnatin tarayya ta amince da kashe naira biliyan 46 domin gyarawa da sake gina titin sauka da tashi na biyu a filin jirgin sama na Mallam Aminu Kano da ke Kano, an shawarci ’yan Arewa su riƙa nuna godiya ga kyawawan ayyukan shugaban ƙasa Bola Tinubu, musamman ganin cewa wannan ƙoƙari ya nuna gaskiya da rashin son kai ga yankin.

Yayin da yake mayar da martani kan amincewar aikin, daraktan kuɗi na hukumar kula da Kogin Hadejia-Jama’are, Hon. Dr. Musa Iliyasu Kwankwaso, ya ce:
“Ina sa ran mutanena, ba tare da la’akari da jam’iyya ba, za su gode wa Shugaba Tinubu saboda wannan abu ne da zai ƙarfafa harkokin kasuwanci da cinikayya a duk faɗin yankin.”

Ya ƙara da cewa:
“Ya kamata mu riƙa godiya idan an yi mana alheri, ba wai kullum sai mun rika ƙorafi kan ƙananan matsaloli mu manta da abubuwan alheri da ake yi mana ba.”

Ministan Sufurin Jiragen Sama da Ci gaban Sararin Sama, Festus Keyamo, ne ya sanar da amincewar yayin ƙaddamar da sabuwar hanyar zirga-zirgar cikin gida ta Muhammadu Abubakar Dankabo da aka sake fasalin ta a filin jirgin.

Keyamo ya bayyana cewa kusan kashi 60 cikin 100 na kuɗin kwangilar an riga an saki, kuma an fara aikin a wurin.

Ya ce aikin wani ɓangare ne na ƙoƙarin inganta filin jirgin sama na Kano da kuma ƙarfafa matsayinsa a matsayin babbar cibiyar zirga-zirgar jiragen sama da kasuwanci ga Arewacin Najeriya.

Yayi ƙarin bayani kan ci gaban, Dr. Musa Iliyasu Kwankwaso ya yaba wa Shugaba Tinubu, Shugaban hukumar kula da sufurin jiragen sama kuma tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Dr. Umar Abdullahi Ganduje, Ministan Sufurin Jiragen Sama, Shugaban Kwamitin kasafin ƙudi na Majalisar Wakilai, Abubakar Kabir Bichi, da dukkan wadanda suka ba da goyon baya wajen amincewa da aikin.

Ya bayyana cewa bayan kammala gyaran titin jirgi na biyu, Filin Jirgin Sama na Mallam Aminu Kano zai dawo da martabarsa a matsayin babbar cibiyar tattalin arzikin Arewa.

Kwankwaso ya yi kira ga manyan Arewa, malamai da shugabanni da su fito su nuna godiya, tare da koyar da iyalansu soyayya da goyon baya ga shugabannin da ke son ci gaban yankin.

By ukarofi

Leave a Reply