Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Ma’aikatar Noma da Samar da Abinci ta Tarayya tare da haɗin gwiwar abokan hulɗarta na ci gaba, ta amince da sabunta Manufofin ƙasa Kan Daidaito Tsakanin Mata Da Maza A Sauya Fasalin Tsarin Noma Da Abinci (NGPAST) domin ƙara haɗa kowa da kowa a harkokin noma da kuma bunƙasa samar da abinci a ƙasar nan.
An ƙaddamar da wannan manufa ne a birnin Abuja, inda aka bayyana cewa za ta taimaka wajen kawo sauye-sauye da za su sa tsarin noma da samar da abinci a Nijeriya ya kasance mai ɗorewa, mai haɗa kowa da kowa, tare da bai wa mata da maza dama iri ɗaya.
Da yake jawabi a wajen taron, Ministan Noma da Samar da Abinci na Tarayya, Sanata Abubakar Kyari, wanda ƙaramin Ministan Noma da Samar da Abinci, Sanata Aliyu Sabi Abdullahi ya wakilta, ya bayyana sabuwar manufar a matsayin wata hanya mai amfani da za ta tabbatar da adalci wajen bai wa mata da maza damar samun albarkatun noma, damar kasuwanci da kuma shiga cikin yanke muhimman shawarwari.
Ministan ya jaddada cewa noma na taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa tattalin arziki, samar da ayyukan yi da kuma tabbatar da wadatar abinci. Sai dai kuma ya nuna damuwa cewa har yanzu akwai gibin da ke hana mata da dama shiga harkokin noma yadda ya kamata duk da irin muhimmiyar gudunmawar da suke bayarwa a sarkar samar da abinci.
A cewarsa, sabuwar manufar za ta taimaka wajen saka manufofin da ke kula da bukatun mata da maza cikin shirye-shiryen noma da tsare-tsaren gwamnati, lamarin da zai taimaka wajen amfani da cikakken ƙarfin da ke cikin wannan fanni.
Kyari ya kuma yaba da gudunmawar ƙungiyoyin ci gaba da suka taimaka wajen tsara wannan manufa, ciki har da ActionAid Nigeria, AGRA da GIZ.
Ya buƙaci hukumomin gwamnati, kamfanoni masu zaman kansu da sauran masu ruwa da tsaki su haɗa wannan manufa cikin shirye-shiryensu, kasafin kuɗinsu da tsarin aiwatar da ayyukansu. Haka kuma ya tabbatar da cewa ma’aikatar za ta samar da ingantattun hanyoyin sa ido da tantancewa domin tabbatar da an samu sakamakon da ake buƙata.
A nasa jawabin, Ƙaramin Ministan Noma da Samar da Abinci, Sanata Aliyu Sabi Abdullahi, ya ce shirye-shiryen ma’aikatar sun yi daidai da Manufar Sabunta Fata ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu a fannin noma.
Abdullahi ya ƙara da cewa ma’aikatar na aiki tare da ofishin Uwargidan Shugaban ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, wajen yaɗa shirin “Kowane Gida Ya Mallaki Lambu”, tare da shirye-shiryen wayar da kai kan abinci mai gina jiki da ilimin kula da gida a matakan jihohi da ƙananan hukumomi ƙarƙashin Shirin Sabunta Fata.
Tun da farko, a jawabin maraba, Babban Sakataren Ma’aikatar Noma da Samar da Abinci, Dakta Marcus Ogunbiyi, wanda Daraktan Sashen Tallafin Kayan Noma, Mista Abana Waziri Abba ya wakilta, ya ce sabuwar manufar za ta taimaka wajen magance manyan matsalolin da ke hana cikakken shigar mata da maza cikin harkokin noma tare da rage yawan amfanin gona.
