Daga GAMBO ISA a Abuja
Shugaban Karamar Hukumar Katagum ta Jihar Bauchi, Alhaji Yusuf Babayo Zaki, ya yaba da irin ayyukan ci gaba da Gwamna Sanata Bala Abdulkadir Mohammed ke gudanarwa a fadin jihar, yana mai cewa gwamnan ya nuna jajircewa wajen bunkasa rayuwar al’umma da gudanar da mulki mai anfani ga kowa.
Wannan ya zo ne a daidai lokacin da shi ma Shugaban ƙaramar Hukumar Zaki, Dakta Adamu Yakubu Sakwa, ya yaba da ƙwazon Gwamna Bala ɗin.
A cikin wata sanarwa da ya fitar kuma aka rabawa manema labarai a Abuja, Alhaji Yusuf Babayo Zaki ya bayyana cewa gwamnatin Bala Mohammed ta samu gagarumar nasara a fannoni daban-daban da suka hada da bunkasa albarkatun jama’a, noma, kiwo, ilimi, lafiya, tsaro da kuma samar da ababen more rayuwa.
Ya ce gwamnatin jihar ta aiwatar da manyan ayyukan tituna, ciki har da titunan Trunk B da C da suka hada garuruwa da kananan hukumomi daban-daban, lamarin da ya saukaka zirga-zirga da harkokin kasuwanci a jihar.
Shugaban karamar hukumar ya kuma yaba da gyaran da gina sabbin sakatariyoyin gwamnati na zamani, samar da hasken rana a tituna da wuraren gwamnati, da kuma fadada hanyoyin cikin birane da kauyuka, wanda ya ce ya taimaka wajen inganta ayyukan gwamnati a matakin kasa.
Ya kara da cewa gina kasuwanni na zamani da shaguna a garin Azare, ciki har da shaguna 18 da kuma cibiyar GSM Village, zai taimaka matuka wajen samar wa matasa hanyoyin dogaro da kai da habaka tattalin arziki.
A bangaren tsaro kuwa, Alhaji Yusuf Babayo Zaki ya jinjinawa gwamnan kan kokarinsa na inganta tsaro ta hanyar gina ofisoshin ‘yan sanda, tallafawa jami’an tsaro da kungiyoyin sa-kai, samar da motocin aiki da kuma gudanar da tarukan tantance matsalolin tsaro a kai a kai.
Ya yi kira ga al’ummar yankin da su ci gaba da zaman lafiya da hadin kai tare da daukar nauyin tabbatar da zaman lafiya a tsakanin su.
A fannin lafiya, shugaban karamar hukumar ya yaba da yadda gwamnatin jihar ta horas da ma’aikatan lafiya, ta inganta cibiyoyin kiwon lafiya, ta gina asibitin zamani a Katagum tare da samar da cibiyoyin lafiya na matakin farko a sassa daban-daban na jihar.
Ya ce samar da kayan aiki ga ma’aikatan lafiya da daukar sababbin ma’aikata ya taimaka wajen inganta ayyukan kiwon lafiya da saukaka samun kulawa ga jama’a.
Dangane da noma da kiwo, Alhaji Yusuf Babayo Zaki ya bukaci manoma da makiyaya su ci gajiyar shirye-shiryen gwamnatin jihar da suka hada da rabon kayan noma, samar da wuraren kiwo, ayyukan likitocin dabbobi da kuma tallafin noman rani.
Ya bayyana Katagum a matsayin daya daga cikin manyan cibiyoyin noma da kiwo a yankin Arewa maso Gabas, yana mai jaddada muhimmancin zaman lafiya tsakanin manoma da makiyaya domin tabbatar da ci gaba mai dorewa.
Haka kuma ya yi kira ga Hukumar Raya Kogin Hadejia-Jama’are da ta gina madatsar ruwa a yankin domin bunkasa noman rani da samar da ruwa ga dabbobi.
Shugaban karamar hukumar ya kuma bukaci ma’aikatan gwamnati da su kasance masu himma, gaskiya da jajircewa wajen gudanar da ayyukansu domin cimma manufofin ci gaban gwamnati.
Ya roki Asusun Tallafa wa Ilimi na Jihar Bauchi da ya tallafa wa Karamar Hukumar Katagum da kayan koyarwa da na karatu, musamman domin inganta ilimin yara mata da karfafa gwiwar mata wajen neman ilimi.
Alhaji Yusuf Babayo Zaki ya kuma nuna godiyarsa ga Gwamna Bala Mohammed kan shirye-shiryen tallafawa marasa galihu da matasa, yana mai cewa irin wadannan tsare-tsare sun taimaka wajen rage talauci da samar da hanyoyin dogaro da kai.
Ya yaba da shirye-shiryen horas da matasa sana’o’i, samar musu da ayyukan yi da kuma kafa cibiyar GSM Industrial Hub Village, wanda ya ce zai kara habaka tattalin arziki tare da samar da karin guraben aikin yi.
A cewarsa, Gwamna Bala Mohammed jagora ne mai hangen nesa wanda ya samu karbuwa a matakin kasa sakamakon ayyukan alherin da yake gudanarwa, ciki har da jagorancin kungiyar gwamnonin PDP.
Ya kammala da kira ga al’ummar jihar, shugabannin al’umma, malamai da ma’aikatan gwamnati da su ci gaba da mara wa gwamnati baya tare da addu’ar samun ci gaba da zaman lafiya a Jihar Bauchi da Najeriya baki daya.
Shi ma Shugaban ƙaramar Hukumar Zaki, Dakta Adamu Yakubu Sakwa, ya yaba wa Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Muhammad, bisa irin gagarumar gudunmawar da yake bayarwa wajen bunƙasa ci gaba da kyautata rayuwar al’ummar jihar. A cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja, Sakwa ya bayyana cewa gwamnatin Bala Muhammad ta samu nasarori masu yawa a fannoni daban-daban da suka haɗa da ilimi, lafiya, noma, tsaro da samar da ababen more rayuwa.
Ya ce daga cikin manyan ayyukan da gwamnatin ta aiwatar akwai gina da gyaran sakatariyoyin gwamnati na zamani, samar da fitilun hasken rana a yankuna daban-daban, da kuma gina hanyoyin cikin gari da na haɗa al’ummomi. Haka kuma ya yabawa gwamnatin bisa gina kasuwanni da shaguna na zamani a Zaki tare da samar da ingantattun ofisoshi da ɗakunan taro masu amfani da hasken rana.
Dakta Sakwa ya bayyana cewa gwamnatin Bala Muhammad ta aiwatar da sama da ayyukan raya ƙasa 228 a Zaki da sauran ƙananan hukumomin jihar.
Ya ce daga cikin waɗannan ayyuka akwai gina hanyoyin Trunk B da suka haɗa yankin Sakwa, waɗanda ya ce ba a samu irin su ba tun zamanin gwamnatin Shehu Shagari a shekarun 1980.
A fannin tsaro da lafiya kuwa, shugaban ƙaramar hukumar ya yabawa gwamnan kan gina ofisoshin ‘yan sanda, tallafa wa jami’an tsaro da ƙungiyoyin sintiri, da samar da motocin aiki. Haka kuma ya jinjina masa kan gina asibitin zamani a Zaki, inganta cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko, horar da ma’aikatan lafiya da samar musu da kayan aiki domin inganta ayyukan kula da lafiyar jama’a.
Dangane da noma da bunƙasa matasa, Dakta Sakwa ya buƙaci manoma da makiyaya su ci gaba da amfani da shirye-shiryen tallafin noma da kiwo na gwamnatin jihar. Ya kuma yabawa shirye-shiryen horas da matasa sana’o’i da kafa cibiyar masana’antar GSM Industrial Hub Village, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen samar da ayyukan yi da bunƙasa tattalin arziki.
Ya kammala da kira ga al’umma da ma’aikatan gwamnati da su mara wa shirye-shiryen gwamnati baya tare da ci gaba da addu’ar zaman lafiya da ci gaban Jihar Bauchi da Najeriya baki ɗaya.
