Babu amfanin samun mace in har ba za ta taimaki mijinta ba – Jiddah Haulat Nguru (2)

“A wannan zamani sana’a kamar dole ta zamewa ‘ya mace”

Daga AISHA ASAS

A satin da ya gabata, mai karatu idan bai manta ba, mun ɗauko fira da matashiya Jiddah Haulat Nguru, inda ta fara bayyana mana tarihi da kuma irin sana’ar da take yi, wadda ta tabbatar mana ana cin kasuwarta ne a kafafen sadarwa, sannan ta yi mana bayanin yadda ta fara, da hanyoyin da take bi don siya da siyar da kayanta a kafafe kamar Fesbuk, WhatsApp da sauransu.

A wannan satin, za mu ɗora ne daga inda muka tsaya. Kamar yadda muka sanar, baƙuwar tamu za ta fara da tambayar da wuri bai ba mu damar jin amsarta ba, kafin wasu tambayoyin da za su biyo baya.

Idan kun shirya, har wa yau dai, Aisha Asas ce tare da Jiddah Haulat Nguru:

MANHAJA: Akwai mata masu zaman kashe wando, a naki hasashen me hakan ke nufi a rayuwarsu?

JIDDAH HAULAT NGURU: Wannan tafiya suke da rayuwa cike da rashin manufa da cimma kyakkyawan wuduri. Sabida idan kika zauna zaman kashe wando kenan ke ba ki da wani ‘future’ da kike son cimmawa rayuwarki ko ta ‘ya’yanki. Kawai komai ya zo salamu alaikum babu tsari. Balle ki san me yaranki za su zama ko suke da burin zama a rayuwarsu. Ba ki da wani dogon lissafi ko nazarin cigaban rayuwa. Irinsu za ki ga komai ya zo ba su san da shi ba har ya wuce. Wataran ma cigaban ta ƙofar dakinsu zai bi, amma ba su san menene shi ba.

Wasu matan na kukan ba su da jari ne shi ya sa ba sa yin sana’a. Wacce shawara ki ke da ita gare su?

Yanzu sana’a ai ‘Fashion’ ta ke buƙata ba jari ba, musamman a gurin macen da ke ta’ammali da ‘social media’. Akwai abinda ake kira ‘Affiliated marketing’, yawancin ‘yan ‘online’ da ita suka dogara. Wani shago ko wasu mutanen suna da kaya, sai ka karɓa akan farashin sari ka tallata kayan ka samu riba. Ko ni Ina bayar da kayana akan hakan. Kin ga daga nan mace ta na yi hakan a hankali a hankali har Allah zai ba ta na ta jarin itama da za ta dogara da shi.

Sanar da mu irin ƙalubalen da ki ka dinga cin karo da su a sana’a ta intanet.

Ƙalubale kam Alhamdulillah akwai su dole tunda rayuwa ake. Na farko matsalar masu mota da customers, musamman yanzu da kuɗin mai ya qaru. Direbobi kana kai musu kaya za su raba kuɗin mota gida biyu su ce haka za a bayar da kuɗin kayannan duk ƙanƙantarsa. Shi kuma customer zai ga kuɗin ya masa yawa gaskiya gara ya haƙura. Kai kuma wataqila a wannan cinikin da za a tattara ribarka a kayan bai fi 500 ko 1000 ba, wataran ma bai fi 300 ba. Wani customer ma bai san cewa wataƙila ba ka ci komai akan kayansa ba, ka haƙura ne sabida kiran kasuwa. To sai su saka a tsakiya ka rasa yanda za a yi. Idan Allah ya taimake ka ka samu direba mai fahimta da customer mai fahimta sai a yi komai cikin sauƙi. Amma wasu kam dole a hakan za a rabu ba daɗi, ko ya siya ya na jin haushinka, ko kai ka haƙura ka cika masa kuɗin motar, musamman idan abin mai lalacewa ne kana gudun yin asara.

Haka masu delivery na cikin gari. A ‘online business’ ne kaɗai mutum zai sayi kayanka, ka kira masa abin hawa ya kai masa saƙo, ya ce sai ka masa ciniki. Alhalin da kasuwa zai je ya siyo kaya zai biya kuɗin abin hawa ya je ya biya na dawowa, wataƙila wannan na ‘delivery’ bai kai shi kuɗi ba. Amma ba zai yi ‘complain’ ba. Wasu gani suke idan sun sayi kaya a gurinka kamar alfarma suka maka. Eh alfarma ce, amma dukkanmu taimakon juna ne, shi ya ga abinda yake so, kai kuma ya raba ka da shi ya ba ka kuɗi. To dukka sai an sa haƙuri da fahimtar juna.

Sai ƙalubale na gaba, wani duk kyan abinda za ka ba shi sai ya kushe, ko kuma sau goma kana ba shi mai kyau, sai aka samu kuskure sau ɗaya ba zai iya cinyewa ba. Ba a hana ‘complain’ ba , amma wasu har da kamar wulaƙanci.

Sai ƙalubale na gaba ni da ya fi damuna shi ne, yawancin sana’ata ta kayan ci ce, masu saurin lalacewa musamman kifi, idan zafi ya zo ko damuna zai yi tsutsa idan ba a karɓa da wuri ba. Sai ka kawo wani sa’in ba lokacin za a karva ba. Shi kuma kindirmo idan ya ji zafi zai yi tsami dole sai ya kasance kullum a cikin firiji, ga matsalar wuta da ake fama da shi. Abubuwan dai da ɗan dama.

Na san ba za a rasa nasarori ba.

Ah Alhamdulillah akwai nasarori masu tarin yawa, suna kan zuwa ma. Wannan hirar da BluePrint Manhaja, ta yi da ni itama nasara ce. Kasuwancinan ya min abubuwa da dama a rayuwata da ba zan taɓa mantawa da su ba. Ya rufa min asiri ya taimakeni ya taimaki wani na yana kan yi ma In sha Allah. Sannan kullum ina faɗa ya hada ni da mutanen arziki da dama a rayuwata. Sannan ya hanani babu ko da kaɗan ne. Ko ya na yi ‘broke’ Ina kasa kayana za a iya siya na biya buƙatata.

Wane buri ki ke da shi kan sana’ar da ki ke yi?

Wallahi ina da burika masu yawa sosai. Musamman akan sabuwar sana’ata ta kindirmo. Yanzu da farko Ina da burin siyan firiza mai solar wacce ba sai na jira Nepa ba. Sannan na buɗe kamfanin Producing, ba na dinga yi a gida ba. Sannan na buɗe branch-branch a dukkan jihohi na ƙasar nan har da maƙofta. Shi ya sa yanzu na fara rarraba kayana a hannun ‘distributors’ na jihohi, sabida Ina son mutane su fara saninsa su ɗanɗana shi tun yanzu. Ina son na ga na ɗaukaka kamar yanda Rufaida Yoghurt suka ɗaukaka. Ina da burin na ga ‘yan’uwana mata sun kama sana’a sun dogara da kansu sun bar zaman banza.

A taki fahimta, menene matsayin sana’a ga ‘ya mace a wannan zamani?

Ni a tawa fahimtar a wannan zamanin sana’a kamar dole ya zamewa ‘ya mace. Sabida waɗancan dalilin da na faɗa da farko. Sannan a fahimtar rayuwa da lissafi yawanci yara sun fi rayuwa a hannun mahaifiyarsu. Wataƙila ko mahaifin ya rasu ko sun rabu da mahaifiyar. To idan uwa ba ta sana’a za ki ga ita da rayuwar yaran duk a gigice. Abin Allah ya kiyaye sai ki ga a irin wannan yanayin rayuwar su ta lalace babu tarbiyya, tunda babu karatu babu abin biyan buƙatar rayuwa. Ko’ina mace ta yi ita da ‘ya’yanta ƙyamatarsu ake. A ƙarshe wasu sai dai su koma bara ko yawon banza ko shaye-shaye. Amma idan mace ta kama sana’a, buƙatar wasu ma biya musu ta ke ba ta yaranta kaɗai ba.

A wannan lokaci da muke ciki da matsin rayuwa sai ta’azzara yake yi. Wane kira za ki yi ga mata kan taimakon mazaje a buƙatun gida?

Shawara ga mata dan Allah a kama sana’a , kuma kar a yiwa maigida kyashi kan abinda aka samu. Duk duniya mace babu inda ya kamata ta rufawa asiri kamar gidanta da na iyayenta. Ban ga amfanin samun mace ba a duniyar nan da za ta kasa taimakon mijinta da komai. Wasu matan har taƙama suke akan hakan. “Wa ni ai kuɗina nawa ne ba zan taimaka masa da ko maggi ba.” Ba ta san cewa waɗanda ta ke faɗawa hakan kallon marar daraja suke ma ta ba. Domin in ta taimaka ɗin kanta ta rufawa asiri da ‘ya’yanta. Matuƙar namiji baya miki mugunta dan Allah ke ma kar ki yi masa. Sai ki ga asirinku a rufe , babu wanda zai san babun ku. Mata a daure a rinqa taimakon mazaje musamman ma a wannan lokacin na karyewar tattalin arziki.

Wane kalar abinci ki ka fi son ci?

To fa! (dariya) A abinci ina da zaɓi, ba ni da zaɓi. Ni kawai in dai abinci yayi daɗi, to Ina cin kowanne gaskiya.

A fahimtarki mace ce matsayin kwalliya ga mata?

A fahimtata kwalliya ra’ayina ne ga mata. Amma fa babu macen da ba ta kwalliya. Ina jin wasu matan idan ana hira da su, sai su ce, “ai ni ba na kwalliya daga hoda, sai witlips.” Na rasa ma’anar wannan maganar. Hoda da kwalli da maiqon baki ai su ne kwalliya. Duk wani abu da za a qara akan hakan kuma ado ne. So ni dai a nawa ganin kowacce mace tana kwalliya, kuma kwalliya ita ce mace. Dan ba macen da za ta yi wanka ta shafa Mai kawai ta fito, sannan ta ga ta yi yanda ta ke so duk kyaunta. Dole sai ta haɗa da hoda, ba kamar maza ba, da su haka Allah ya yi su ba ruwansu da hoda bayin Allah.(Dariya). Dan haka kwalliya ita ce mace.

Wacce irin kwalliya ki ka fi sha’awa?

A kwalliya na fi sha’awar sassauƙa. Wacce zan shafa mai da hoda na saka kwalli na sa man leɓe. Na fi gani na a daidai gaskiya. A ado kuma na fi jin daidai idan na yafa lafaya ko hijabi gaskiya. Amma Ina yin kowanne har da mayafi.

Mun gode da lokacin ki.

Ni ma na gode ƙwarai da wannan damar da ku ka ban. Ubangiji ya ɗaukaka gidan jaridar Blueprints Manhaja ya ɗaukaka ma’aikatanta, ya tallafi rayuwar mata da ƙananan yara. Allah ya ba mazaje ikon dafawa da tallafar matansu da yaransu yanda za su tsaya da ƙafafuwansu ko da ace ba sa raye a duniyar. Na gode.

Amin ya Rabbi.