Har yanzu akwai tsofaffin marubutan da ba su yarda da rubutun onlayin ba – Jamila R/Lemo

“Na samu kaina a harkar rubutu tun Ina ‘yar shekara tara”

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Ga duk mutumin da ya kasance tsohon makarancin littattafan Hausa ne, musamman littattafan da jajirtattun mata gwanayen riqe alqalami suka wallafa a shekarun baya, ba zai kasa karanta littafin Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo ba, marubuciyar ‘Mamaya’, ‘Zaƙi Da Maɗaci’, da Bakin Ganga. Wacce bayan kasancewarta marubuciya har wa yau kuma ma’aikaciya ce ƴar jarida, da ta daɗe tana bayar da gudunmawa a harkar ilimi da cigaban al’umma. Littafinta na ‘Kanya Ta Nuna’ da ta fara bugawa a shekarar 2002 ya kasance zakaran gwajin dafi, wanda shi ya fara haska tauraruwarta a tsakanin marubuta. Shekaru tara bayan dogon hutun da ta tafi, yanzu Jamila Rijiyar Lemo ta dawo da zafinta, don ba ta yi qasa a gwiwa ba ta shiga ayarin marubutan onlayin na yanar gizo, har kuma ta sake sabon littafinta mai suna ‘Makomarmu’. A zantawarta da wakilinmu Abba Abubakar Yakubu, marubuciyar ta bayyana yadda take ƙoƙarin sake fitar da tsofaffin littattafanta a yanar gizo, don dawo da tagomashinta da kuma sake qullewa da masu bibiyar rubutunta.

MANHAJA: Ko za ki gabatar mana da kanki?

JAMILA R/LEMO: Sunana Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo. Ni asalin ƴar Jihar Kano ce, daga Ƙaramar Hukumar Ungoggo. Ni ma’aikaciya ce a ma’aikatar yaɗa labarai ta Jihar Kano. Yanzu haka ni ce Jami’ar Yaɗa Labarai a Ƙaramar Hukumar Dala. Na taɓa yin aure, kuma ina da yara shida mata da maza. Alhamdu Lillah.

Za mu so mu san tarihinki a taƙaice.

An haife ni a shekarar 1980. Na yi karatuna tun daga firamare zuwa matakin digiri na farko wanda na samu a Jami’ar Bayero da ke Kano (BUK) a fannin tattara bayanai da adana su, da a turance ake kira Library And Information Science.

Ba mu labarin yadda ki ka samu kanki a harkar rubutu.

Haƙiƙa na samu kaina a harkar rubutu tun ina ‘yar shekara tara; a lokacin ina aji biyu zuwa uku a matakin firamare. Watarana yayanmu Nasir ya gama yi mana bitar abin da aka koya mana a makaranta a ƙarshen mako, sai na ɗauki littafin rubutunsa (Exercise Book) ina dubawa; a nan ne na ga wani rubutaccen labarin wasan kwaikwayo da ya rubuta, take sai na fahimci ƙirƙira ya yi. Ban yi ƙasa a gwiwa ba da ke ina da ɗabi’ar yawan tambaya game da abin da nake son sani ko na tabbatar, na tambaye shi, shi ya rubuta? Ya amsa. “Na’am! Ni na rubuta.” Take sai ƙwaƙwalwata ta ɗarsu kan ni ma zan iya saƙa labari na rubuta kamar yadda na ga ya yi, kuma ban yi shiru ba na amayar masa hakan. Take shi ma ya ba ni damar hakan tare da ƙarfafa ta. Ya kawo kuɗi ya ba ni. “Maza sayo littafi da biro ki rubuta na gani.”

To, haka aka yi, a lokacin na rubuta littafi har ma na yi masa suna ‘Idan Ba Ka Ci Naman Kura Ba…’ Wannan shi ne ainihin sila ko maƙasudin fara rubuce-rubucena har kawo yanzu ban fasa yi ba, bisa lamuncewa ta Ubangiji Allah Madaukakin Sarki!

Wacce gwagwarmaya ki ka sha kafin ki samu karvuwa da shahara a tsakanin marubuta?

To, Alhamdu Lillah ba za a ce babu gwagwarmaya ba, abin da na sani shi ne; na fuskanci ƙalubale sosai tun daga littafin da na fara bugawa wato ‘Kanya Ta Nuna…’ Tun farkon fara aikin a na’ura mai kwakwalwa kafin ma ya kai matakin miƙa wa kamfani a buga, na sha kuka a hanya wajen zarya kan yadda aka riƙa yi min yawo da hankali. A taƙaice dai, da ƙyar da siɗin goshi na samu aka kammala buga littafin, amma ana kai shi kasuwa mutane da dama suka sanni ta hanyar sunana, ba ma iya ƙasarmu Nijeriya ba hatta wasu ƙasashen ƙetare irin su; Nijar da Ingila domin har intabiyu wasu suka yi da ni a wancen lokacin, yayin da suka kawo ziyara Nijeriya dangane da harkokin adabin Hausa. Gwagwarmayar da ta biyo bayan wannan ita ce, wajen karvar kuɗi daga masu sayar mana da littattafai, da kyar suke biyan mu kuɗaɗenmu bayan littafin ya daɗe da ƙarewa a kasuwa lokaci mai tsawo. Sannan da aka tashi ba ni ma a tsittsinke aka riƙa bani. Haka dai al’amura suka ci gaba da gudana, kura da shan bugu gardi da amshe kuɗi; kowanne littafi zan fitar sai na sake masa sabon jari, har Allah Ya kai ni hannun wanda na samu sawaba da sauƙi a wajensa ta fuskar gaskiya da riƙon amana bakin iyawarsa.

Kin wallafa littattafai sun kai nawa?

Littatafaina guda tara ne: akwai ‘Kanya Ta Nuna…’1, 2, & 3, ‘Shan Koko…’1, 2, & 3, ‘Zaƙi Da Maɗaci’…1, 2 & 3, ‘Mamaya’ 1 & 2, ‘Tattabara’…1, 2, & 3, ‘A Daidaita Sahu'(Tarihinta da Ayyukanta 2004-2007), sai ‘Cizo da Kamar Ceto…’1, 2 & 3, da kuma ‘Bakin Ganga…’1 & 2, sannan akwai ‘Makomarmu’.

Littafin ‘Zaƙi da Maɗaci’ shi ne Bakandamiyata a cikin duk littatafaina, mutane da dama suna matuƙar son labarin kuma a shekarar da ya fita kasuwa, shi ne ya zama zakara wajen dabarun iya ba da labari. Ya ƙunshi rayuwar wasu attajirai aminan juna da suka yi hulɗar kasuwanci tare, akwai tsananin so da ƙauna da shaƙuwa tsakanin dangin taurarin littafin biyu da ke ƙunshe a littafin, amma hakan bai hana su faɗawa a cikin tashin hankali na gwagwarmayar rayuwa ba, duk da irin rayuwar alatu da kuma kwanciyar hankalin da suke ciki sakamakon jarrabawa ta Allah da yake wa bayinSa muminai, mai kuɗi ko talaka.

A taƙaice labarin yana magana ne a kan “Layu nalu izza hatta tazullaha! Ma’ana rayuwa ba ta ɗaukaka sai ta ƙasƙanta! Duba da wasu mutane masu yi wa masu hannu da shuni mummunar fahimta har ma ka ji suna iƙirari “Su ci a nan, mu ci a can!”

Shi littafin ‘Shan Koko’ shi littafi ne da a karan kaina nake matuƙar sonsa, domin littafi ne da yake ƙunshe da abin tausayi a cikinsa, kusan kishiyar ‘Zaƙi Da Maɗaci’ ne kasancewar labarin wasu talakawa ne masu tsananin rauni. Da yawa ana ƙyama da tsangwamar talaka, musamman marasa gata da galihu duk da ba shi ya ɗora wa kansa ba, har ma a riƙa fifita mai kuɗi ko ture shi a kan abin da shi ma yake da haƙƙi da kuma iko a cikinsa, koda talakan ya fi mai kuɗin nagarta. A takaice wannan littafi yana nuni ne da cewa talauci ba hauka ba ne, mutum ba shi yake ɗorawa kansa ba, shi ma nau’i ne na jarrabawa da Allah Yake yi wa bayinSa muminai, kamar yadda Ya ce a tsarkakan sunayenSa kyawawa. “Ba Ya jarrabtar bawa sai mumini masoyinSa.” Sadakallahul Aziim. Kuma kowa ya sani raba bawa da arziƙi sai mutuwa.

Sannan shi kuma littafin ‘Makomarmu’ littafi ne da na fito da shi a cikin wannan shekara ta 2023 kuma ya bambanta da sauran littatafaina matuqa da gaske, domin na yi shi ne a kan doron nazari da zurfin bincike, duba da halin da muke ciki a wannan marra na taɓarɓarewar al’amura bakiɗaya. Ƙunshiyar littafin; mutanen da suna da bambanci da na yanzu musamman Hausawa, mafi yawa mun sauka daga kan al’adunmu masu kyau tare da gurɓacewar ɗabi’unmu. Allah Ta’ala Yana cewa a cikin littafinSa mai tsarki. “Ba Ya sauyawa ko gyarawa mutane halin da suke ciki na ɗabi’u har sai sun gyara na daga abin da yake gare su.” Suratul Ra’ad aya ta goma sha ɗaya

Bisa fahimtata da nazari, matuƙar ba mu sauya halayenmu ba to, ba za mu taɓa ganin daidai ba, shi ya sa a matsayina na marubuciya na rubuta wannan littafi akan jigon tarbiyya da ilimi, ta hanyar hikima da azanci domin ‘Makomarmu’ ba ta wajen kowa tana hannunmu.

To, wanne darasi ki ka fi mayar da hankali wajen faɗakarwa cikin rubuce-rubucenki, kuma ta yaya ki ke gano jigon da za ki yi rubutu a kai?

Soyayya! Ɗalibai ne guda uku; na farko a karan kaina ina son so ƙwarai da gaske, kuma ban yi mamakin yadda na tsinci kaina a haka ba sai da wani masani na yanayin da aka haifi mutum da yanayin halittarsa ya yi min wasu tambayoyi na amsa. Ya ce dole ne in zama haka. Har ma ya ƙara da cewa, “wanda ya tsinci kansa a rukunin farko ne zai iya fina son so!” Na biyu sai na gano a fahimta ta Bahaushe shi ne koma baya wajen iya renon soyayya, don haka yana buƙatar wayarwa sosai a kanta, na uku shi ne kasancewata marubuciya. Kuma ita soyayyar nan ba hauka ba ce, ba tawaya ba ce, kamar yadda na ji daga malamai. To, me zai hana in faɗakar da jinsina a kanta ba? Waɗannan dalilan ne suka sa na mai da hankali sosai wajen amfani da ita a babban jigo na labarina. Amma ba ita kaɗai nake kambamawa a zaren labaraina ba, ina ƙoƙarin saka wasu abubuwan da al’umma suke buƙatar nusarwa a kansu kamar; gaskiya, amana, ɗa’a, da ilimi, a cikin saƙar labaran ta yadda soyayyar za ta samu kayan alatun ado da ƙyalƙyali a cikinta. Za a iya gane haka idan aka yi duba da irin yanayin sunan yankan littattafaina, domin har wa yau babu wani littafina da sunan shi ya yi kama da tsagwaron soyayya a bangonsa.

Kuma na kan samu jigon labarina daga bakin mutane idan suka yi wani furuci a cikin zance wala’allah da ni ko da wasu idan kunnena ya ji. Misali littafina ‘Kanya Ta Nuna…’a bakin wani almajirin gidanmu na ji ya furta yana hira, na ce in Allah Ya yarda sai na rubuta littafi da wannan karin maganar. Haka ‘Mamaya’… na je gidan ƙanwata ban iske ta ba ta shiga maƙwafta, tana dawowa ta ba ni labari. “Maman wane ce ta haihu, yanzun nan muka rabu lafiya-lafiya babu alamar ciwo, ina shigowa ko mayafi ban ajiye ba aka biyo ni da gudu in zo ta haihu, na ce tab! Wannan ai naƙudarta ita ce fijo haihuwarta ta zama ‘Mamaya’!”

Tun da kalmar ‘Mamaya’ ta daki kunnuwana, wani abu ya ɗarsu a ƙwaƙwalwata, tana rufe bakinta na ce, nima in sha Allahu sai na rubuta littafi da wannan sunan kuma in Allah Ya yarda duk wanda ya karanta labarin sai ya mamaye shi. Allah kuwa Ya lamunce min na rubuta, da yawa waɗanda suka karanta suna kai wa ƙarshen labarin na ɗaya suke kirana a waya. Tab! Ya aka yi haka? Kaza-kaza dai. Wasu ma tambaya ta suke yi, “Wai don Allah fim ne na gani?” Na ce, a’a wallahi ƙirƙirar labarin kawai na yi ba gani na yi ba.

Wani sa’in kuma ina kallon wata mas’ala ta mutane sai na gina labari akai don warwarewa ko kuma nuni da hannunka mai sanda. Wani lokacin kuma haka kawai zan zauna na ƙirƙiri labarin da zai zama kukan kurciya jawabi ne mai hankali yake ganewa.

Yaya ki ke kallon faɗuwar kasuwar bugaggun littattafai da tasowar kasuwar bayan fage ta onlayin?

Babu daɗi ko kaɗan! Kuma matsala ce gagaruma da ta zama wani ƙatoton aiki a gare mu marubuta, musamman mu tsofaffin marubuta littattafan Hausa, duba da irin yadda muka samu tasgaro ta fuskoki daban-daban. Farko rashin gaskiya da cin amana da wasu ‘yan kasuwa suka yi mana wanda ya haifar da karyewar tattalin arziqin mafi yawan cikinmu, musamman mata, ga matsalar rashin tsaro da ya hana baƙi daga wasu jihohi da suke cin kasuwar littatafanmu sosai a baya, sannan tsadar rayuwa da karyewar tattalin arziƙin duniya da ya shafi kusan kowa, ga uwa uba rashin ɗabi’a ta karance-karance ga al’ummarmu ta Hausawa, sai kuma cigaban zamani, watau komai da ya koma yanar gizo da wasu sabbin marubuta ‘yan zamani suke ta cin sharafinsu akai. Ga shi mu tsofaffin marubutan har yanzu mafi yawanmu mun ƙi yarda mu saki jiki mu bi zamani mu tafi tare a ci gaba da damawa da mu, sai ‘yan tsirarinmu ne suke kamantawa.

Aka ce idan duka ya yi yawa na kai ake ƙarewa, da babu gara ba daɗi, ya kamata marubuta littattafai mu yi ƙoƙari mu koma onlayin ɗin ka’in da na’in ta yadda za mu farfaɗo da harkokin rubuce-rubucenmu, duba da cewar harkar yanar gizo duniya ce a tafin hannu. Da yawa mutane yanzu wayar hannu ta zama tamkar mahaɗar rayuwarsu ta yadda mutane ba sa iya taɓuka komai ba tare da ita ba, kuma ko yaya ɗan abin da za ka samu na kuɗin da za a sayi labarinka ba tare da wani jari ba, ya fiye maka jiran-jira, kare jiran tsakin mai, za a rage zafi tare da sassautawa rai ƙunci da takaici na al’amuran rayuwar nan, sannan yanzu lokaci ne da ya kamata marubuta su zage dantse tare da ƙara himmar faɗakarwa da wayar da kan al’umma duba da halin da ake ciki. Ashe ba za mu yi amfani da wannan damar ba ta irin waɗannan kafofi na sadarwa? Wannan shi ne abin da nake gani ya dace mu yi a mahangata. Shi zamani idan ya zo dubawa ake, a yi amfani da abin da zai ciyar gaba a watsar da akasin haka.

Shin har yanzu kina da sha’awar ci gaba da rubutu? Kuma yaya ki ke ganin za ki sake dawo da mu’amalarki da masu bibiyar rubutunki yanzu da harkar rubutu ta koma onlayin?

Da gasken-gaske kuwa! Rubutu tashi na yi ina yin sa cikin ikon Allah kuma Annabi (SAW) ya ce, “Ka yi amfani da damarka tun kafin ta kuvuce maka.” To, mai zai hana ni rubutu idan ba ikon Allah ba? Kuma a wani ɓangaren ina da matuƙar ra’ayin rubutu ƙwarai da gaske, in sha Allahu zan ci gaba ba zan fasa ba da yardar Allah Ta’ala.

Dawo da mu’amalata tare da makarantana tuni nasa ɗanba, ga shi nan na fara rubuta littattafaina a shafina na dandalin sada zumunta na fesbuk, kuma in sha Allahu sai na kammala labarin littafin na ɗaya kyauta ga makarantana waɗanda na sani da waɗanda ban sani ba. A wani ɓangaren kuma za a riqa karantawa a kafofin yaɗa labarai in sha Allahu, domin nan ma hanya ce da za ta sake haɗa alaƙa tsakanina da masu bibiyar rubutuna.

Ba mu taƙaitaccen bayani kan littafin da ki ke fitarwa ta shafinki na Facebook, ‘Kanya Ta Nuna’. Sabon littafi ne ko tsoho?

‘Kanya Ta Nuna…’ ba sabon littafi ba ne, tsohon littafina ne kamar yadda na faɗa a baya. Shi ne ma littafi na farko da na fara ɗab’i a shekarar 2002. Amma duba da zamani da yanayi, ina zamanantar da labarin duk da cewar ban sauka daga kan ainahin jigon da na saka zaren labarin tun asali ba; kuma ina yi wa makarantana albishir in sha Allahu su ma ragowar littatafaina haka zan riƙa dawo da su ina zamanantar da labaran ciki daidai da zamanin da muke ciki ɗaya bayan ɗaya, kamar yadda na fitar da su a baya, bi da bi.

Ban da manhajar Facebook da WhatsApp da marubutan onlayin suke fitar da rubutunsu, akwai masu karantawa a YouTube, shin ke ma kina tunanin buɗe naki shafin ne?

Da izinin Allah kuwa har Instagram da YouTube za a ga na vulla da rubuce-rubucena, komai a hankali ake bi. Na san in sha Allahu da sannu-sannu idan makarantana suka samu labari za su riƙa bibiya su karanta, kuma dama buƙatar maje Hajji sallah, in dai an gani an karanta kuma an samu abin da aka amfana a cikin labarin to, buƙatata ta biya, duk da cewar rabona da rubuta littafi kimanin shekara tara kenan, musamman ma da yanzu ya zama kai ya waye sosai, kusan kowa ma yana onlayin ɗin kamar yadda na yi bayani a baya. Yanar gizo yanzu ta zama duniya a tafin hannun mutane! Don haka ina nan tafe zan buɗe shafi a YouTube, in sha Allahu.

Za mu ci gaba a mako mai zuwa, in sha Allah.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *