Zargin cin hanci: Gwamnatin Kano ta dakatar da manajan kamfanin KASKO

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

A wani yunƙuri da gwamnatin jihar ke yi na yaƙi da cin hanci da rashawa, Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya bayar da umarnin dakatar da Manajan daraktan kamfanin samar da aikin gona na Kano (KASCO), Dakta Tukur Dayyabu Minjibir.

Ta cikin wata sanarwar da Babban Sakataren yaɗa yada labaran Gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya sanya wa hannu, ta ce Gwamnan ya bayar da umarnin dakatarwar ne a Laraba, wanda Sakataren Gwamnatin jihar Kano, Dr. Abdullahi Baffa Bichi ya miƙa.

An dai dakatar da Manajan Darakta ne bisa zargin hannu a sayar da hatsin da bai dace ba na Gwamnatin Jihar Kano.

Ya bada umurnin binciken gaggawa yayin da Gwamna ya nanata alƙawarin rashin haƙurinsa a kan cin hanci da rashawa,

An kuma umurci Dakta Dayyabu da ya miƙa al’amuran kamfanin ga babban jami’i a hukumar nan take har sai an kammala bincike.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *