“Ilimin ‘ya mace har mijinta ke amfana”
Daga AISHA ASAS
Mai karatu barkan mu da sake ganin zagayowar sati lafiya. Kamar kowanne mako, shafin Gimbiya na yi maku tanadi na musamman wanda muke da tabbacin mata za su amfana ta vangarori da dama, ya Allah ya zama ƙwarin gwiwa ga wasu, wasu ya zama ilimi da zai taimaka masu wurin miƙewa neman na kai, yayin da yake zama allon kwaikwayo don saisaita rayuwarsu bisa ga turba da za ta tsirar da su.
A wannan satin, mun samu baƙuncin wata matashiya da ta ɗauki sana’a da muhimmanci, mai sana’ar ‘yankunne ce, kuma mai sana’ar man gyara gashi da kuma wasu daga cikin kayan ƙawa na mata.
A tattaunawar Blueprint Manhaja da ita, matashiyar da ta yi zurfi a karatun boko, ta bayyana muhimmancin sana’a da matsayin ta ga rayuwar ‘ya mace. Kafin wasu shawarwari da ta ba wa mata.
Idan kun shirya, Wakiliyarmu. AISHA ASAS, ce tare da Malama Hafsat Ya’u:
MANHAJA: Za mu so jin tarihin rayuwarki a taƙaice.
HAFSAT YA’U: Sunana Hafsat Ya’u Adamu, ni ‘yar asalin Jihar Katsina ce. An haife ni a garin Shagamu, Jihar Ogun, shekara ta 1992. Na fara karatun primary a N.P.A Staff School Lagos, na ƙare a S-tee international school, sannan na je F.G.G.C Gusau na yi secondary, daga nan kuma na wuce ABU Zaria na yi degree a Microbiology. Sannan kuma na yi aure a garin Gusau, Jihar zamfara. Ina da yara biyu, alhamdu lillahi.
A yanzu me ki ka sa gaba, aiki ne ko sana’a?
Sana’a gaskiya, duk da cewa ana neman aikin, koda kuwa aikin ya samu, ba wai barin sana’ar zanyi ba.
Me ya sa ki ka fi son sana’a fiye da aiki?
Na zavi sana’a fiye da aiki saboda jin daɗi na, sannan abu ne wanda ko da zan yi aikin zan haɗa da shi. Turawa suna cewa “do something you love” to gaskiya Ina son sana’a duk da ban yi tunanin zan yi sana’ar ba ni da kawai aiki daga baya da na fara sana’ar sai na ji hankali na ya kwanta da ita.
Ba mu labarin sana’ar da ki ke yi da dalilin da ya sa ki ka zaɓe ta.
Gaskiya na yi sana’o’i da yawa tun Ina jami’a na fara, amma sana’ar yankunne ita ce na fara, babana shi ya fara saro min ‘jeweleries’ daga ‘trade Fair’ a Lagos da kanshi. Gaskiya na ji daɗin siyar da ‘jeweleries’ ɗin sosai lokacin Ina Gusau, don can ni ke aure. Daga baya da suka ƙare sai na maida kuɗin a ƙaro, amma tunda hutu ya ƙare zan koma makaranta sai na ce ma mamana ta siya min ‘fashion earrings’ na ‘yanmata aka siyo na tafi da su, da yake lokacin banda ilimin kasuwancin sosai sai na kasa sayar da su yanda na sayar dana farko haka na yi ta yawo da su daga baya ma sai dai inyi ta kyautar da su, to lokacin sai na ƙyale sana’ar ‘jeweleries’ ɗin kawai na ce idan anyi hutu zan sari wani abin daban.
Haka aka yi hutu sai mamana da yake tana tava sana’o’i sai ta aiko min da takalma ‘flat shoes’ da gwanjo na mata ‘Pakistan wear’ in siyar. Su kuma sai aka samu matsala gabaɗaya kuɗin su ya tafi a bashi ga shi ni ina da kunyar buɗe baki ince a biya ni bashi, wallahi haka kuɗin ya tafi a bashi sai waɗanda suka ji tsoron Allah suka biya ni, ‘still’ na ƙara saro hijabai daga Zariya, su kam ba laifi an biya ni kuɗinsu, sannan sai na samu wata ‘yar’uwar miji ta ƙwarai, idan na saro hijaban sai ta amsa gabaɗaya ta sayar ƙarshen wata haka zata haɗa min kuɗina cik daga baya ma ta ba ni shawarar in saro har da zannuwan gado. Kaka aka yi sai in saro su tare hijaban in bata dukka ko da ko ba ni gari da zaran qarshen wata ya yi haka za ki ga ta kira ni ta ce min ga kuɗina ya taru.
Abinda ya hana mu cigaba da haka sun buɗe restaurant kuma ita ke kula da wurin, don haka sai ayyuka suka mata yawa, sai na daina wannan sai kuma mijina ya saro min man allayadi da yake Ina yawan amfani da shi ga yarana ina ganin kyan shi Ina faɗa mi shi shi ne ya saro min ko zan dinga sayarwa na fara sayar da shi ne sai muka bar Gusau saboda matsalar tsaro, muka dawo Kaduna. A Kaduna ne na koma sana’ar yankunne, amma wannan karon sai na ce, ‘online marketing’ zanyi kuma na yi, alhamdu lillah ina samu Ina jin daɗi gaskiya.
Ko kin fuskanci wata matsala yayin da ki ka fara wannan sana’a?
Eh gaskiya matsalar da na fara fuskanta ita ce, rashin son shiga cikin mutane da nike da shi kuma sana’a ita sai da mutane kana buƙatar jama’a dayawa don su ne masu siyan kayan idan ba mutane kam ba sana’a, sannan na biyu shi ne bashi, bashi ya fi komai matsala a sana’a. Da ace za a dinga ɗaukar bashin ne ana biya akan lokaci ba matsala, amma wani idan ya ɗauka kamar yaci gado ne bai ma qara waiwayar ka da sunan biya, kinga kenan sai a tashi ba uwa ba riba.
Sannan sai kuma rashin samun ingantaccen ilimi akan sana’ar lokacin da na fara kawai na faɗa sana’ar ne don samun wani hanyar shigowar kuɗi ba tare da sanin shin nawa ya kamata in ɗaura riba na, ya zan yi lissafin ajiya, ya zan jawo hankalin mutane zuwa ga sana’ar tawa sannan me ɗan fuskanta yayin sana’ar. Kinga duk waɗannan kana buƙatar wane da ya daɗe a sana’ar ya ilmantar da kai.
Ta wacce hanya ce ilimin ‘ya mace zai iya amfanar da ‘ya’yanta?
Mace ko mu ce uwa ita ce makaranta ta farko wurin yaranta, ita ce mallamar farko da zata koyar da ‘ya’yanta abubuwa idan ba ilimin ta ya yaranan zasu koya? Babu sai dai idan sun girma an kai su makaranta su koya a can tunda shi uba ba kullum ne yake zaune a gida, sannan duk abinda aka koyo musu a waje ko da ba haka ba ne haka zata bar su da shi tunda ita bata da ilimin akan hakan.
Kinga ko ilimin na da amfani ga uwar sosai, sannan ilimin nan fa ba ga ‘ya’yanta ba ne kawai zai yi amfani ba, har ga miji da al’ummar da ke zagaye da ita.
Ilimi kan sa mace ta zama jajirtacciya akan yaranta, sannan ta san yadda zata tafiyar da yaranta a kowanne halin rayuwa suka samu kansu.
Menene matsayin sana’a ga ‘ya mace a wannan zamani da muke ciki?
Sana’a ga ‘ya mace kam a wannan zamanin ta zama jigon rayuwar ‘ya mace, ba wannan zamanin ba kawai har wanda aka baro da wanda za a shiga. Kamar yadda mawaƙiya Barmani Choge ta ce, “wacce ba ta sana’a aura ce.” In dai mace ba ta aiki gaskiya ya kamata ta kama sana’a.
Da wannan sana’ar ne za ki taimaki duk wani da ke tare da ke, miji duk kuɗin da ke gare shi indai matar shi zata sa kuɗin hannunta ta siya ma shi ‘yar kyauta yana jin daɗin hakan sosai.
Idan ba sana’ar da wane kuɗi zata siya mishi?
Ko kuma da wane kuɗi ne zata jefa sadaka ko ta ba wasu mabuƙata? babu sai ta wurin miji ko iyaye ko wani ɗan uwa idan an bata.
Wasu matan kan ce ba za a iya haɗa taura biyu a tauna su a lokaci guda ba, na daga aiki ko sana’a da kuma kula da iyali. Menene ra’ayinki?
Duk abinda mace zata yi ya kamata ta san yadda zata tsara tafiyar da wannan abin nata bare aka ce matar aure, kinga ga miji ga yara ga kasuwa kowa na buƙatar lokacin shi. Dole za ki tsara kada wani ya takura wani hakan shi zai sa a samu daidaituwa har akai ga cimma buri.
Wasu matan na kukan ba su da jari ne shi ya sa ba sa yin sana’a. Wacce shawara ki ke da ita gare su?
Duk wacce ke kukan rashin jari ne ya hana ta sana’a, to bata shirya sana’ar ba. In har kina da waya sannan kina sa mata data, to gaskiya ba sai da jari ba. Kina iya abinda ake ce mishi ‘dropshipping’ ma’ana kiyi yarjejeniya da wata ko wani ɗan kasuwa kina tallata kayanshi, kina ɗora taki riban da ansamu mai siya ya siya zai turo miki naki riban ya ɗauki nashi kuɗin ya tura ma mai siye kaya. Kinga anan ba ki buƙatar jari iyakar ki talla.
Sanar da mu irin ƙalubalen da ki ka dinga cin karo da su a sana’ar da ki ke yi.
Ƙalubalen kam ga irin nawa sana’ar shi ne siyen kaya masu ƙarancin kwaliti irin ‘yankunnen da ‘yan kwanaki za a ce sun yi baƙi ko kuma in sayar da agogo ace min agogo baya aiki ko ya tsage gaskiya raina na baci da haka sai inga kamar ban kyauta ma kwastomana ba wurin ba su abu marar kyau.
Sannan akwai matsalar kula da kaya wurin direbobi duk aka kai kaya tasha nakan ce a tunatar da su don Allah ‘yankunne ne ko agogo su kular min da shi, saboda ‘yankunne na karewa haka agogo na fashewa.
Nasarori fa?
Nasarori kam an samu da dama, alhamdu lillah tun Ina tallata kayan maƙwabciyata Ina sayarwa har na zo na fara shiga cikin kasuwa Ina sarowa da kaina yanzu har ‘yan sari ƙarƙashina nike da su. Alhamdu lillah. Har ma Ina turawa garuruwa.
Wane buri ki ke da shi kan sana’ar da ki ke yi?
Burina shi ne, idan yau aka yi maganar ‘yankunne, sarqa da agogo, to sunan Hafsat Adam ya biyo baya. Ina da burin kasuwata ta ƙara bunƙasa, Allah ya cika mun burina. Amin.
A wannan yanayi da muke ciki na hauhawan kusan komai na amfanin yau da kullum. Wane kira ki ke da shi ga mata kan taimaka wa mazajensu?
Don Allah ‘yan’uwana mata a miqe a kama sana’a, a daina cewa komai sai miji ya yi. A tausaya ma mazan nan suna iyakar ƙoƙarin su, sai dai suna buƙatar taimakon mu ba wai komai sai maigida ya yi ba, yau maigida idan ya tashi bai da na cefane, kuma kinsan ya saba, yi siya ki taimaka ki yi zai ji daɗi, ya ƙara girmama ki a zuciayar shi. Amma kinga idan ba aikin ko sana’ar da ya za a yi taimakon sai dai a dinga jin haushin juna. Saboda talauci idan ba tawakkali na sa ma’aurata su yi ta jin haushin juna.
Sannan duk mace mai sana’a tana buƙatar ‘support’ na mijinta idan har mace ta samu goyon bayan mijinta akan sana’arta, to ta yi maganin kaso tamannin wurin daidaita gida da kuma sana’arta.
A nawa ra’ayin kam duk abinda mace zata yi a gidan miji ta yi don Allah, sannan don ‘ya’yanta, wani namijin da kiyi da kar ki yi duk ɗaya ne, shi ba zai yi ba, to kinga ko ba za ki biye ma wai idan ya gaji zai yi ba dole ki yi don kanki ko don yaranki.
Wani ko idan ya ga kema kin share wannan ɗawainiyar kin ƙi yi, to yana jin ba daɗi sai ya yi, kinga ya danganta daga irin mijin da mace take aure.
Amma duk namijin kwarai daya san kanshi ya san ƙimar shi ta namiji ba zai sakar ma matar shi ɗawainiyar da shi ya kamata ya sauke ba.
Sannan macen da ta cire ƙyashi take ɗawainiyar gidanta ba tare da ta damu shin mijinta cutar ta da ita yake ya sakar mata hidimar, tabbas ba zata nema ta rasa ba saboda tana abubuwan ta domin Allah ne don haka Allah bazai bari ta taɓe ba.
Ta yaya mace za ta iya tallafawa mijinta idan ya kasance yana da wata mata bayan ita, shin za ta ba shi tallafi ba tare da la’akari da zai iya yi wa ɗayar hidima a ciki ko kuwa za ta tsaya a iya kanta. Wane ne ya fi?
Kamar yadda na ce a sama duk abinda za ka yi a rayuwa ka yi saboda Allah don mace ta taimaka wa miji shi kuma ya yi ma kishiya hidima ai ba faɗuwa ta yi ba bare idan har hidimar nan ta dole ce kamar ta ɓangaren ciyarwa ko magani, idan ana son cigaba a rayuwa dole sai mun kasance masu haƙuri da kauda kai.
Mun gode.
Ni ma na gode.