Matar da har yau ban san ta ba ce ta koya min yadda zan gyara rubutuna – Zee Kumurya

Rashin haɗin kan marubta onlayin ne ya fi damuna”

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

A wannan makon muna ɗauke ne da tattaunawar da wakilin Blueprint Manhaja Abba Abubakar Yakubu ya yi da marubuciya Zainab Shehu Abdullahi, wacce aka fi sani da Zee Kumurya. A cikin tattaunawar tasu za ku ji yadda ta fara samun kanta a harkar rubutun adabi, da buƙatarta na ganin an samu haɗin kai da kyakkyawan jagoranci a tsakanin marubuta. A yi karatu lafiya.

MANHAJA: Ina son ki gabatar mana da kanki?

ZEE KUMURYA: To, Alhamdulillahi. Cikakken sunana shi ne Zainab Shehu Abdullahi, wacce aka fi sani da Zee Kumurya. Ni marubuciya ce daga Jihar Kano, kuma mamba a ƙungiyar marubuta ta Mikiya Writers Association.

Menene tarihin rayuwarki?

Ni haifaffiyar Jihar Kano ce a Ƙaramar Hukumar Tarauni. A nan na yi karatuna na firamare da sakandire. Sannan kuma na yi karatu a matakin diploma a fannin tafiyar da harkokin ma’aikata da jama’a, wato Public Administration, daga Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kano.

Wanne abu ne ya fara jan hankalinki har ki ka fara sha’awar zama marubuciya?

Na taso ina da sha’awar karance-karancen littattafan Hausa sosai tun ina da qananan shekaru. Kuma har daga baya na fara tunanin ni ma in rubuta nawa labarin.

Wa ya fara koya miki dabarun yin rubutu da shawarwarin da suka taimaka ki ka samu gogewa a kan rubutu?

Wata mata ce, da ban san ta ba, ban kuma san sunanta ba. Na san za a yi mamaki to, amma yadda abin ya faru shi ne, ta karanta wani labarina ne sai ta ce ya yi mata daɗi, amma akwai gyara a cikinsa. Daga nan shi ne ta bani shawarwari kan yadda zan gyara labarin da rubutuna gaba ɗaya. Ba zan tava mantawa da ita ba, duk da har yanzu ban san ta ba.

Za ki iya tuna labarin da ki ka fara rubutawa, a kan me ki ka yi labarin?

Na fara rubutu ne da wani labarina mai suna ‘Muneefa’, wanda na yi shi a kan cin amana da yaudarar da wasu samari kan yi wa ƴanmata.

Wanne ƙalubale ki ka fuskanta a farkon fara rubutunki?

Rashin yin sharhi daga makaranta, ya dakushe min gwiwa sosai a farkon fara rubutuna. Na riƙa tunanin ko labarin ne bai da daɗi, har ma dai na fara ji kamar na haqura da rubutun ma gabaɗaya.

Kawo yanzu kin rubuta littattafai sun kai nawa? Kawo sunayensu da taƙaitaccen bayani kan uku daga ciki?

Na rubuta littattafai guda shida, da suka haɗa ‘Muneefa’, ‘Shi Ne Rayuwata’, ‘Abin da Ka Shuka’, ‘Neehal’, ‘Komai Nisan Dare’, da kuma ‘Yi Wa Kai’. Shi labarin ‘Abin da Ka Shuka’, labari ne a kan wani matashi wanda mariƙiyarsa ta nuna duk duniya ta fi kowa son shi a zahiri, amma a baɗini kuma ƙoƙarin kashe shi take yi, saboda dukiyar da aka tsince shi da ita ta zama mallakinta ita da ƴaƴanta.

Shi kuma labarin ‘Neehal’ a kan wata yarinya ne, da aka kashe iyayenta tun tana da ƙananan shekaru. Danginta kuma suka kasa riƙe ta. Hakan ya sa ta fuskanci ƙalubalen rayuwa iri-iri.

Labarin ‘Yi Wa Kai’ kuwa a kan wata mata ne, da ta raina samun mijinta da abin da yake yi mata, saboda tana cikin wani zaure na WhatsApp na matan masu kuɗi, sai ta riƙa hangen abubuwan da suke cewa mazajensu na yi musu.

Wanne labarin ne za ki iya cewa shi ne ya fara fitar da sunanki cikin marubuta, har aka fara gano basirarki?

Littafin ‘Neehal’ shi ne zan iya cewa bakandamiyata a halin yanzu, saboda a dalilinsa ne na samu mabiya da yawa, kuma mutane suke yabawa da basirata.

Wanne salon labari ki ka fi sha’awar rubutu a kai, soyayya ko almara ko zamantakewa?

Gaskiya na fi sha’awar rubutu a kan soyayya. Saboda na yarda cewa, soyayya gishirin rayuwa ce, kuma duk wani abu na rayuwa da ya yi kyau a dalilin soyayya ne, in ma bai yi kyau ba rashin ingantacciyar soyayya ce ta sa komai ya lalace. Kodayake a nan ba ina nufin lallai soyayyar ta zama irin soyayya ta tsakanin saurayi da budurwa ba.

Wacce ƙungiyar marubuta ki ke, kuma me ya ja hankalinki ki ka shiga?

Ina cikin waɗanda suka kafa ƙungiyar marubuta ta Mikiya Writers Association, kuma mun kafata ne domin kawo sauyi a harkar tafiyar da ƙungiyoyin marubuta da inganta rubuce-rubucen Hausa.

A ganinki wacce rawa ƙungiyoyin marubuta ke takawa wajen inganta rubutun mambobinsu?

Zan yi magana kan abubuwan da ƙungiyata take yi, don ban san yadda sauran ke gudanar da nasu tsarin ba. Amma mu a ƙungiyar mu ta Mikiya muna koyawa juna dabarun rubutun adabi da yadda za a kiyaye ƙa’idojin rubutu. Har ma da shirya gasar rubutun gajeren labari a tsakanin mambobin mu, domin ƙara musu gogewa a harkar rubutun labari, da shiga manyan gasanni da ake shiryawa lokaci zuwa lokaci.

Yaya za ki danganta cigaban da marubuta ke samu a yanzu da ake samar da zaurukan koyar da dabarun rubutu, savanin a baya?

A gaskiya wannan ba ƙaramin cigaba ba ne aka samu a harkar rubutun adabi na onlayin, domin a baya ba a samun haka, kowa na rubutu ne gwargwadon iliminsa da fahimtar sa, babu wani tsari na musamman. Amma yanzu sakamakon sadaukarwa da hoɓɓasan da wasu marubuta ke yi ana samun zauruka daban daban da ake tattauna batutuwa na ilimi da ilimantarwa a kan rubutu.

A yanzu rubutun onlayin ya samu canji sosai fiye da da, marubuciya ko marubuci na zaune a cikin gida a ɗakinta za ta koyi yadda za ta inganta rubutunta da kasuwancin littattafanta daga wayar hannunta, saɓanin a baya da sai dai ka nemi bugaggun littattafai na koyon rubutu, ko kuma ka je wani ya koya maka. Ka ga muna da zauruka irinsu Aji Na Musamman, wanda Malam Jibrin Adamu Jibrin Rano ke jagoranta, ga kuma zauren Marubuta na Bamai Dabuwa, da sauran su.

Kin taɓa shiga wata gasar marubuta, kuma wacce nasara ki ka samu?

Na tava shiga wacca muka yi a ƙungiyarmu ta Mikiya har na zo ta biyu, kuma an ba ni shaidar karramawa da kyaututtuka.

Kin taɓa samun wata shaidar yabo ta karramawa ko wata kyauta ta bazata da ba za ki taɓa mantawa da ita ba?

Sai dai addu’o’i da fatan alkhairi.

Wasu daga cikin marubuta na ba da shawarar a riƙa samun auratayya a tsakanin marubuta, kina ganin hakan zai ƙara ƙarfafa zumuncin ku?

E, wannan gaskiya ne ina goyon bayan haka. Kodayake na san akwai wasu da suka yi irin hakan a baya tun kafin bayyanar tsarin rubutun onlayin. In dai akwai so da ƙauna da fahimtar juna, zai ƙara qarfafa zumunci sosai.

Wanene saurayinki a marubuta?

Gaskiya ba ni da saurayi a cikin marubuta, sai dai abokan zumunci da ake mutunta juna.

Wacece babbar aminiyarki a cikin mata marubuta?

Aminaina guda biyu ne, Na’ima Sulaiman Sarauta da A’isha Adam Cool.

Kina da wata gwana ko gwani cikin marubuta da za ki ce rubutunsa na burgeki?

Akwai marubuta da dama da nake sha’awar karanta labaransu, amma gaskiya na fi jin daɗin karatun littattafan ƙawayena, Na’ima Sulaiman Sarauta, A’isha Adam Cool, da Nazeefa Sabo Nashe. Gaskiya rubutunsu yana burgeni sosai.

Kina ganin me ya sa marubuta ba su cika karanta littattafan ƴan’uwansu marubuta ba, musamman da zarar su ma sun fara yin fice?

Ni dai a gaskiya ina kyautata zaton rashin lokacin karatun ne. Ba wai don wani abu ba.

Wacce shawara ki ke da ita ga marubuta, game da wani abu da yake tsaya miki a rai?

Mu haxa kanmu, mu zamo tsintsiya maɗaurinki ɗaya, rashin haɗin kai tsakanin marubuta, musamman mu na onlayin, shi ne abin da yake damuna.

Wanne abu ne marubuta ke buƙatar a ce sun samu don cigaban harkar rubutun adabi?

Ina burin in ga marubuta sun samu kyakkyawan shugabanci, kuma ya zama hukuma ta shiga cikin lamarin, don kawo gyara da cigaban harkar adabi bakiɗaya.

Menene ra’ayinki game da sabbin manhajojin sayar da littattafai na yanar gizo da ake samu, kina ganin ana samun alheri a ciki, ko kin fi gane wanda aka saba?

Babu shakka fitowarsu alheri ne ga cigabanmu. Domin marubuta na samun alheri sosai a cikinsu.

Na gode.

Ni ma na gode.