Henderson ya koma Al-Ettifaq ta Saudiyya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Kyaftin ɗin Liverpool, Jordan Henderson ya koma Al-Ettifaq mai buga babbar gasar ƙwallon ƙafa ta Saudiyya.

Ɗan ƙwallon tawagar Ingila, mai shekara 33 ya amince da ƙunshin yarjejeniyar fam miliyan 12 har da ƙarin tsarabe-tsarabe.

A sakon ban kwana da ya yi wa Liverpool, ya ce zai bar ƙungiyar inda ya yi kaka 12, wadda ya lashe firimiya da Champions League a ita da sauran nasarori.

Henderson yana Liverpool tun bayan da ya koma Anfield daga Sunderlandn kan fam miliyan 20 a watan Yunin 2011.

Ya buga karawa 492 da cin ƙwallo 33 da bayar da 57 aka zura a raga ya kuma ɗauki kofi bakwai a Liverpool.

Henderson zai yi aiki a ƙarƙashin Steven Gerrard, wanda shi ne kocin Al-Ettifaq.

Mutanen biyu sun taka leda tare a Liverpool daga baya Gerrard ya bar Anfield a 2015.

Henderson ya zama kyaftin ɗin Liverpool a 2015, wanda ya ja ragama ta lashe gasar zakarun Turai a 2019 daga baya ta ɗauki UEFA Super Cup da Fifa Club World Cup a kakar gaba.

Haka kuma Al-Ittihad ta taya wani ɗan wasan Liverpool, Fabinho kan fam miliyan 40 ranar 14 ga watan Yuli.