Karamcin marubuta ne ya sa na zama marubuciya – Fadila Lamiɗo

“Ba ƙaramar asara masu satar fasaha ke jawo wa marubuta ba”

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Marubutan Jihar Kaduna kamar na sauran jihohi na ba da gagarumar gudunmawa ga cigaban harkokin adabi. Kama daga matakin ƙungiyoyi har zuwa a ɗaiɗaiku, Jihar Kaduna ta kasance sahun gaba wajen ƙyanƙyashe jajirtattun marubuta, masu ƙwazo da basira wajen ƙirƙirar labarai da ayyukan adabi iri daban daban.

Fadila Lamiɗo, ɗaya ce daga cikin irin waɗannan marubuta masu ƙwazo da himma, kuma tun fara rubutun ta a shekarar 2016 ta samu karɓuwa da shahara cikin lokaci ƙanƙani. Ta kasance daga cikin matasan marubuta na onlayin da ake matuƙar girmamawa, saboda jajircewarta a harkar rubutun adabi. A zantawarta daAbba Abubakar Yakubu, marubuciyar ta bayyana masa yadda sabuwar fasahar ɗora labari a manhajar YouTube ke canza rayuwar marubutan onlayin.

MANHAJA: Zan so ki fara gabatar da kanki.

FADILA: To, Alhamdulillahi. Ni dai sunana Fadila Lamiɗo. Ni marubuciya ce, ‘yar kasuwa, kuma uwa.

Mene ne taƙaitaccen tarihinki?

An haife ni a Jihar Kaduna, a wata anguwa da ake kira da Kwanar Cancangi, a ƙaramar Hukumar Kaduna ta Kudu, a ranar 2 ga watan Fabarairu 1994. Na yi karatuna na firamare a makarantar firamare ta L.E.A da ke Faki Road a cikin garin Kaduna. Sannan na tafi makarantar sakandiren ƴan mata ta G.G.S.S Giwa.

Bayan na kammala ne kuma aka yi min aure. Shekara biyu baya, sai na sake komawa makaranta, inda na yi karatu a vangaren kiwon lafiya a matakin diploma. Ina gamawa kuma sai na fara aiki da wani kamfani mai suna Queens Mobile Agent. Har yanzu ina tare da mijina da yarana huɗu, sannan kuma ina tava kasuwanci.

Waɗanne abubuwa ne suka faru a rayuwarki da za ki iya cewa su ne suka mayar da ke Fadila ta yanzu?

Abubuwa da dama suna faruwa waɗanda su ke iya canza yanayin mutum, amma abin da zan iya cewa ya mayar da ni Fadila ta yanzu shi ne rasuwar mahaifiyata, a lokacin ne na gane ashe a baya ban san abin da duniya take ciki ba. Wannan ya sa na tsinci kaina a wani yanayi da na mayar da komai ba komai ba. Duk wani abin da zai dame ni ba na sa shi a kaina, a kodayaushe ina ƙoƙarin yin mu’amala ne da abubuwan da za su sani farin ciki.

Me ya ja hankalinki ki ka fara sha’awar rubutun littafin Hausa?

Yawan karance-karancen littattafan Hausa tun ina ƙarama shi ne ya jawo hankalina har na fara rubuta labari, tun lokacin ana rubutawa a takarda, sannan ba a fara rubutu a onlayin ba. Sai dai a wancan lokacin ba na yin nisa nake ajiyewa. Sai daga lokacin da aka fara rubutu a shafukan sada zumunta ne na sake jarabawa na ga ya karvu, jama’a na jin cigaban labarin.

Wa ya fara nuna miki yadda za ki yi rubutun littafi, kuma wanne labari ki ka fara rubutawa?

Ni kaɗai na fara rubutana, kuma ba na yi ne da niyyar na zama marubuciya ba, kawai shafi ɗaya na rubuta na xora a wani zaure na Facebook, domin a lokacin ban san kowa daga cikin marubuta ba. Yanayin yadda na ga jama’a na jiran cigaban labarin shi ya ba ni ƙwarin gwiwar rubuta wani shafin. Littafin da na fara rubutawa sunansa ‘Za Ki Gane Kuren Ki’.

Wanne ƙalubale ki ka fara fuskanta a farkon fara rubutunki, daga gida ko daga abokan rubutu?

Babu wani ƙalubale da na fuskata gaskiya, don inda a ce na fuskanci wani ƙalubale da wataƙila ba na cikin marubuta a yanzu. A lokacin abin bai shiga raina sosai ba, marubutan da nake ganin sunansu daga nesa su ne suka yi ta jawoni cikin su har na saki jiki na cigaba da rubutu.

Kawo yanzu kin rubuta littattafai kamar guda nawa?

Na rubuta littattafai guda goma sha takwas. Sun haɗa da ‘Za Ki Gane Kurenki’, ‘Tsuntsun da Ya Ja Ruwa’, ‘Tsuntsu Mai Wayo’, ‘Mijin Marainiya’, ‘Asirinsa Ya Tonu’, ‘Ta Mishi Illah’, ‘Kowanne Bakin Wuta’, ‘Muguwar Miya’, ‘Daukan Fansa’, ‘Bugun Zuciya’, ‘Abin Da Zuciya Ke So’, ‘Baya Ba Zani’, ‘Daminar Bana’, ‘Mai Cetona’, ‘Sawun Baya’, ‘Baƙar Fura’, ‘Ba Labari’, ‘Ciwon ‘Ya Mace’.

Wanne labarin ne ya fara fitar da sunanki a tsakanin marubuta, kuma me ya bambanta shi da sauran littattafanki?

Labarina na ‘Bugun Zuciya’ shi ne ya fara fitar da sunana sosai, saboda yadda salonsa ya bambanta da na sauran labaraina. Sakamakon yadda jigon labarin ya zo sa wani irin salo da ba a saba da irinsa a wancan lokacin ba. Domin za ka ga yawancin labaran da ake yi daga karshe taurarin na cimma muradinsu, amma cikin ‘Bugun Zuciya’ taurarin ba su cika burinsu ba, kasancewar tauraron labarin ɗan daba ne.

Kuma na yi bincike sosai kafin na fara rubuta labarin, don haka na yi amfani da kalmomin da su ke amfani da su wajen furta kalamansu, wannan ya ja hankalin masu karatu yayin da marubuta suka yo kaina, wasu na jinjinawa wasu kuma na kawo min gyara saboda labarin na zuwa saɓanin hasashensu.

Ki yi mana bitar wasu littattafanki uku da suka fi samun karɓuwa a wajen masu karatu.

Littafin ‘Bugun Zuciya’ ya ƙunshi labarin wani ƙaura ne wato ɗan daba, wanda ya shahara wurin faɗace-faɗace da shaye-shaye. Ya yi ƙaurin suna sosai a unguwarsu, wanda har ya kai jama’a manya da yara na tsoron bi ta unguwar da yake. Daga bisani ya faɗa soyayya da ‘yar gidan tarbiyya, kuma masu tsattsauran ra’ayi.

Sai littafin ‘Baya Ba Zani’ wanda shi kuma labari ne da ke nuna illar sakacin da wasu iyaye ke yi wajen rashin sa ido ga yaransu da suka fara girma, ba tare da an nuna musu illar cudanyar namiji da mace ba; koda a ce akwai zumunci mai karfi a tsakanin su.

Sannan akwai littafin ‘Kowanne Bakin Wuta’ wannan labari ne da yake nuna illar aurar da yariya ga mijin da yake baƙo wanda ba ɗan ƙasa ba, kuma ba a tabbatar da ainihin su waye iyayensa ba. A ƙarshen labarin tauraruwar ta sha da ƙyar daga zuwa ƙasar dangin mijinta.

Wanne alheri ki ka taɓa samu a dalilin rubutu?

Alhamdulillahi. Na samu alheri da dama ta dalilin rubutu.

Kin taɓa shiga wata babbar gasar marubuta, kuma wacce karramawa ki ka samu?

Ban taɓa shiga wata gasa ba gaskiya, saboda a kodayaushe burina bai wuce in ga na aika wani muhimmin saƙo wanda zai faɗakar da al’ummar mu ba.

Wacce ƙungiyar marubuta ki ke, kuma wanne taimako zamanki a ƙungiyar yake miki?

Ni mamba ce a cikin ƙungiyar marubuta ta Adabi Writers Associations, kuma zamana cikin ƴan’uwa marubuta ya taimaka min matuƙa. Domin kuwa a duk lokacin da wani abu ya shige min duhu a vangaren rubutu da na kawo cikin ƙungiya za a warware min shi.

Ya dangantar marubutan Jihar Kaduna take da sauran marubutan Hausa na adabi?

Babu shakka marubutan Jihar Kaduna na da kyakkyawar alaƙa da sauran marubutan adabi na sauran jihohi, ana zumunci tare kuma yawanci ana tare da su cikin ayyukan ƙungiyoyi da halartar taruka. Lallai muna da kyakayawar danganta da su sosai.

Wanne yunƙuri ku ke na ganin kun samar da haɗin kai a tsakanin marubutan Kaduna, da inganta tsarin rubuce-rubucenku?

Zan yi magana a matsayina na ni Fadila, ba a matsayin ƙungiya ba, duk kuwa da kasancewata ɗaya daga cikin jagororin ƙungiyar Matasan Marubutan Jihar Kaduna (MAJIK). Amma kuma sha’anin tafiyar da al’amarin ƙungiya abu ne mai matuƙar wuya, domin duk yadda naso a kawo cigaba sai in da akwai haɗin kai, idan har babu haɗin kai babu wani abin da yake yiwuwa a tafiya irinta ƙungiya. Lallai akwai ƙalubale masu yawa da ake fuskata waɗanda dama can manyanmu irin su Ado Ahmad Gidan Dabino sun faɗa mana. Wannan ne ya sa har yanzu bamu karaya ba, in sha Allah na yi imanin za a samu cigaba.

Wanne ƙalubale ku ke fuskanta daga marubuta littattafan batsa, kuma wanne mataki ku ke shirin ɗauka a kansu?

To, ni dai shawarata gare su shi ne su guji rubutun batsa, su kuma sani cewa abin da suke rubutawa zai wanzu tsawon lokaci. Su tsaftace rubutun su, akwai hikimomin yin rubutun da zai ja hankalin jama’a ba tare da an yi batsa ba. Kuma da a ce sai an yi batsa ake samun ɗaukaka da manyan marubutan baya ba su samu ɗaukaka ba.

Yaya sabbin hanyoyin kasuwancin littattafai na manhaja ya inganta cinikin littattafan onlayin?

Lallai an samu cigaba da canje-canje sosai, don kuwa yanzu akwai sabbin hanyoyin yin kasuwanci littafi cikin sauƙi fiye da ka buɗe zaure a manhajar WhatsApp ka sa masu son karatun littafinka a ciki suna biyanka suna karantawa kamar yadda ake yi a da.

Wanne ƙalubale masu satar fasaha suke haifar wa marubuta na onlayin?

A gaskiya ba ƙaramar asara suke jawo wa marubuta ba, domin in da a ce babu masu satar fasaha a wannan lokacin da marubuta sun cigaba sosai, saboda ba ƙaramin alheri za a samu ba. Amma yanzu yana da wuya ka rubuta littafi wani can ya fi ka samun kuɗi a kansa. Ka ga kenan ya zama Kura da shan bugu gardi da kwashe kuɗi.

Ke ma kina karanta littattafanki a YouTube ne, kuma wacce riba ake samu da hakan?

E, ina da YouTube channel har ma da Website, kuma Alhamdulillahi ina samun alheri ba kaɗan ba, asanadin su na samu abubuwa da dama da nake kallo a sanadin Youtube da Website ɗin na same su. Da a ce marabuta sun san alherin da ake samu a cikin wannan harkar ta Website da basu yi wasa da shi ba.

Domin su ne suke da damar da za su yi harkar ta karvu cikin sauƙi, saboda wannan tsari ne da yake son mutanen da suka iya ƙirƙirar abubuwa da kansu, kuma marubuta su ne suke iya ƙirƙira labarai nasu na kansu ba tare da sun yi satar fasaha ba ko canza salon labarin da wasu suka rubuta ba.

Wanne buri ki ke da shi nan gaba a harkar rubutu?

Ban cika sa buri ba gaskiya, saboda ko na yi burin wani abu, idan babu shi a ƙaddarata ba zan samu ba. Kawai ina dai addu’a Allah Ya tabbatar min da abin da ya fi alheri a gareni.

Wanne karin magana ne ya fi tasiri a rayuwarki?

Komai nisan gari da wani a gabansa!

Na gode.

Ni ma na gode.