Raba wa ‘yan Nijeriya 25,000 ba zai yi wani tasiri ba – ACF

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ƙungiyar Tuntuɓar Juna ta Dattawan Arewacin Nijeriya, ACF ta bayyana matsayinta game da tattaunawar da aka yi tsakanin gwamnatin ƙasar da kuma manyan ƙungiyoyin ƙwadago na NLC da TUC a ranar Litinin, lamarin da ya kai ga janye yajin aikin da suka shirya tsunduma a ranar Talata 3 ga watan Oktoba.

Bayan wata doguwar tattaunawa tsakanin wakilan ƙungiyoyin da wakilan gwamnati, yanzu dai ɓangarorin biyun sun cimma matsaya wadda ta kai da dakatar da tsunduma yajin aikin nan da kwana 30 masu zuwa.

Dama ƙungiyoyin sun yi shirin shiga yajin aikin ne saboda matsin rayuwa da mafi yawan ‘yan Nijeriya suke ciki, waɗanda suka samo asali daga cire tallafin man fetur da wasu sabbin manufofi da gwamnatin Shugaba Tinubu ta gabatar.

Cikin batutuwan da aka cimma akwai biyan kuɗi da suka kai 25,000 da Gwamnatin Tarayya za ta yi a duk wata har na tsawon watanni uku ga magidanta miliyan 15 wanda za a fara daga wannan wata na Oktoba, kuma shirin zai haɗa da ‘yan fansho.

Wani lamarin da kungiyar ACF ta ce gwamnatin ya kamata ta bai wa arewacin ƙasar fifiko lokacin gudanar da shirin.

Rahoton hukumar ƙididdiga ta ƙasar kan talauci a shekarar 2022 ya nuna cewa kashi 65 cikin ɗari na mutanen dake kangin talauci na zaune ne a arewacin ƙasar.

Murtala Aliyu shi ne babban sakatare na ƙungiyar kuma a tattaunawarsa da BBC ya ce “janye yajin aikin ya fi zama alheri saboda babu abin da zai sake haifarwa sai matsin rayuwa ga masu ƙaramin ƙarfi”.

Ya ce wannan ɗage yajin aikin da ‘yan ƙwadago suka yi wata dama ce ga Gwamnatin Tarayya ta sake tuntuɓar masana, ta sake tunani kan hanyoyin da za ta fito da su domin cire mutanen Nijeriya daga ƙangin rayuwar da suke ciki.

“Duk yadda aka yi talaka ne ke wahala, ƙarin kuɗin mai kansa yake ƙarewa tsadar kayan masarufi da tashin farashin dala, wasu sabbin manufofi da gwamnati ta zo da su wanda a tunaninta za su samar da sauƙi, amma gaskiya mutane na ji a jikinsu,” in ji Murtala Aliyu.

Ya ce rabawa mutane kuɗi ba zai tava zama mafita ba ga halin da ƙasar ke ciki, saboda gwamnatin da ta shuɗe ta Buhari ma ta yi wane tasiri hakan ya yi ga rayuwar talakan Nijeriya?

Ya kuma yi kira ga gwamnatoci a kowanne mataki da su bai wa yankin arewacin Nijeriya muhimmanci yayin shirye-shiryensu, ganin cewa talakawa sun fi yawa a nan.

“Mu ne ke da ƙananan sana’o’i irin noma da sauransu, ƙaramin jari zai iya kai wa manomi ga samun nasara, shi yasa muke so a bai wa mutanenmu muhimmanci”.

Ya ce kada su kuma gwamnatocin jihohi su zubawa ta Tarayya idanu su qi taimaka mata, su ma sai sun shigo domin dai duka a kai ga nasarar taimakawa talaka.

By Editor