Ko yau na bar shugabancin Jami’ar Nasarawa na kafa tarihi – Farfesa Sulaiman

Daga JOHN D. WADA a Lafiya

A yayin da mahukuntan Babbar Jami’ar Jihar Nasarawa da Gwamnatin Jihar ke cigaba da murnar cikar jami’ar shekaru 20 da kafuwa, Wakilin Manhaja, John D. Wada, ya samu damar tattauna da shugaban Jami’ar Farfesa Suleiman Bala Mohammed inda ya bayyana nasarori da ƙalubale da jami’ar ke fuskanta kawo yanzu, da suka haɗa da shirin hura wisu wato ‘whistle blowing policy’ a Turance da ta kirkiro don gano tare da hukunta miyagun ɗalibai da malamanta, da batun ƙungiyoyin asiri da sauransu. Ga yadda tattaunawar ta kasance:

Manhaja: A kwanakin baya kun kafa wata doka ta musamman ta hura wisu wato wadda ake kira ‘Whistle Blowing Policy’ a Turance, don rage ko magance munanan ayuka a jami’ar nan. Yaya dokar ke aiki a yanzu haka?
Wannan shirinmu na musamman na hura wisu kamar yadda ka sani, ɗaya ne daga cikin muhimman shirye-shiryenmu a jami’ar nan. Kuma mun kafa dokar ne a cigaba da ƙoƙarin da muke yi na yaƙi da munanan ɗabi’u a jami’ar nan bakiɗaya. Wato bayan mun lura cewa akwai wasu munanan ayuka dake wakana tsakanin ɗalibai, da ma wasu malamanmu. Kodayake, ba ma fuskantar ƙalubalen aiwatar da dokar a kan ɗalibanmu. Ba wai da zarar aka kama ɗalibi ko ɗaliba ba da laifin nan take za a gurfanar da shi ba. Sai an fara kai shi agaban kwamiti. Kwamitin idan ya tabbatar da laifinsa, sai ya hukunta shi dai-dai da laifinsa. Kai in ya yi tsanani ma, za a sallame shi daga jami’ar kwata-kwata. Amma akan samu wasu ƙalubale a ɓangaren gano wasu malamai dake karya dokokin, kuma a yi wahalar gano su. Shi ya sa na umurci kwamitin dake kula da wannan fanni da sauran ɗalibanmu cewa, su riƙa sa ido a harkokin malaman, da ma sauran ma’aikatanmu waɗanda ba malamai ba. Kuma duk wanda aka kama da laifin, nan take sai a sanar da kwamitin don ɗaukar matakin hukunci a kansa dai-dai da laifinsa. Wannan shi muke nufi da dokar hura wisu ]in a taƙaice.

Kawo yanzu akwai wani tasiri da dokar ta yi?
Kwarai kuwa. Ba ƙaramin sakamako da nasara muke samu ta dokar ba kawo yanzu. Kuma hakan ya kasance babban darasi ga masu aikata ɗanyen aiki a jami’ar nan. A yanzu galibin waɗannan miyagun mutane sun tuba sun bar munanan ayukansu. Kuma jama’a da dama daga ciki da wajen jami’ar nan bakiɗaya a kusan kullum suna cigaba da yaba mana dangane da wannan hangen nesa da muka yi na ƙirƙirowa, ko na ce kafa wannan dokar.

Kawo yanzu kimanin ɗalibai ko malamai nawa kuka hukunta, bayan kun cafke su? 
Kodayake, a yanzu ba ni da sanin yawan waɗanda aka kama da laifin kasancewar mataimakina na fannin ilimi ne ke kula da lamarin. Wato shi yake da cikakken bayyani a kan yawan su da sauransu.

Amma za ka iya ƙimanta yawansu?
Zan ce kimanin mutum 12 ne. Kuma a yanzu da muke magana, kwamitin aiwatar da dokar yana cigaba da gudanar da bincike na musamman a kan wasu da suka ƙunshi ɗalibai da malaman da ake zargi da hannu cikin waɗannan ɗanyun ayyuka a jami’ar nan.

Ɗaya daga cikin manya kuma mahimman ajandojinka ko ince ƙudurorinka da zuwanka kujerar shugabancin jami’ar nan shi ne, tabbatar da kammalawa tare da gina sabbin gine-ginen ɗakunan karatu da sauransu. Ko ka cimma burikanka kawo yanzu?
A gaskiya ba wai yabon kai ko wani abu makamancin haka ba. Kawo yanzu akwai ayyuka da dama musamman na gine-ginen azuzuwan da sauransu, kamar yadda ka tambaya da muka faro muka kuma kammala da yardar Allah. Har ila yau, akwai wasu kuma da dama da muka faro. Kodayake, ba mu kammala su ba, amma mun kafa tubalansu. Kuma muna cigaba da taɓa ayyukan a hankali. Don kamar yadda ka sani, ire-iren ayukan cigaba na gwamnati kamar waɗannan dole sai ka bi a hankali. Don dole ne kana aikin, kana kuma yin la’akari da tanade-tanaden dokokin gwamnati. Musamman waɗanda suka shafi ayyukan bunƙasa manyan jami’o’inta kai-tsaye da sauransu, don tabbatar da gaskiya da riƙon amana a ƙarshe. Saboda haka, a taƙaice zan ce kawo yanzu kamar yadda na bayyana maka, mun iya faro tare da kammala wasu mahimman ayukan cigaba da dama a jami’ar nan a karkashin jagorancina. Kuma akwai wasu da dama da muke cigaba da yi a yanzu da lokaci ba zai ba ni damar bayyana maka dukansu ba. Kuma muna yin haka ne don mu tabbatar mun bar tarihinmu ma bayan mun bar nan. Inda za a ce lallai su wane fa sun kawo canje-canje da dama ga jami’ar nan, da yardar Allah.

Yanzu bari mu taɓo batun ayyukan ‘yan ƙungiyar asiri da ya zamo ruwan dare a jami’oin ƙasar nan bakiɗaya ciki har da taku. Yaya kuke kula da wannan mummunar lamari a nan?
A gaskiya zan iya fa]a da babbar murya cewa, batun harkokin ‘yan ƙungiyar asiri a jami’ar nan yana da sauƙi. Kodayake, ba ina nufin cewa kwata-kwata za a rasa ‘yan ƙungiyar a jami’ar nan ba. Amma a gaskiya kamar yadda na bayyana, ba ma samun rahotannin ayyukansu a nan. Idan ma suna nan, to wataƙila suna gudanar da miyagun ayukansu ne a ɓoye ba a fili ba, kamar yadda lamarin yake a wasu jami’oin ƙasar nan daban-daban. Kodayake, a kwanakin baya na samu labari cewa an kashe wani mutun a wani otal dake nan garin Keffi, kuma ana zargin wasu ‘yan ƙungiyar asiri ne da aikata kisan gillar. Amma lamarin ya auku ne a wajen makarantar nan. Kuma har yanzu ban samu wani rahoto cewa ɗalibanmu ne suka aikata ba. Amma ina sanar da kai cewa, muna nan muna sintiri na musamman tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro. Kuma duk ɗalibi ko ɗalibar da aka kama da laifin, za mu tabbatar ya yaba wa aya zaƙinta.

Akwai kuma wani zargi da wasu a jihar nan musamman iyayen yara ke yi cewa, kuna yawancin ɗaliban da kuke ɗauka, daga wajen jihar nan suka fito, maimakon daga jihar nan kamar yadda majalisar dokokin jihar nan ta umurci ku yi kwanakin baya. Yaya gaskiyar lamarin?
Na gode sosai da wannan tambaya da ka yi min. Don kamar yadda ka bayyana ne sau da yawa nakan karanta a jaridu da sauransu. Inda za ka ji wasu na waɗannan zarge-zarge marasa tushe balle makama. Kuma ina so na yi amfani da damar nan in ƙaryata, tare da musanta wannan zargi. Ina so al’ummar jihar nan da ƙasa bakiɗaya su sani cewa, wannan zargi ne kawai maras mafaka kamar yadda na bayyana. Kuma ga dukkan alamu, wasu ne da ba sa son cigaban jami’ar nan ke yaɗawa. Daga nan kana da damar ziyartar sashenmu na harkokin ɗaukar ɗalibai, wato ‘admission unit’ ɗinmu a Turance. Domin ka bincika da kanka don tabbatar da gaskiyar lamarin. Saboda haka, ba shakka duk da cewa muna ɗaukar ɗaliban da suka cancanta ne, suka kuma ci jarabawarsu ta cigaba da karatu a manyan jami’o’i. Amma ina tabbatar maka cewa, muna yin la’akari da ba da fifiko ga ɗalibai ‘yan asalin  jihar nan fiye da na waje. Saboda haka, ba zan yi wani dogon bayani dangane da wannan zargi ba. Kawai abinda zan ce a taƙaice shi ne, duk wanda ke wannan tunani, to ina yin amfani da damar nan don ƙalubalantar sa cewa, maimakon ya riƙa wannan zargi mara tushe, ya kawo ziyara ta musamman a nan za mu kuma ba shi damar gudanar da cikakken bincike a kan lamarin don ya gane gaskiyar lamarin.

A ƙarshe, a yayin da kuke cigaba da murnar cikawar jami’ar nan shekaru 20 da kafuwa, misali, Allah ya kiyaye, idan a yau aka ce gwamnati ta dakatar da kai daga wannan muƙami, waɗanne ayukan cigaba ko ince gado za ka iya bugar ƙirji cewa da kai da sauran waɗanda suka jagoranci jami’ar a baya kuka iya bari a ƙasa cikin waɗannan shekaru 20?
To, ko dai ban ce komai ba, na tabbata cewa jama’a da dama a ciki da wajen jihar nan za su shaida cewa, tabbas ina ɗaya daga cikin shugabanni da suka taka muhimmiyar rawa suka kuma ba da gagarumar  gudumawa wajen kawo sauye-sauye masu ma’ana ga fasali da harkokin karatun ɗalibai, kuma ‘ya’yanmu a jami’ar nan bakiɗaya, a kuma kowanne fanni a cikin waɗannan lokuta. Kuma tabbas a lokacina ba yabon kai ba, tarihi zai shaida cewa na kafa tubullan ayyukan bunkasa harkokin ilimi na zamani da na addini a jami’ar nan da jihar nan bakiɗaya. Wato dai kamar yadda kake gane wa idanuwanka a yanzu. Na gode.