Yadda fursunoni 252 suka tsere daga kurkukun Jos bayan kai hari

Daga HABU ƊAN SARKI

Biyo bayan wani mummunan hari da wasu mahara da har yanzu ba a tantance ko su wanene ba, suka kai babban gidan yarin Jos, dake ƙarƙashin Hukumar Kula da Gidajen Gyara Halinka ta Nijeriya, a ranar Lahadi da ta gabata 27 ga watan Nuwamba, an tabbatar da tserewar fursunoni 252, ciki har da waɗanda ake zaton an kai harin ne domin su.

Babban Kwantirola mai kula da Cibiyar Gyara Halinka ta Jos, Samuel Aguda ya tabbatar da ɗan bindiga ɗaya ne daga cikin maharan da suka kai farmakin da muggan makamai aka kashe a cikin kurkukun yayin da sauran suka tsere da fursunoni masu yawa. An kuma kashe wasu fursunoni 9, wasu 7 kuma an tsinci gawarwakin su a yayin gujewa daga gidan yarin.

A rahoton farko da hukumar ta fitar ranar Litinin, awa 24 bayan harin da aka kai, an bayyana cewa, an samu nasarar kama wasu fursunoni goma da suka gudu, yayin da wasu iyaye suka dawo da wasu guda biyu da suka koma gida.

Kwamishinan ýan sanda na Jihar Filato, Bartholomew Onyeka, ya ba da umarnin sanya wuraren binciken ababen hawa a kusurwoyi daban daban na babban birnin jihar, domin gano fursunonin da suka tsere da gano ɓatagarin da suka kai wannan mummunan hari da ta yi sanadin kashe wani ma’aikacin gidan yarin mai muƙamin Mataimakin Sufritanda, da kuma lalata ginin Cibiyar Gyara Halinka ta Jos.

Gwamnan Jihar Filato Simon Lalong wanda ya bayyana takaicin sa game da abin da ya faru, ya kuma umarci gamayyar rundunonin tsaro da ke jihar su yi duk abin da ya kamata domin gano waɗanda suka kitsa wannan hari da sauran fursunonin da suka tsere.

Wannan mummunan hari da shi ne irin sa na farko, ya girgiza jama’a sosai a ciki da wajen Jihar Filato, saboda yadda waɗanda suka kai harin suka aiwatar da farmakin cikin wani yanayi da ya shammaci kowa, har kuma suka cimma manufar su suka tafi cikin takaitaccen lokaci ba tare da cikas ba.

Tun da farko jama’a sun yi ta yabawa da ƙoƙarin da haɗin gwiwar jami’an tsaro suka yi na killace dukkan hanyoyin kai wa ga gidan yarin, amma hakan bai hana maharan tserewa ta ɓarauniyar hanya ba. Abin da ya ɓata ran gwamnati da shugabannin rundunonin tsaro na jihar.

Cibiyar Gyara Halinka da ke Jos tana makwabtaka ne hedkwatar ýan sanda ta Jihar Filato da da Hedkwatar ýan sandan farin kaya ta DSS da Babban Dibishin na ɗaya na rundunar ýan sanda, waɗanda duk suke kewaye da barikin ýan sanda da na jami’an Hukumar Gyara Halinka ta ƙasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *