Sai da na girma na shiga karatun boko – Hon. Ado Rodi

Daga MUHSIN TASIU YAU a Kano

Gwarzon ɗan gwagwarmaya kuma matashi abun koyi, Hon. Ado Idris, wanda aka fi sani da Ado Rodi, ɗan kasuwa ne kuma ɗan siyasa, Kansila Mai Gafaka (Supervisory Councilor) a Ƙaramar Hukumar Kumbotso da ke Jihar Kano. Ga yadda tattaunawarsa da Wakilin Blueprint Manhaja, Muhsin Tasiu Yau, ta kasance:

Za mu so mu ji taƙaitaccen tarihin rayuwarka
An haifi ni a 1982 a unguwar Sheka. Na taso na yi shekara uku zuwa huɗu sai aka kai ni makarantar allo. Mahaifina ɗan kasuwa ne kuma ya rasu tun muna ƙanana, ba mu girma da shi ba. Mahaifina ɗan kasuwa ne. Ya kai ni makarantar allo ni da yayana mun zauna a makarantar allo lokaci mai tsawo. Ban samu na yi makarantar boko da wuri ba sai bayan wasu shekaru, sannan na shiga makarantar yaƙi da jahilci, inda na samu shaidar kammala makarantar firamare da sakandare duka cikin shekara bakwai a Makarantar Abacha Youths Center. Kuma na zamo mai ƙwazo duba da karatun Alƙur’ani da na samu daidai gwargwado. Na samu kwalin NCE kuma.

Yaushe ka fara kasuwanci?
To, Alhamdulillahi, domin kasuwanci da ma gadar sa muka yi a wurin mahaifin mu, mahaifina ɗan kasuwa ne a ƙofar Nasarawa shagunan su ne waɗanda aka rushe su lokacin Buhari saboda haka na tashi da son kasuwanci. Don haka na tashi ba ni da kasala da rashin mutuwar zuciya. Na fara yin kara wanda ake yin girki na kawo cikin gari na siyar in samu abin da zan rufawa kaina a siri na buƙatuna, har na zo na fara zuwa kasuwar ‘yan lemo na na dinga tsinto lemo na zo unguwar mu ina siyarwa wanda a lokacin ana samun irin wanda ake tsincewa marar kyau sosai mu kuma sai mu karɓa. Daga nan sai muka juwa ɗauko su yalo da gyada da albasa da sauransu.Daga nan muka koma kamfanin Ɗangote na filawa inda muka rinqa yin dako a ciki, mun samu kamar shekara uku muna wannan gwagwarmaya daga nan muka koma kasuwa inda nan ma muke dako sabo da muna da hazaƙa ba mu daɗe ba kawai sai mukai sahawara mu fara sana’a muna juya kuɗi. Mun fara da abin da ake cewa ka-yi- na- yi, har ta kai da wani yayanmu ya yi mana faɗa gudun kada mu dauko abin da ya fi ƙarfinmu. Sai muka fara tarar masu sayen kaya mu kai su shago. Daga nan na fara zama ɗan kasuwa har na fara da samun naira dubu goma tawa ta kaina Wanda wani maigidana wanda nake saran kaya a wajensa, bayan naga na samu dubu gomar nan sai na fara tunanin ya zan yi na ƙara samun wata dubu goman don na inganta kasuwancina. Inda zan raba gomar farko na ajiyeta a waccen sana’ar wannan da na ƙara samu na riqe a aljihu na ina juya su su ma daban.

Tarihin siyasarka fa?
Farkon ubangida na da na fara ta dalilin sa shi ne Alh Jafaru ɗan Maliki, bayan na ɗan jingine kasuwanci muka fara ‘yar siyasa gadan -gadan a je nan a je can kuma a kafa nake wannan yawon siyasar in na tashi daga Ɗan Maliki sai na je Fanshekara a ƙafa na dawo, na tafi Na’ibawa a ƙafa da ma wasu wuraren da yawa duk a ƙafa. Ana cikin haka, sai aka yi sabom chairman Sagir Fanshekara a ƙaramar hukumar Kumbotso inda har ya kasance ina da albashi duk wata ana bani naira dubu hudu (N4000) kuma ni wannan dubu huɗun kallonta nake tamkar dubu dari N1000.

A wannan lokacin kuma a hakan tana kashe mun ‘yan buƙatuna har ƙarshen wata. Daga baya sai na bar gidan Sagir Fanshekara na koma gidan wani daban inda kuma cikin hukuncin Ubangiji a shekara ta 2007 sai muka faɗi zaɓe Hon Manniru Babba ya ci. Da naga haka sai nace tunda mun faɗi ya kamata na koma kasuwa tunda Ahamdullilah ina da nasibi a kasuwa. Bana mantawa na je wajan wani kwamishina akan ya taimake ni da dubu hamsin na fara kasuwancin sai ya ce bai San irin gudunmuwar da nake bayar ba a ƙaramar hukumar Kumbotso ba don haka sai ya tura ni wajan jagororin mu na wannan lokacin sai ya kasance wanda aka tura ni wajan su domin su wakilce ni suje su faɗa masa wacce irin gudunmawa nake badawa a Kumbotso sai ya kasance su wannan mutanen suka rinƙa kwan gaba kwan baya su ma kai ni wajan nasa ma sunƙi wannan kuɗin a ƙarshen dai ban same shi ba.

Ba na mantawa ranar ƙarshen muna gidan shi kwamishinan har ma muka sami sabani da wani makusancinsa a lokacin saboda bai kaini wajan shi kwamishina ba muka dai yi cacar baki da shi waɗanda ke wajen na tabbata waɗanda ke wajen wasu za su tuna. A lokacin sai wani ya ja ni waje ina tsaye a wajen ya kira wasu wanda muke tare a wajen su shiga gidan su karya inda aka ba su shayi da madara da kwai ni kuwa ko karyawa ban yi ba na zo gidan. Ban a mantawa ina ƙofar gidan ƙarshen ina ƙofar gidan sai Aminu Mai dawa ya Fito ya tambaye ni ina zan je don ya rage min hanya akan vespa. Ya kaini kasuwar Sabon gari ya ajiye ni a dai- dai kwanar da zan Shiga layinmu. Cikin hukuncin Ubangiji ban fito ba sai da wannan kuɗin da nema a ba ni. Daga ranar kuma ban fito da kuɗi ba a kullum sai na fito da naira dubu tamanin ta wannan lokacin.

A cikin ɗan taƙaitaccen lokacin Allah ya buɗe min haryar samu komai ya warwaren mun har na samu sukunin sayen muhalli. A hankula na mallaki rumfa a kasuwa na ɗauki yara kuma masu taimaka min su ma kuma na hoar da su kasuwanci wanda wasu suna ƙarƙashina a yanzu wasu kuma har sun bunƙasa su ma a yanzu suna cin gashin kansu . Wanda Alhamdulillahi wannan shi ne burin duk wani ɗan kasuwa.Kuma sana’ar da nake yi ita ce ta duk wani abu wanda ya shafi buhu kuma har gobe ita nake.

To, mai ya mayar da kai siyasa tunda har ka ma fuskanci butulcin wasu ‘yan siyasa?
Ni mutum ne mai son na taimaki Al’umma sai na ga yadda ‘yan siyasa na wannan lokacin yadda suke taimako al’umma wannan shi ya bani sha’awa sai na ga lokaci ya yi da zan koma ruwa a siyasa domin nasa al’umma farin ciki a rayuwata.

Ya ka ke haɗa kasuwanci da siyasa?
Ba zai ba da wani wahala sosai ba ko yau kafin na zo nan ofishin sai na je kamfanonin da nake mu’amala da su na dauki kaya na tura kasuwa sannan na fito nan wajan siyasa nan cikin office ɗin nan. Don ai siyasa ba sana’a ce ba ba ofishin neman kuɗi ba ne sho waje ne na bayarwa waje ne na taimakon al’umma.

Wane kira za ka yi kan matasa da suka rungumi siyasa ita kaɗai?
Ina shawartar ‘yan uwa na matasa kar ku zama sai dai a ba ku, ku zama masu bayarwa saboda in dai za ka dogara da wannan ba za ka taɓa cika burinka a rayuwa ba. Sannan siyasa ba kasuwanci ba ne abu ne da ka ke marar tabbas amma shi kasuwanci komai ƙanƙantarsa zai rufa maka asiri. Sannan in ka dage a ciki watarana za ka shahara ka kuma bunƙasa. Sannan in har kana da abin yin ka a hannu in ka shigo harkar siyasa za ka yi tasiri ba za a ganka wurin kwaɗayi ba sai dai in ka sa son zuciya. Sannan za ka yi farin jini saɓanin in an san kai ci ma zaune ne daga nesa in an hango ka za a fara tsaki ana darewa. Don haka kullum in na samu irin wannan dammar nake faɗawa matasa su yi koyi da Hon Hassan Garba Farawa chairman ɗin Kumbotso na yanzu saboda kyan halayyarsa sannan shi mutum ne jajirtacce mai dogoro da kai mai son jama’arsa su dogara da kansu duk abin da yake hidima da shi ga al’umma yana yi ne daga aljihunsa ba wai sai ya jira an turo ba. Kun ga da a ce shi ma da siyasar ya dogara kaɗai da al’umma ba su amfana da shi ba. Anan ina addu’a Allah ya taimake shi.

Wanne abu ne na farin ciki da ya taɓa faruwa da kai wanda ba za ka manta da shi ba a siyasa?
Alhadulillah, abin farin ciki da ya taɓa faruwa da ni akan Hon. Hassan Garba da ya ba ni award ne ƙarƙashin ƙungiyata ta Kumbotso sabuwa, a wajen a cikin dubban jama’a ya yabe ni sosai. sannan kuma aka naɗa ni supervisory councilor wannan naɗi har ƙwalla ya sa ni wurin saboda ban taɓa tunanin za a yi min wannan naɗin ba.

Me ka ke alfahari da shi a zamanka ɗan kasuwa kuma ɗan siyasa da ka taka matakin kansila?
Ni a kullum burina shi ne taimakon al’umma don haka a yanzu na sama da mutum arba’in aiki sannan a rumfata akwai sama da mutum sha biyar wanda a ƙarƙashina suke. Sannan ina da ɗan ƙaramin kamfani wanda shi ma akwai kusan mutum bakwai a ciki. Na fitar wa da ‘yan unguwarmu kwalbatu sannan na zuba ƙasa kuma duk wannan abubawan da na dan faɗa ba da kuɗin ƙaramar hukuma nake ba da kuɗina nake. Duk abin da muke yi a ƙungiyarmu ta Kumbotso sabuwa na tallafa wa al’umma kamar marassa lafiya da taimakon da bai gaza dubu hamsin zuwa ɗari muna yi ne aljihumnu da masu sayen magani mukan ajiye kuɗi a kemis mu ce a karɓa . Irin waɗannan abubuwa ina jin daɗinsu sosai don na ceton al’umma ne.

Mene ne kiranka na ƙarshe ga matasa?
To, ni kirana ga matasa shi ne har kullum duk wanda ba ka so ba baƙin ciki za ka yi masa ba, in ka na yi masa baƙin ciki to lallai ɗagawa sama zai yi. Don haka mu cire hassada da ƙyashi a al’amuranmu sai mu ga ci gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *