
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun halaka wani limami tare da wasu mutum uku a wani hari da suka kai a ƙauyen Illela Dawagware da ke ƙaramar hukumar Goronyo ta Jihar Sakkwato.
Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun kai harin ne da misalin ƙarfe 12:20 na daren ranar Lahadi inda suka riƙa harbe-harbe, lamarin da ya yi sanadin mutuwar Limamin mai suna Mallam Liman Lawwali Na Audu a gidansa da kuma wasu mutum uku.
Baya ga waɗanda aka kashe, maharan sun kuma yi garkuwa da mazauna ƙauyen mutum 12 tare da tafiya da su bayan gari.
Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaye sunansa, ya bayyana cewa da fari ‘yan ƙauyen sun yi yunƙurin daƙile harin, amma haka ba yiwu ba sakamakon ƙarfin makaman ‘yan bindigar.
Harin ya haifar da fargaba da jimami a tsakanin al’ummar yankin, yayin da mazauna garin ke kira ga hukumomin tsaro da su ɗauki matakan gaggawa wajen ceto waɗanda aka sace tare da daƙile hare-haren da ake cigaba da fuskanta a wasu sassan jihar.
