
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Sanannen mawaƙin Nijeriya, David Adeleke da aka fi sani da Davido, ya yi tsokaci bayan nasarar da kawunsa Ademola Adeleke ya samu na sake zama gwamnan jihar Osun.
Da yake murna kan al’amarin, Davido ya yi rubutu a shafinsa na X inda ya ce: “We did it, Uncle”, wato “Mun cimma nasara, Kawu”.
Hakan na zuwa ne bayan da Hukumar Zaɓe ta Ƙasa INEC, ta sanar da Ademola Adeleke na jam’iyyar Accord Party (AP) a matsayin wanda ya lashe zaɓen, wanda aka gudanar a ranar Asabar.
Adeleke ya yi nasara ne bayan sakamakon ƙananan hukumomin 30 na faɗin sun nuna cewa ya samu ƙuri’a 511,067, yayin da Oyebamiji na APC ya samu 444,815. Najeem Salaam na ADC kuma ya samu 17,180.
An gani a wani faifan bidiyo yadda Davido ya bayyana farin cikin kan nasarar da suka samu a zaɓen, wanda ya ja hankalin jama’a a sassan jihar.
