
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Zakaran ɗan ƙwallon ƙafa na duniya Cristiano Ronaldo, ya bar sansanin karɓar horo na tawagar ƙasar Portugal gabanin wasan da za ta yi da Denmark a gasar UEFA Nations League a yau Alhamis, yana mai cewa zai bayyana dalilinsa na ɗaukar matakin a lokacin da ya dace.
Kyaftin ɗin na Portugal ya tabbatar da haka ne a wani saƙo da aka wallafa a kafar Soshiyal Mediya a ranar Laraba, lamarin da ake ganin na da alaƙa da tsamin dangantar tsakanin sa da sabon kocin ƙasar, Jorge Jesus. Ronaldo ya ce hakan ya biyo bayan ganawar kaciyan da ‘yan jarida da kuma wata hira da Shugaban Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Portugal, Pedro Proença.
Ɗan wasan mai shekaru 41 ya ƙara da cewa zai faɗi dalilansa ga ‘yan ƙasar, yayin da ya kuma yi wa tawagar da takwarorinsa fatan samun nasara. Wannan mataki dai ya biyo bayan fargabar barin Ronaldo cikin tawagar na tsawon kwanakin rashin tabbas kan cigaba da kasancewar sa ɗaya daga cikin ‘ya’yan tawagar.
Ronaldo ya ɗumama benci a wasan da ƙasarsa ta doke Norway da ci 2 da 1 a Nations League na ranar Lahadi duk da cewa yana sahun ‘yan wasan da suka fara wasan da Portugal ta yi da Wales. Daga bisani bai samu shiga sahun atisayen tawagar ba inda hukumar ƙwallon ƙasar ta ce yana gudanar da nasa ne a keɓance.
Rahotanni gidajen jarida a ƙasar sun alaƙanta wannan hali da rashin samun isasshen lokacin wakiltar tawagar a wasanni musamman ganin yadda aka jingine shi a wasansu da Norway duk da cewa ya yi ƙwarya-ƙwaryan motsa jiki yayin wasan. Reuters ta ruwaito cewa wannan al’amari ya taimaka wa ƙarfafa rashin jituwar ɗan wasan da jami’an horarwa.
