Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
A jawabinsa bayan sanya hannu a kasafin kuɗin, gwamna Dikko Raɗɗa ya bayyana cewa sai da aka saurari buƙatar alummomi dake gundumomi 361 na faɗin jihar wanda aka sanya wasu a kasafin kuɗi.
Haka kuma gwamnan ya ce bayan sauran alummomi “Ni da kai na sai da na saurari ma’aikatu da hukumomin gwamnatin domin kare kasafin kuɗin kafin daga baya a gabatarwa majalisar dokoki”Inji Raɗɗa.
Gwamna Raɗɗa wanda shine gwamna na farko a ƙasar da ya sanya kasafin kuɗin 2027, ya yabawa Kakakin Majalisar da sauran ‘yan majalisar da kammala zama kan kasafin kuɗin kan lokaci,yayi fatan Allah bashi ikon aiwatar da kasafin kuɗin domin amfanin al’ummar Jihar Katsina.
Tunda sai da Kakakin Majalisar dokoki Rt Hon Nasiru Yahaya Daura ya jinjina wa gwamna Raɗɗa bisa shine na farko da ya sanya hannu a kasafin kuɗi da ya zama doka.
Ya kuma jaddada cikakken goyon baya da shi da ɗaukacin Yan Majalisar dokokin Jihar ga gwamnatin Dikko Raɗɗa da jam’iyar APC a jihar da ƙasa baki ɗaya.
Kakakin Majalisar ya yi kira ga al’ummar Jihar da su cigaba da ba gwamnatin Dikko Raɗɗa goyon baya a ƙoƙarinsa na aiwatar da ayyukan bunƙasa ƙasa.
