Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Ƙungiyar malaman jami’o’i ta ƙasa (ASUU), reshen Jami’ar Umaru Musa Yar’adua (UMYU) da ke Katsina, ta nuna damuwa kan bashin wasu haƙƙoƙin alawus da wasu daga cikin mambobinta ke bin gwamnatin jihar, wanda ta ce ya haura na watanni 40.
Ƙungiyar ta kuma zargi cewa an dakatar da biyan bashin alawus ɗin ayyukan ilimi (Earned Academic Allowances – EAA), wanda a baya ake biya a kashi-kashi, bayan fara aiwatar da yarjejeniyar ASUU da gwamnatin tarayya ta shekarar 2025.
Shugaban ASUU na reshen UMYU, Comrade Aminu Usman, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da ya gudanar a Katsina.
Ya ce bashin EAA da ya samo asali tun daga zangon karatu na shekarar 2022/2023, ba ya cikin yarjejeniyar da gwamnatin jihar Katsina ta cimma da ASUU kan aiwatar da yarjejeniyar ASUU da gwamnatin tarayya ta shekarar 2025.
A cewarsa, wannan alawus wani haƙƙi ne da aka riga aka samu sakamakon ayyukan da mambobin ƙungiyar suka gudanar.
Ya ƙara da cewa wasu daga cikin waɗanda suka cancanci karɓar kuɗaɗen da ake binsu sun rasu, yayin da iyalansu ke cigaba da jiran a biya musu kuɗaɗen.
Kwamared Aminu Usman ya nuna damuwa kan dakatar da biyan bashin EAA bayan fara aiwatar da yarjejeniyar shekarar 2025.
Ya ce ƙungiyar na kallon matakin a matsayin wani nau’i na hukunci, yana mai cewa ASUU ta yi imanin cewa dakatar da biyan bashin bai cikin abin da kwamitin da gwamnatin Jihar Katsina ta kafa domin aiwatar da yarjejeniyar ke da alhakin gudanarwa.
Ƙungiyar ta ce bashin da mambobinta ke bin gwamnatin ya haura watanni 40, ciki har da ƙarin albashin da ya biyo bayan ƙarin mafi ƙarancin albashi na ƙasa na Naira 70,000, da kuma ƙarin albashin kashi 25 da 35 cikin 100, tare da bashin da ya samo asali daga aiwatar da yarjejeniyar ASUU da gwamnatin tarayya ta shekarar 2025.
ASUU-UMYU ta kuma nuna damuwa kan zargin cire malaman jami’ar da ke hutun aiki na sabbatical da kuma malaman da aka ɗauka a matsayin visiting lecturers daga sabon tsarin albashi da alawus-alawus.
Ƙungiyar ta ce malaman da abin ya shafa sun koka da cewa ba a nuna sabon albashi da alawus-alawus ɗin a cikin kuɗaɗen albashinsu na watan Agusta da Satumba na shekarar 2026 ba.
Saboda haka, ASUU ta buƙaci a gaggauta dawo da biyan dukkan bashin EAA ba tare da wani sharaɗi ba.
Haka kuma, ƙungiyar ta buƙaci a samar da jadawalin biyan dukkan bashin da ake bin malaman, wanda za a rubuta kuma a cimma matsaya a kai tsakanin ɓangarorin.
ASUU ta kuma buƙaci a shigar da dukkan malaman jami’ar, ciki har da malaman visiting da na sabbatical, cikin sabon tsarin albashi da alawus-alawus da aka tanada a ƙarƙashin yarjejeniyar ASUU da gwamnatin tarayya ta shekarar 2025.
A cewar shugaban ƙungiyar, ASUU ta rubuta wa mai ziyartar jami’ar kuma gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Raɗɗa, da majalisar gudanarwar jami’ar UMYU, da kuma mataimakin shugaban jami’ar, tana neman a gaggauta shawo kan matsalar.
Dangane da matakin da za ta ɗauka na gaba, ASUU-UMYU ta ce za ta sake kiran taron majalisar mambobinta domin duba halin da ake ciki da kuma yanke shawarar matakan da suka dace domin ganin an biya mata buƙatunta.
Ƙungiyar ta yi gargaɗin cewa za ta iya ayyana rikicin ƙwadago bisa tanadin dokokin ƙwadago da ake da su, idan har ba ta samu ingantacciyar amsa mai gamsarwa cikin wani lokaci mai ma’ana ba.
