Daga AISHA ASAS
A da, idan mutum ya ga wani kyakkyawan labari ko doguwar maƙala, tambayar farko da za ta zo masa ita ce: wane marubuci ne ya rubuta wannan? Yanzu kuwa akwai wata tambaya da ta fara shiga tsakanin marubuta, mawallafa da masu karatu: shin mutum ne ya rubuta, ko kuma wata na’ura ce ta taimaka masa? Wannan tambayar da a shekarun baya ta kasance kamar labarin makomar da ba ta zo ba, yanzu ta zama wani ɓangare na rayuwar rubutu. Basirar na’ura, wato Artificial Intelligence (AI), ta shiga cikin duniyar rubutu da ƙarfinta , tana taimaka wa wasu wajen tsara tunani, gyara rubutu, fassara da neman bayanai, yayin da wasu kuma suka fara amfani da ita wajen samar da labari tun daga farko har ƙarshe.
A nan ne duniyar adabi ta fara fuskantar wata hanya mai fuska biyu. Dalilin kiranta mai fuska biyu kuwa shi ne, wasu na ganin ta matsala, yayin da wasu ke ganinta mafita. Ga wata mahanga ba za mu iya kawar da kai kan yadda rubutu ya fara tashi daga kalmar ‘abu na musamman’ duk da cewa marubuci ba kalmomi kaɗai yake bayanawa ba ko nuna gwaninta kan jan zaren rubutu ba. Yana bayyana tunaninsa, kallonsa ga duniya, abubuwan da ya gani, abubuwan da ya sha wahala a kansu, da kuma irin muryar da ta bambanta shi da wani marubuci ta ɓangaren taushi ko zafin zuciya, ƙunci ko soyayya da kuma ra’ayoyi kan ɓangarorin rayuwa.
Don haka tambayar da ta fi muhimmanci ga masu muhawara kan wannan darasin namu ita ce, idan wata na’ura za ta iya haɗa kalmomi masu kyau cikin ‘yan daƙiƙu, shin wannan ya isa a ce ta zama marubuciya? Ko kuwa rubutu yana da wani abu da ya wuce daɗaɗan kalmomi?
A shekarar 2026, wannan muhawara ta ƙara ɗaukar zafi saboda abin da ke faruwa a duniyar marubuta. A Birtaniya, marubucin wasan kwaikwayo Jack Thorne, wanda ya jagoranci Writers’ Guild of Great Britain, ya yi gargadin cewa wasu marubuta suna amfani da AI wajen samar da cikakkun rubuce-rubuce maimakon su yi aikin ƙirƙira da kansu. Ya kuma yi kira da a samu dokar da za ta hana amfani da abin da AI ta samar ba tare da bayyana hakan ba a aikin ƙwararru, yana mai cewa hakan na iya zama yaudara ga masu karatu da kuma cutar da sana’ar marubuta.
Amma ba batun amfani da AI wajen rubutu kaɗai ne ke tayar da hankali ba. Wata babbar tambaya ita ce: daga ina AI take samun abubuwan da take koya da su? Domin waɗannan na’urori ba sa tasowa da kansu suna ƙirƙirar labaran daga babu. Ana horar da manyan tsarin AI da tarin bayanai da rubuce-rubuce, kuma a nan ne marubuta suka fara tambayar ko ya dace a yi amfani da ayyukansu wajen horar da na’ura ba tare da izininsu ko wata yarjejeniya ba.
Wannan batu ya kai kotuna. A Amurka, wasu marubuta ciki har da John Grisham da George R.R. Martin suna cikin masu ƙalubalantar OpenAI da Microsoft kan amfani da ayyukan marubuta wajen horar da tsarin AI. A yanzu haka kotu tana fuskantar babbar tambaya ta ko amfani da littattafan da aka kare da haƙƙin mallaka wajen horar da AI yana ƙarƙashin dokar fair use, ko kuwa keta haƙƙin marubuta ne? Sakamakon wannan shari’a na iya yin tasiri ga yadda za a tsara dangantakar AI da rubuce-rubuce a nan gaba.
Ba wannan kaɗai ba ne. A watan Yulin 2026, wata kotun Amurka ta amince da yarjejeniyar dala biliyan 1.5 a wata shari’ar da marubuta suka shigar kan Anthropic saboda amfani da ayyukansu wajen horar da AI. Wannan lamari ya nuna cewa batun bai tsaya a iya muhawarar masana fasaha kawai ba, ya riga ya zama batun kwace dama, haƙƙin mallaka da makomar sana’ar rubutu.
Sai dai akwai wani abu da ya kamata a bambanta, amfani da AI wajen taimakawa marubuci ba daidai yake da bai wa AI aikin rubuta komai ba. Marubuci zai iya amfani da ita wajen neman ra’ayoyi, gyara kuskuren rubutu, tsara bayanai ko taimakawa a wani mataki na aikin. Hukumar Haƙƙin Mallaka ta Amurka ta ce amfani da AI a matsayin kayan taimako ba ya hana a kare aikin da mutum ya samar da kansa; abin da dokar ke dubawa shi ne irin rawar da ƙirƙirar ɗan adam ta taka wajen samar da aikin. Kuma bayar da umarni ga AI kawai, ba tare da wani babban abin ƙirƙira daga mutum ba, ba shi ne ke ba da haƙƙin mallaka kai tsaye ba.
Wannan batu ya fi muhimmanci ga marubutan Afirka saboda yawancin ƙasashen nahiyar har yanzu suna ƙoƙarin daidaita tsoffin dokokin haƙƙin mallaka da sabuwar duniyar AI. Wani bincike da aka wallafa a shekarar 2026 kan dokokin Afirka ya nuna cewa ƙasashe suna da hanyoyi daban-daban wajen kallon wanda zai zama ma’abucin aikin da AI ta taimaka wajen samarwa, kuma akwai buƙatar a ƙara fayyace dokokin domin kare masu ƙirƙira yayin da tattalin arzikin fasahar zamani ke girma.
A Najeriya ma, batun ba zai iya zama na ƙasashen waje kawai ba. Hukumar Haƙƙin Mallaka ta Najeriya ta bayyana kanta a matsayin hukumar da ke kula da kare haƙƙin marubuta, masu fasaha, mawaƙa da sauran masu ƙirƙira. Amma zuwan AI yana kawo tambayoyin da dokokin da aka tsara kafin wannan zamani ba su yi tunani a kansu sosai ba. Idan AI ta taimaka wajen rubuta littafi, wane ne mamallakin haƙƙinsa? Idan aka yi amfani da wani marubuci wajen horar da na’ura ba tare da izininsa ba fa? Kuma idan wani ya yi amfani da AI wajen kwaikwayon muryar wani marubuci fa?
Ga marubucin Hausa ma, wannan ba batu ne da ya kamata a ce ya shafi Turawa da Amurkawa kaɗai ba. Yayin da rubuce-rubucen Hausa ke ƙara shiga kafafen zamani, ana samun ƙarin damar amfani da AI wajen rubutu, fassara, gyara da yaɗa littattafai. Amma a lokaci guda akwai buƙatar marubuci ya tambayi kansa abin da yake son ya kare: kalmar Hausa ce kawai, ko kuma muryar da yake amfani da Hausa wajen bayyana abin da yake cikin zuciyarsa?
Domin AI na iya sanin yadda ake haɗa jimla, amma wannan ba yana nufin ta rayu irin rayuwar marubucin ba. Ba ta tashi a unguwar da marubucin ya taso ba, ba ta zauna da mutanen da suka gina tunaninsa ba, ba ta yi fama da talauci ko soyayya ko rabuwa ko rashin adalci da ya sa wani labari ya taso a cikin zuciyarsa ba. Za ta iya samar da labarin mutum mai fama da yunwa, amma ba ta jin yunwar. Za ta iya rubuta labarin uwa da ta rasa ɗanta, amma ba ta san yadda shiru yake a gidan da irin wannan rashi ya bari ba.
Wannan ne ya sa wasu ke ganin cewa babbar darajar marubuci a zamanin AI ba za ta kasance kawai iya rubuta kalmomi cikin tsari ba. Darajar za ta koma ga abin da mutum yake da shi da ba a iya kwafan shi cikin sauƙi, wato kamar hangen duniya, kwarewar rayuwa, murya, tunani da ikon tambayar abin da wasu suka daina tambaya.
Amma kuma bai kamata a mayar da AI gaba ɗaya a matsayin maƙiyin marubuci ba. Kamar yadda kwamfuta ta sauya yadda ake rubutu, kamar yadda intanet ta sauya yadda ake bincike, AI ma na iya zama wani sabon kayan aiki. Matsalar tana farawa ne a lokacin da kayan aikin ya koma wanda yake yin aikin gaba ɗaya, ko kuma aka ɓoye yadda aka yi aikin daga mai karatu.
Saboda haka, tambayar da ke gaban duniyar adabi ba wai “AI za ta kashe marubuci?” kawai ba ce. Tambayar da ta fi dacewa ita ce, idan AI za ta iya rubuta abu mai kama da na mutum, me za mu fara nema a cikin rubutun ɗan adam? Wataƙila amsar za ta kasance a cikin abin da ba a iya samu ta hanyar koyo, kamar raɗaɗi ko farin cikin da mutum ya ji, rauninsa, abin da ya yi imani da shi, abin da ya gani, da kuma dalilin da ya sa ya ji cewa dole ne ya rubuta wannan labarin.
Domin a ƙarshe, kalmomi na iya zama abu da na’ura za ta iya samarwa. Amma dalilin da ya sa mutum ya zaɓi waɗannan kalmomin domin ya ba duniya wani labari, shi ne abin da har yanzu ke tabbatar da marubuci ya fi AI a fagen rubutu.
2.
Salman Rushdie: Marubucin da rubutu ya yi sanadin rasa idonsa, ya samu babbar karramawa
Daga AISHA ASAS
Akwai marubutan da rubutunsu ya ba su suna, akwai waɗanda ya kai su ga manyan lambobin yabo, sannan akwai waɗanda rubutunsu ya zama wani ɓangare na tarihin rayuwarsu ta yadda ba za a iya raba mutumin da abin da ya rubuta ba. Salman Rushdie na cikin irin waɗannan marubuta. Shekaru da dama ya shafe yana rubutun da yake zama fuskar muhawara da ce-ce-ku-ce, yana kuma fuskantar barazana saboda wasu daga cikin ayyukansa. Amma abin da ya faru da shi a shekarar 2022 ya sauya rayuwarsa ta wata hanya da ba zai taɓa mantawa da ita ba, wato an kai masa hari da wuƙa a gaban jama’a, har ya samu munanan raunuka da suka bar shi da nakasa. Duk da haka, bai ajiye alkalami ba.
Yƙdda abin ya faruwa kuwa shi ne, a ranar 12 ga Agusta, 2022, Rushdie na shirin gabatar da jawabi a Chautauƙua Institution da ke New York, Amurka, inda zai yi magana kan muhimmancin kare marubuta da masu fasaha daga barazana da cutarwa. Sai dai kafin ya fara jawabin, wani mutum ya yi dirar mikiya kan dandamalin, cikin azama ya kai masa hari da wuƙa. Abin da ya kamata ya zama taron tattaunawa kan adabi ya rikiɗe cikin ‘yan daƙiƙu zuwa wani yanayi na neman ceton rai. Rushdie ya samu munanan raunuka don haka cikin gaggawa aka garzaya da shi asibiti.
Harin bai tsaya a kan raunukan da aka gani a ranar ba. Ya bar Rushdie da sakamakon da zai ci gaba da kasancewa tare da shi. Domin daga baya aka bayyana cewa ya rasa ganin ido ɗaya, sannan ya samu matsala wajen amfani da hannunsa na dama. Ga marubuci wanda aikinsa ya dogara da karatu, tunani da rubutu, irin wannan rauni ba ƙaramin sauyi ba ne. Amma maimakon ya ɗauki abin da ya faru a matsayin ƙarshen aikinsa, Rushdie ya koma inda ya saba komawa idan rayuwa ta yi masa zafi, wato fagen rubutu.
Daga cikin abin da ya rubuta bayan harin akwai littafinsa Knife: Meditations After an Attempted Murder, wanda ya mayar da abin da ya faru da shi zuwa labari mai ratsa zuciya. A cikin littafin, ya yi magana kan harin, raunukan da ya samu, doguwar hanyar murmurewa da kuma mutanen da suka kasance tare da shi a lokacin. Ya kuma yi rubutu kan soyayya da goyon bayan da ya samu daga matarsa Eliza, iyalinsa, likitoci da masu kula da shi yayin da yake ƙoƙarin dawo da wani ɓangare na rayuwarsa bayan harin. Littafin ya kuma kasance ɗan takarar National Book Award na 2024 a fannin rubuce-rubucen da ba almara ba.
Amma idan aka koma baya, za a ga cewa harin na 2022 ba shi ne karo na farko da rubutun Rushdie ya jefa shi cikin hatsari ba. Sunansa ya yi fice sosai bayan wallafa Midnight’s Children, littafin da ya lashe babbar lambar yabo ta Booker Prize, sannan daga baya aka zaɓe shi a matsayin Best of the Booker. Sai kuma The Satanic ɓerses, littafin da ya haifar da babbar muhawara a duniya kuma ya jawo masa barazana mai tsanani bayan Ayatollah Ruhollah Khomeini na Iran ya bayar da fatawar kisa a kansa a shekarar 1989.
Duka wannan na nuni da cewa dangantakar Rushdie da rubutu ba ta taɓa zama mai sauƙi ba. Rubutunsa ya kawo masa shahara da yabo, amma a wasu lokuta ya kuma zo da barazana da tsoro. Duk da haka, bai ɗauki shiru a matsayin hanyar tsira ba. Ya ci gaba da rubuta littattafai, makaloli da sauran ayyuka da suke bayyana shi a matsayin marubuci, yana amfani da alƙalami wajen kallon tarihi, siyasa, al’adu da rayuwar ɗan adam.
Abin da ya fi ɗaukar hankali shi ne yadda ya sake komawa ga almara bayan harin. A shekarar 2026, an sanar da dawowarsa da wani sabon aikin almara mai suna The Eleɓenth Hour, tarin gajerun labarai da suka taɓo batutuwan shekaru, mutuwa, kadaici, tarihi da rayuwar ɗan adam. Wannan ma ya zama wata alama ta cewa duk da abin da ya faru da jikinsa, har yanzu duniyar da yake ginawa da kalmomi ba ta rufe masa ƙofa ba.
Sai kuma ga wani sabon babi da ya zo a wannan watan. A ranar 10 ga Satumba, 2026, National Book Foundation ta sanar da cewa za ta bai wa Salman Rushdie lambar yabo ta 2026 Medal for Distinguished Contribution to American Letters, wato babbar lambar karramawa da ake bai wa marubuci saboda gagarumar gudunmawar da ya bayar ga adabin Amurka. Za a miƙa masa lambar yabon a bikin National Book Awards na 77 da za a gudanar a New York ranar 18 ga Nuwamba, 2026, kuma marubuciya Kiran Desai ce za ta miƙa masa lambar.
Wannan karramawa tana zuwa ne bayan kusan shekaru 50 na rubuce-rubucen Rushdie, shekarun da suka haɗa da shahara, yabo, ce-ce-ku-ce, barazana, hari da kuma doguwar hanyar murmurewa. Ya rubuta litattafai 15 na almara da sauran ayyukan rubuce-rubuce, kuma aikinsa ya samu karɓuwa a sassa daban-daban na duniya. National Book Foundation ta bayyana karramawar a matsayin girmamawa ga gudunmawar da ya bayar ga adabi tsawon shekaru da kuma tasirin aikinsa ga masu karatu da marubuta.
