Nasarawa @30: Jega da Kukah sun ce rashin shugabanci nagari ya jefa Nijeriya matsala

Spread the love

Daga JOHN D. WADA a Lafiya

Tsohon shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa INEC, Farfesa Attahiru Jega da Bishop na Katolikan Sokoto Bishop Rev. Matthew Hassan Kukah sunce rashin shugabanci nagari na dogon lokaci da gurɓacewar tarbiyya ne ke cigaba da kawo cikas ga cigaban Najeriya.

Sun bayyana hakan ne a birnin Lafiya jihar Nasarawa ranar a wajen lacca ta cika shekaru 30 da ƙirƙirar jihar wato a ranar 1 ga Oktoban 1996.

Farfesa Jega wanda ya gabatar da babbar lacca mai taken “Jihar Nasarawa a Shekaru 30: Daga tushe zuwa sauyi,” ya ce Najeriya ta sha fama da “mummunan rashin sa’a na fama da mummunan shugabanci” a matakai biyu – daga mulkin soja marar dimokuraɗiyya da rashin tuntuɓar jama’a, da mulkin farar hula tun 1999 wanda ya tada manyan fata amma ya bar ‘yan ƙasa da dama musamman matasa cikin takaici sakamakon talauci da rashin aikin yi da shakku kan sahihancin zaɓe da sauran su.

Bishop Kukah kuma wanda ya yi magana kan taken “Haɗin kai a cikin banbance-banbance: Shekaru Talatin na gina jihar Nasarawa mai hadin kai,” yace gazawar Najeriya mafi girma itace rashin iya sarrafa bambance-bambancen al’adu da addinai yana mai cewa bayan shekaru 66 da samun ‘yancin kai ƙasar ba ta manta da bambance-bambancen na ta ba kamar yadda Dr. Nnamdi Azikiwe ya ba da shawara kuma ba ta fahimci bambance-bambancen ba kamar yadda Sir Ahmadu Bello ya faɗa.

Da yake amfani da Nasarawa a matsayin misali Jega ya tuna cewa jihar na ɗaya daga cikin jihohi shida da marigayi Shugaban ƙasa Janar Sani Abacha ya ƙirƙira. Da yake nakalto tsohon Gwamna Abdullahi Adamu, yace Nasarawa a lokacin ƙirƙirar ta tana da “titin kwalta guda ɗaya, babu hukumar samar da ruwa, babu sakatariya,” da yawan jama’a miliyan 1.5 da gudummawar kuɗin shiga na cikin gida, IGR, na kashi 3.7 a 1997.

Shekaru talatin bayan haka Jega yace jihar na da mutane kimanin miliyan 3.3, IGR ya ƙaru zuwa kashi 11 cikin 100 da makarantun firamare na gwamnati sun ƙaru daga 1,402 zuwa sama da 2,100 da sakandare daga kusan 150 zuwa 490 da manyan makarantu daga 2 da ɗalibai 2,500 zuwa 18 da dalibai sama da 60,000 da cibiyoyin kiwon lafiya daga 150 zuwa 895 da titin kwalta daga 200-300km zuwa 1,500km, wanda aka gina 639km a cikin shekaru bakwai da suka gabata.

Ya kawo rahotannin bankin duniya, NBS da UNDP, yace talauci ya ragu daga kashi 70 a 1996 zuwa kashi 62 a 2026, yayin da bayanan NBS na 2022 ya sanya Nasarawa a kashi 57 cikin ɗari, duk da cewa talauci mai fuskoki da yawa ya kasance a kashi 79.8 cikin ɗari. Ruwan famfo ya ƙaru daga kashi 5-8 zuwa kashi 29 a birane, yayin da yawan ‘yan mata masu shiga makaranta ya ƙaru daga 68,000 zuwa 333,000.

Jega ya kuma bayyana gwamnatin gwamna Abdullahi Sule na shekaru bakwai a matsayin “babban haske na bege,” yana mai nuni da jarin da aka zuba a sabunta birane, lafiya, noma, ilimi, masana’antu da haƙar ma’adanai, yana mai cewa idan aka ci gaba da haka, Nasarawa na iya zama “jihar da za a yi koyi da ita.”

Bishop Kukah kuma yace Nasarawa mai ƙabilu sama da 30 da suka haɗa da Eggon da Alago da Mada da Bassa da Tiv da Fulani da Jukun da Hausa da Idoma da sauran su a ƙananan hukumomi 13 tamkar ƙaramar Najeriya ce. Yace babi na biyu na kundin tsarin mulkin 1999 ya sanya walwalar ‘yan ƙasa a matsayin babbar manufar gwamnati, kuma sashe na 14 kan halayen tarayya na nufin samar da jin daɗin zama ɗan ƙasa.

Ya lissafa arzikin jihar kamar su fadamar ruwa ta Farin Ruwa a Wamba da aka shirya tashar wutar lantarki ta 20MW, Tafkin Hunki Oxbow a Awe, Tafkin Peperuwa a Doma, ƙananan tafkuna sama da 60, ma’adanai masu yawa da jarin masana’antu kamar Dangote – amma ya yi gargaɗin cewa ci gaba ba shi da ma’ana idan bai sauya rayuwar mutane ba.

“Yara a Wamba, Doma da Awe sun fahimci zama ɗan ƙasa ta hanyar tallafin karatu, hanyoyi da makarantu masu aiki, ba ta hanyar jawabi ba,” in ji Kukah.

Ya tuna da cewa a lokacinsa na mataimakin shugaban jami’a, ya ba da shawarar kowace ƙaramar hukuma ta bayar da kashi 1-2 na kasafinta ga jami’ar jihar domin ɗalibai daga ƙananan hukumomi 13 su iya karanta likitanci, injiniya da gine-gine.

Kukah yace zanga-zangar neman sabbin jihohi na samo asali ne daga rashin jin daɗin zama ɗan ƙasa kuma ya yi gargaɗi kan fifita wani addini fiye da wani.

“A ƙarshe, ‘yan Najeriya sun yarda cewa ƙasar na da cin hanci da rashawa ne kawai; ba sa neman kawo ƙarshen cin hanci da rashawa, kawai suna son nasu mutumin ya shiga cikin cin hancin. Ba za mu iya gina ƙasa a kan irin wannan gurɓacewar tarbiyya ba,” in ji shi.

Ya kuma yaba wa marigayi Janar Sani Abacha, wanda ya ƙirƙiro Nasarawa a 1996, yana mai bayyana shi a matsayin “Shugaban Ƙasa mafi zargi a Najeriya, amma mutumin da ya yi abubuwa masu yawa.”

Dukkan waɗanda suka yi jawabi a wajen laccar sun ce dole Najeriya ta sauya daga kasafin kuɗi na shekara-shekara zuwa shugabanci mai hangen nesa da sauyi da aka gina kan adalci da haɗin kai.

A nasa jawabin gwamna Abdullahi Sule ya yi kira ga jihohin Arewa ta Tsakiya da su tashi su nemi ‘yancin kai na tattalin arziki da tsaro, yana mai cewa lokacin jiran rabon tarayya ya kamata ya ƙare.

Sule ya ce Najeriya na komawa zuwa ga ƙarin cin gashin kai na yankuna a fannin tattalin arziki, gudanarwa da tsaro, musamman tare da turawar samar da ‘yan sandan jihohi, wanda ke nuni da raba madafun iko ga jihohi.

Yace batun ya tashi daga tsohon Gwamna Turaki Keffi kuma ya zama mai gaggawa bayan an ambaci Arewa ta Tsakiya a taron Majalisar Ɗinkin Duniya, UNGA, a New York kwanan nan kan ma’adanai masu ƙarfi. A cewarsa, yankin na da mabuɗin makomar masana’antun Najeriya – Benue da Kogi sun yi suna wajen samar da siminti, Nasarawa a lithium, yayin da Plateau ta shahara da tin tun da daɗewa.

“Wannan babbar dama ce da dole mu haɗa kai don samun ‘yancin kan da muke buƙata. Lokacin da jihohi ke cewa muna jiran rabon tarayya ya kamata ya kare. Muna da karfin, muna da shugabanci, muna da kwarewa, kawai muna bukatar hangen nesa da jajircewa,” in ji Sule.

Ya ce kirkirar Nasarawa a ranar 1 ga Oktoba, 1996 wani lokaci ne mai ma’ana wanda ya cika dogon burin shiga siyasa da ci gaba kusa da jama’a, yana mai cewa bayan shekaru 30, bambance-bambance ya kasance ƙarfin jihar.

Sule ya yi alƙawarin cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da aiki har sai an kawo ƙarshen garkuwa da mutane a Nasarawa, yana mai lura da cewa darussan da aka koya daga laccocin za su shiryar da jihar wajen gina Arewa ta Tsakiya mai haɗin kai da dogaro da kanta.

By ukarofi

Leave a Reply