Gwamnatin Tarayya ta ayyana Alhamis a matsayin hutun zagayowar Ranar ‘Yancin Kai

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Alhamis, 1 ga watan Oktoba, 2026 a matsayin ranar hutu domin karrama cikar Nijeriya shekeru 66 da samun ‘yancin kai.

Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da Babbar Sakatariyar Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida, Dakta Magdalene Ajani ta fitar a ranar Laraba, 30 ga Satumba. A cewar sanarwar, Ministan Cikin Gida, Tunji-Ojo, wanda ya ayyana haka a madadin gwamnatin tarayyar, ya taya ‘yan Nijeriya da ke gida da waje murnar Ranar ‘Yancin Kai ta cikar Nijeriya shekeru 66 da samu daga hannun Turawa.

Ministan ya kirayi ‘yan ƙasa da su yi amfani da lokacin wajen nuna haɗin kai, kishin ƙasa, son zaman lafiya da girmama juna a tsakaninsu ta yadda hakan zai taimaka wa ƙoƙarin sauke nauyin da ke kansu na samar wa Nijeriya ci-gaba mai ɗorewa.

Ya bayyana cewa, zaman lafiya da ɗorewar al’amura suna da muhimmanci wajen ciyar da kowace ƙasa gaba, don haka yake kiran ‘yan Nijeriya da su yi koyi da magabatan ƙasar wajen nuna tsantsar soyayya a gare ta. Haka kuma, ya buƙace su da su yi aiki wajen samar da Nijeriyar da a nan gaba al’umma mai zuwa za ta yi alfahari da ita, yana mai fatan yiwuwar cimma hakan.

Kazalika, ya ce bambance-bambancen al’ummar Nijeriya dama ce ta ƙarfafawa, inda ya nemi ‘yan ƙasa da su cigaba da ƙoƙarin wanzar da haɗin kan ƙasa a madadin rarrabuwa a tsakaninsu. Har ila yau, ya jaddada cewa Gwamnatin Tarayya ta Ajandar Sabunta Fata, tana aiki tuƙuru wajen tabbatar da inganta Nijeriya domin amfanin dukkan ‘yan ƙasa a matsayin nuna godiya ga hidimar magabatan ƙasar.

A ranar 1 ga Oktoban 1960 ne Nijeriya ta samun ‘yancin kai daga hannun Turawan mulkin mallaka kuma ƙasar za ta cika shekara 66 da samu a ranar Alhamis.

By Babaji

Leave a Reply