
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A ranar Laraba Mai Martaba Sarkin Masarautar Zazzau, Ambasada Ahmed Nuhu Bamlli ya kai ziyarar ban-girma ga Shugaban Hukumar Jigilar Alhazan Nijeriya (NAHCON), Ambasada Isma’il Abba Yusuf a hedikwatar hukumar da ke Abuja.
A yayin haka ne Sarkin ya tabbatar wa NAHCON samun goyon bayan masarautarsu yayin da kuma ya yi kira da a cigaba da ƙoƙarin inganta harkokin hukumar wajen gudanar da jigilar alhazan Nijeriya.
A wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’ar NAHCON, Shafi’i Sani Mohammed ya fitar a ranar Laraba, 30 ga Satumba, basaraken ya yaba wa shugabancin NAHCON bisa ƙoƙarinta samar da gyare-gyare a harkokin aikin hajji, yana mai cewa gudanar da dubunnan alhazai nauyi ne da ke buƙatar sadaukarwa, dabaru da tsare gaskiya da adalci.
A cewarsa, Masarautar Zazzau da sauran cibiyoyin gargajiya muhimman jigo ne wajen wayar da kan maniyyata da tabbatar da samun nasara a harkokin hajji, yana mai kira ga NAHCON da ta cigaba da ƙoƙarin inganta harkokinta ta yadda za a shawo kan dukkan matsalolin da ake fuskanta.
A nasa jawabin, Shugaban NAHCON ya bayyana godiyarsa ga Sarkin bisa wannan ziyarar mai tarihi, yana mai bayyana ta a matsayin abin da za ta ƙarfafa wa hukumar gudanarwa da jami’an NAHCON gwiwa wajen sauke nauye-nauyen da aka ɗora musu bisa inganci.
Ya kuma tabbatar wa sarkin cewa za su yi nazari akan muhimman batutuwan da aka tattauna yayin ganawar tasu ta yadda za a gudanar ingantaccen aikin hajjin da gwamnati da al’umma za su gamsu da shi a nan gaba.
