Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Jam’iyyar NDC a Jihar Zamfara ta yi watsi da hukuncin kotun Lokoja, ta bayyana cewa jam’iyyar ta ci gaba da kasancewa a matsayin wadda aka amince da ita bisa doka duk da hukuncin da babbar kotun tarayya ta yanke kwanan nan a Lokoja.
A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi, shugaban jam’iyyar na jihar, Alhaji Surajo Garba Maikatako, ya ce hukuncin wani cikas ne na doka na ɗan lokaci, ba zai hana jam’iyyar shiga zaɓen 2027 ba.
Mai katako ya bayyana hukuncin Lokoja, wanda Peace Movement ta samu, a matsayin ba ƙarar da aka shigar a kan hukuncin da ya tilasta wa INEC yin rijistar NDC ko kuma ƙarar da ke ƙalubalantar wanzuwar jam’iyyar.
Ya ce jam’iyyar ba ta yarda da hukuncin ba, duk da cewa tana da matuƙar girmama doka.
Shugaban jam’iyyar ya bayyana cewa ƙungiyar lauyoyi ta ƙasa, tana aiki bisa umarnin shugaban jam’iyyar na ƙasa, Sanata Henry Seriake Dickson, da sakataren ta na ƙasa, Sanata Cleopas Moses Zuwoghe, yayin da tuni suka shigar da ƙara a kotun ɗaukaka ƙara.
Ya bayyana ƙwarin gwiwar cewa kotun ɗaukaka ƙara za ta dawo da cikakken matsayin jam’iyyar a ƙarƙashin doka.
Maikatako ya tabbatar wa ‘yan Jam’iyyar cewa NDC tana bin dukkan ƙa’idojin kundin tsarin mulki da na shari’a sosai, ta gudanar da zaɓukanta da na fidda gwani, kuma ‘yan takarar dukkan muƙamai suna nan daram.
Ya ce shirye-shiryen babban zaɓen 2027 suna kan gaba.
Sanarwar ta kuma yaba wa ɗan takarar gwamnan jihar Zamfara na jam’iyyar, Sanata Kabir Garba Marafa, yana mai bayyana shi a matsayin alama ce ta sabuwar jihar Zamfara da suke fatan samu wacce ke fama da matsalar ‘yan ta’adda, talauci, da rashin shugabanci nagari.
Maikatako ya buƙaci magoya bayansa da su kwantar da hankalinsu, su kasance cikin haɗin kai, kuma su jajirce.
Ya yi zargin cewa akwai wani yanayi mai hatsari inda ake amfani da ɓangaren shari’a don murƙushe wasu jam’iyyun siyasa.
“NDC tana nan daram don ci gaba da zama, kuma za tayi nasara da Ikon Allah”. Cewar Maikatako
