
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
An kammala wasannin rukunin K da L a gasar Kofin Duniya na 2026 da ke gudana a Amurka cikin wani salo mai kama da wasan kwaikwayo a ƙoƙarin zuwa zagayen ‘yan 32.
A sakamakon haka ne Portugal za ta kara da Croatia a Toronto a ranar 2 ga Yuli, a wata karanbatta da ka iya zama wasa na ƙarshe a gasar ga Cristiano Ronaldo mai shekaru 41 ko kuma Luka Modric.
Portugal ta koma matsayi na biyu ne bayan da ta tashi wasa babu ci tsakaninta da Kolombiya a rukunin K, yayin da Croatia ta ƙare a matsayi na biyu bayan doke Ghana da ci 2 da 1 a rukunin L.
Ita kuwa Ingila, ta ƙare ne a matsayi na ɗaya a rukunin na L bayan doke Panama da ci 2 da nema, inda Harry Kane da Jude Bellingham suka zura ƙwallayen.
A birnin Atlanta kuwa, Kongo ta kafa tarihin lashe wasa na farko a gasar bayan doke Uzbekistan da ci 3 da 1, sakamakon da ya ba su damar shiga sahun mafi kyawun ƙasashen da suka ƙare a matsayi na uku.
A ranar 4 ga Yuli ne Kolombiya da ta lashe rukunin K, za ta kara da Ghana a birnin Kansas.
A wani ɓangare kuwa, zakaran ɗan ƙwallon duniya, Lionel Messi ya sake kafa tarihi bayan Argentina ta doke Jordan da ci 3 da 1 a filin Dallas.
Messi mai shekaru 39 ya shiga wasan ne bayan minti 60 da farawa inda ya zura ƙwallo guda ta bugun tazara a minti na 80, lamarin da ya kai adadin ƙwallayensa a gasar zuwa guda shida.
Sannan hakan ya sa ya zama ɗan wasa na farko a tarihi da ya zura ƙwallo a wasannin Kofin Duniya guda bakwai a jere tun daga rukunin ƙalubale na gasar a 2022.

