Mashigar Hormuz: Amurka ta yi ruwan wuta a Iran

Spread the love

Shugaba Donald Trump na Amurka ya zargi Iran da karya yarjejeniyar tsagaita wuta bayan wani jirgin sama mara matuki ya kai hari kan wani babban jirgin ɗaukar kaya a Mashigin ruwan Hormuz.

Harin ya faru ne kusa da gabar tekun Oman, inda aka kai wa jirgin ruwan Ever Lovely mai tutar Singapore hari. Jirgin mallakar kamfanin jigilar kaya na Taiwan, Evergreen Marine, ne.

Babu wani ma’aikacin jirgin da ya ji rauni, kuma jirgin ya samu damar ci gaba da tafiyarsa. Rundunar sojin Amurka ta ce ta dakile wasu jirage marasa matuka da ake zargin suna cikin harin.

Trump ya bayyana harin a matsayin “wawanci” kuma ya yi gargadin cewa ba za a amince da sake karya yarjejeniyar tsagaita bude wuta ba.

Iran ta musanta cewa tana da hannu a harin, duk da cewa wasu jami’an Amurka sun ce suna zargin Tehran da alhakin kai harin.

Wannan lamari ya faru ne a daidai lokacin da Amurka da Iran ke ci gaba da tattaunawa kan yarjejeniya ta wucin gadi domin rage tashin hankali da bude Mashigin ruwa Hormuz, da magance takaddama kan shirin nukiliyar Iran da takunkumi.

Harin ya kuma kawo tsaiko ga kokarin taimaka wa jiragen ruwa da suka makale a yankin Tekun Fasha, lamarin da ya ƙara damuwa kan tsaron wannan muhimmiyar hanyar safarar man fetur a duniya.

By Babaji

Leave a Reply