A wani mataki da ake kallon zai taimaka wajen ƙarfafa haɗin kai da zaman lafiya a nahiyar Afirka, Cibiyar Kasa da Kasa ta Ilimin Kafofin Watsa Labarai da Ilimin Bayani (IMILI), wadda ke daga cikin cibiyoyin da ke aiki ƙarƙashin inuwar UNESCO a matsayin cibiyar Category 2 ta farko a wannan fanni, ta sanar da ƙaddamar da ɗaya daga cikin manyan shirye-shiryenta na nahiyar baki ɗaya mai suna Africa Against ɗenophobia Project (AfAɗ-P), wato Shirin Yaƙi da ƙyamar Baƙi a Afirka.
An gudanar da ƙaddamarwar ne ta kafar intanet a ranar Alhamis, 18 ga watan Yuni, 2026, daidai lokacin da duniya ke bikin Ranar Yaƙi da Kalaman ƙiyayya ta Duniya, lamarin da ya nuna muhimmancin aikin da shirin ke da shi wajen ƙarfafa haɗin kai da kuma daƙile yaɗuwar saƙonnin da ke haddasa rarrabuwar kawuna a tsakanin al’ummomin Afirka.
ƙaddamar da wannan shiri na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da nuna damuwa kan hare-haren ƙyamar baƙi da ake kai wa ‘yan ƙasashen Afirka daban-daban da ke zaune a ƙasar Afirka ta Kudu. A cikin ‘yan shekarun nan, irin waɗannan hare-hare sun janyo ce-ce-ku-ce a duniya, tare da kiraye-kirayen da aka yi wa gwamnatin shugaban ƙasar Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa, da ta ɗauki tsauraran matakai domin kawo ƙarshen irin waɗannan ayyuka da ake zargin wasu bata-gari ke aikatawa.
A cikin wata sanarwa da Cibiyar Bayar da Bayanai ta Majalisar ɗinkin Duniya (UNIC) ta fitar a ranar Juma’a, an bayyana cewa an tsara shirin AfAɗ-P ne domin ɗaukar matakan kariya da kuma rage yaɗuwar ƙyamar baƙi da kalaman ƙiyayya da kuma yaɗa bayanan ƙarya, waɗanda ke barazana ga haɗin kan al’umma, bunƙasar haɗin gwiwar yankuna da kuma daidaiton tattalin arzikin nahiyar Afirka.
Taron ƙaddamarwar ya haɗa manyan masana da wakilai daga ƙasashen Afirka daban-daban da kuma Birtaniya, inda suka gudanar da tattaunawa mai zurfi kan hanyoyin magance waɗannan matsaloli da ke ƙara ta’azzara a nahiyar.
Wadanda suka halarci taron sun fito daga ƙasashen Uganda, Namibia, Mozambiƙue, Afirka ta Kudu, Najeriya, Birtaniya, Morocco da Saliyo. Tattaunawar ta mayar da hankali kan muhimman batutuwa da suka haɗa da rawar da yaɗa bayanan ƙarya, karkatattun bayanai da kalaman ƙiyayya ke takawa wajen ƙarfafa ƙyamar baƙi a nahiyar, da kuma muhimmancin ɗaukar matakan gaggawa domin tabbatar da zaman lafiya da ci gaba mai ɗorewa a Afirka.
Har ila yau, mahalarta taron sun tattauna hanyoyin da za a bi wajen tinkarar waɗannan ƙalubale tare da gabatar da sabbin dabaru da mafita masu ɗorewa da za su taimaka wajen kawar da matsalar daga tushe.
A saƙon da ya gabatar, Jami’in Majalisar ɗinkin Duniya mai kula da ayyukan jin ƙai da kuma wakilin MDD a Najeriya, Mohamed Malick Fall, ya bayyana cewa yaƙi da kalaman ƙiyayya a wannan zamani na fasahar basirar wucin gadi (AI) na buƙatar haɗin kan kowa da kowa.
Ya ce dole ne gwamnatoci su ƙarfafa manufofi da dokoki da za su tabbatar da amfani da fasahar AI cikin adalci da ɗaukar nauyi, tare da kare haƙƙin ɗan adam da ‘yancin faɗin albarkacin baki.
A cewarsa, kamfanonin fasaha ma suna da alhakin tabbatar da cewa tsarin da suke ƙirƙirawa yana da gaskiya, adalci da kuma ɗaukar nauyi, domin kada algoritim ɗinsu ya zama hanyar yaɗa abubuwan da ke haddasa ƙiyayya ko rikici.
