Amurka ta yi amai ta lashe kan batun yarjejeniyar nukiliya da kuɗaɗen Iran da aka yi 

Spread the love

Saɓanin bayanai tsakanin Washington da Tehran ya tayar da ƙura kan yarjejeniyar kawo ƙarshen yaƙi, yayin da Majalisar Dattawan Amurka ta kaɗa ƙuri’ar dakatar da yaƙin duk da adawar Trump

Daga bayanan da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya tattara, wata sabuwar takaddama ta ɓulla tsakanin Amurka da Iran kan muhimman abubuwan da suka shafi yarjejeniyar da aka cimma domin kawo ƙarshen yaƙin da ya ɗauki watanni ana gwabzawa tsakanin ɓangarorin biyu.

Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa Iran ta amince a riƙa gudanar da bincike da sa ido kan cibiyoyinta na nukiliya har abada, amma Tehran ta fito karara ta musanta wannan iƙirari, tana mai cewa babu irin wannan yarjejeniya da aka cimma a tattaunawar da aka yi tsakanin ɓangarorin biyu.

Wannan saɓani ya sake jefa inuwa kan makomar yarjejeniyar zaman lafiyar da aka rattaba wa hannu a makon da ya gabata, wadda aka tsara domin kawo ƙarshen yaƙin da ya janyo asarar rayuka da barnar tattalin arziki a yankin Gabas ta Tsakiya.

Bayan kammala zagayen farko na tattaunawa a ƙasar Switzerland ranar Litinin, jami’an Amurka da na Iran sun gabatar da bayanai masu karo da juna kan wasu muhimman batutuwa da suka haɗa da yadda za a sarrafa kuɗaɗen Iran da aka daskarar a ƙasashen waje, ikon zirga-zirga a mashigin ruwa na Hormuz, da kuma batun yaƙin da Isra’ila ke yi a Lebanon.

Duk da haka, Trump ya nuna kwarin gwiwa kan ci gaban tattaunawar, inda ya shaida wa magoya bayansa a wani gangamin siyasa da ya gudanar a Jihar Pennsylvania cewa al’amura na tafiya yadda ya kamata tsakaninsa da Iran.

A wani mataki da ya nuna alamun sassauci daga Washington, gwamnatin Amurka ta rage wasu takunkuman tafiye-tafiye da aka sanya wa tawagar ƙwallon ƙafar Iran da ke halartar gasar cin kofin duniya. Sabon tsarin ya ba wa tawagar damar isa birnin Seattle daga Tijuana da ke Mexico kwanaki biyu kafin wasansu na gaba maimakon kwana ɗaya kacal kamar yadda aka tsara tun farko.

Sai dai yayin da gwamnatin Trump ke ƙoƙarin nuna cewa yarjejeniyar na tafiya daidai, alamu sun fara bayyana cewa goyon bayan jama’a ga yaƙin na raguwa a cikin gida.

Wani binciken jin ra’ayin jama’a da Reuters tare da Ipsos suka gudanar ya nuna cewa kashi 35 cikin ɗari na Amurkawa na ganin ƙasarsu ta shiga mawuyacin hali fiye da yadda take kafin fara yaƙin da Iran, yayin da kashi 23 cikin ɗari ne kawai suka yi imanin cewa Amurka ta fi ƙarfin da take da shi a baya.

By ukarofi