Da dama sun jikkata yayin da sabbin kuratan sojoji suka yi hatsari a hanyar Zariya

Spread the love

Wasu daga cikin sababbin matasan da aka ɗiba aikin soja sun yi hatsari yayin da suka taho daga Jihar Imo domin fara karɓar horo a sansanin horar da Sojojin Nijeriya da ke Zariya, Jihar Kaduna, a safiyar Asabar.

A cewar wasu majiyoyin soji, masu neman aikin na kan hanyarsu ta zuwa cibiyar horaswa domin fara horon soja lokacin da hatsarin ya faru. An ce tafiyar tana ƙarƙashin kulawar Laftanar Kanal P.D. Ngal.

Majiyar ta ce sun tashi daga Jihar Imo zuwa Zariya kafin wannan mummunan hatsari ya afku.

Bidiyoyin da ke yawo a kafafen sada zumunta sun nuna wasu daga cikin waɗanda suka jikkata kwance a gefen hanya da kuma cikin motocin da suka lalace, yayin da jami’an ceto da masu wucewa ke ƙoƙarin ceto su. Daga bisani an kai da dama daga cikinsu asibitoci domin samun kulawar likitoci.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a tabbatar da musabbabin hatsarin ba, haka kuma ba a sanar da adadin waɗanda suka jikkata ko suka rasa rayukansu a hukumance ba.

Sansanin na Sojojin Najeriya da ke Zariya ita ce cibiyar horas da sabbin sojoji, inda masu neman aikin da suka yi nasara ke shafe watanni suna samun horo mai tsanani kafin a ɗauke su aiki a hukumance.

Majiyoyin soji sun kuma bayyana cewa duk mai neman aikin da ya samu mummunan rauni kafin ko yayin horo, kuma ya kasa kammala atisayen da ake buƙata, na iya rasa damar ci gaba da aikin saboda dalilan rashin lafiya.

By Babaji

Leave a Reply