
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Rundunar Sojojin Nijeriya ta bayyana cewa, waɗanda aka kama da hannu a laifin gudanar da haramtattun masana’antun haɗa makamai a Jihar Filato, sun amsa cewa suna samarwa tare da sayer wa ‘yan ta’addan Fulani saboda suna biyan farashi mai tsoka akan sauran masu siya, fallasa abin da hukumomi suka kira da babban sababin ruruwar rikicin jihar.
Selong Sule, shugaban dakarun Atisayen Safe Haven (OPSH) a lokacin da yake ganawa da taron manema labaran sojoji a Jos a madadin Babban jami’in rundunar (GOC) ta uku kuma kwamandan atisayen ne ya bayyana haka.
A cewar Zagazola Makama, Sule ya ce an yin nasarar kama masu laifin ne bayan wani bincike na sirri da aka gudanar da ya taimaka wajen ganowa da lalata haramtattun masana’antun haɗa makamai a jihar.
Sule ya bayyana cewa, wasu daga cikin mutanen, da fari sun yi iƙirarin suna samar da makaman ne da nufin kariyar kai ga yankunansu, amma daga bisani suka amsa cewa sayar wa mayaƙan Fulani suke yi saboda sun fi biyan farashi da kaso mai tsoka.
Babban jami’in ya ƙara da cewa, makaman gargajiya da ake samarwa barazana ce ga ayyukan jami’an tsaro a Filato.
Kazalika, ya ce duk da cewa fararen hula da dama suna mallakar bindigogi don kare kai, kewayawar haramtattun makamai acikin al’umma na ƙara yawan aikata manyan laifuka da rikicin ƙabilanci a sassan jihar.
