Buhari ya halarci bikin rantsar da Shugaban Ƙasar Gambia

A yau Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya tafi ƙasar Gambia don halartar bikin rantsar da Shugaban Ƙasar, Adama Barrow.

Jakadan Nijeriya a ƙasar Gambia, Mohammed Manu Kola tare da Mataimakin Shugaban Gambia, Dr. Isatou Touray da sauransu na daga cikin waɗanda suka tarbi Buhari da tawagarsa a Babban Filin Jirgin Saman Banjul na ƙasar.