Mataimaki na musamman kan gangamin jama’a a gwamnatin Katsina Alhaji Abdulaziz Maituraka ya raba ƙwai da indomi ga mutane 200 masu sana’ar shayi a garin Katsina.
Haka kuma Maituraka ya raba wa ya’yan jam’iyar APC na ƙaramar hukumar Katsina tallafin kuɗi Naira miliyan huɗu.
Ya bayyana cewa ya’yan jam’iyar na ƙasa za su amfana da tallafin na kuɗi kyauta da suka haɗa da shugabannin jam’iyar na ƙaramar hukumar Katsina da shugabannin jam’iyar a matakin gunduma.
Sauran sun haɗa da kansiloli 11 da tsaffin kansiloli da shugabannin rumfunar zaɓe na karamar hukumar.
Maituraka wanda yake magana ga dandazon ya’yan jam’iyar a Katsina ya ce wannan tallafi da ya bada ya amsa kiran da Gwamna Dikko Raɗɗa ya yi kan manyan ya’yan jam’iyar APC a jihar da su fito su tallafawa ya’yan jam’iyar waɗanda ke ƙasa da su.
Ya kuma yi alƙawarin cigaba da tallafawa masu ƙananan sana’o’i da ya’yan jam’iyar masu ƙaramin ƙarfi.
Banda wannan tallafi na kayan sana’a da kuɗi ga ya’yan jam’iyar har wala yau Maituraka ya karrama wasu fitattun manyan jami’an ‘yan sanda biyu masu ritaya da suka yi fice wajen yaƙi da matsalar tsaro a ƙaramar hukumar Katsina.
A jawabinsa, shugaban jam’iyar APC na jihar Katsina Dr Bishir Gambo Saulawa ya yabawa Maituraka da ya amsa kiran da Gwamna Dikko Raɗɗa ya yi kan tallafawa al’umma musamman ya’yan jam’iyar APC a jihar.
Ya yi kira ga jiga jigan ya’yan jam’iyar da suyi koyi da irin wannan ƙoƙarin da Maituraka ke yi wajen tallafawa masu ƙananan sana’o’i, ya’yan jam’iyar APC da ciyar da mabuƙata a jihar.
Shugaban jam’iyar ya kuma shawarci yan adawa a jihar da su rinƙa duba da sharhi mai ma’ana ga ayyuka da gwamnatin Dikko Raɗɗa ta aiwatar maimakon maida hankali wajen sukar shi gwamnan.
Dr Saulawa ya taɓo aikace aikacena raya ƙasa da gwamnatin Dikko Raɗɗa ta aiwatar a fannin kiwon lafiya,ilimi,raya birane da gina alumma.
