Mai Mala Buni na musamman ne a Nijeriya – Nura Dalhatu

Kwamared Nura Dalhatu Audu, ya bayyana cewa, Gwamnan Jihar Yobe, Hon. Mai Mala Buni, na musamman ne a Nijeriya. Saboda haka ne ma ya ke samun nasarori ga duk abin da ya tunkara a rayuwarsa. A cikin wannan tattaunawar da ya yi da manema labarai, ciki har da Wakilin Blueprint Manhaja, MUHAMMAD AL-AMEEN, tare da sauran muhimman batutuwa. Ga yadda cikakkiyar tattaunawar take:

Masu karatu za su so sanin Kwamared Nura Dalhatu Audu?
Alhamdulillah, kamar yadda duk wanda ya sanni sunana Nura Dalhatu Audu, kuma an haife ni a garin Gashuwa, ta ƙaramar hukumar mulkin Bade a jihar Yobe sannan kuma na yi karatunan firamare da sakandire tare da NCE a mahaifata, wanda daga bisani na tafi Jami’ar Ahamdu Bello da ke Zariya na yi digiri a fannin ilimin tarihi, wanda kuma yanzu haka ina digiri na biyu a jami’ar. Baya haka kuma ni ɗan siyasa ne kuma ina taɓa kasuwanci domin dogaro da kaina da kuma taimakon masu ƙaramin ƙarfi a cikin al’umma. Sannan kuma na taɓa Koyarwa a makarantun gwamnati da sauran ayyukan taimakon kai da kai daga cikin ɗan abin da Allah ya hore min. Wanda a lokuta da dama mu kan tallafa wa yara maras galihu ta hanyar saka su makaranta ko almajirai da ‘yan gudun hijira. Har wala yau muna kai taimako a gidan yari da ke garin Gashuwa domin taimaka wa yan fursuna da magungunan zazzabin cizon sauro da sauran kayan abinci da makamantan su, kuma in sha Allah zan ci gaba a ƙoƙarin tallafa wa mabuƙata da ɗan abin da muke da shi iya gwargwadon hali. Saboda burinmu shi ne mu ma mu tallafa domin daɗaɗa wa al’umma kuma don ya kasance a rayuwar mu mun yi abin a zo a gani kuma jama’a ta amfana da rayuwar mu. Wannan shi ne kaɗan daga cikin burinmu a rayuwa, kuma Alhamdulillah muna matuƙar godiya ga Allah kan wannan dama da ya bamu. Sannan kuma wannan ita ce tarbiyyar da Maigidanmu Gwamna Mai Mala Buni ya koya mana kuma muke alfahari da ita a matsayin mu na yaransa kuma yan gani-kashenin shi. Har wala yau, dangantaka ta da Gwamna Buni ta zarta ‘goyon baya’ ni “Xan Gani-kashenin sa ne, yayin da ƙaunar shi ta zama aƙida a wajena. Sannan kuma tsohuwar alaƙa ce tsakanina da Gwaamna Buni, tun a jam’iyyar ACD da AC. 

Yaushe ne alaƙarka da gwamnan ta faro?
Gaskiyar magana alaƙarmu da Maigirma Gwamna ta faro ne tun wani zuwan su garin Gashuwa, a lokacin ya na shugaban jam’iyyar AC da Alhaji Tijjani Tumsa; a lokacin shi ne ɗan takarar Gwamna a jam’iyyar, da kuma marigayi Muhammad Laminu wanda a lokacin shi ne ɗan takarar Majalisar dokoko a ƙaramar hukumar Bade. Shi ne ya ganni sai ya riƙe hannuna ya ce min: “Samari me sunanka?” Sai na gaya masa sunana Nura Dalhatu Audu, wanda tun daga wannan ranar ya bani lambar wayarsa muke gajsa wa. A haka muke dashi har ya dawo jam’iyyar ANPP, a zamanin Marigayi Gwamna Mamman Ali, haka ya kasance maigidana. Sannan wannan bai tsaya nan ba, abin ya kasance a matsayin babban maigidana al’amarin da ya kai ga kusan a gidansa babu wanda bai sanni ba, tare da abokanansa da sauran jama’arsa duk sun san ni yaronsa ne. Kuma ya na matuqar girmama ni kuma ya ɗauke ni tamkar ɗansa da ya haifa ta fannin bani shawarwari da ƙarfin gwiwa, wanda ya kai ga idan zai wuce zuwa Abuja ko Kaduna ya kan tsaya ya dubani a lokacin da nake Jami’ar Ahamdu Bello da ke Zariya- shi da abokinsa Alhaji Ari-Baye tare da wani direbansa Aloma, ya ƙarfafa ni ya ce mu dage muyi karatu, kuma ya taimaka min ta hanyoyi da dama. 

Me za ka ce dangane da yadda ya haɗa ayyuka biyu a lokaci guda: a matsayin gwamnan jihar Yobe kuma shugaban riƙo na APC na ƙasa? 
Gaskiya a matsayina na mai fafutikar inganta rayuwar jama’a, mai son ganin al’umma suna samun walwala da daidaito, a rayu cikin yanci da jin daɗi. Kuma mai burin ganin an bar kowa ya yi ra’ayinsa matuƙar bai taka dokokin Allah ko na ƙasa ba. Na yi murna kuma ina matuƙar jin daɗin salon gwamnatin Gwamna Mai Mala Buni, saboda idan kayi la’akari da lokacin sa ya karɓi jagorancin wannan jihar daga wanda ya gada- Sanata Alhaji Ibrahim Gaidam; muna addu’a Allah ya ƙara masa lafiya. Wanda Ina bibiyar jawabin kama aiki da ya gubatar a babban ɗakin taron gidan gwamnatin jihar Yobe, kuma tun a wancan lokacin har yanzu ina bin kalaman da ayyukan da ya alƙawarta, kuma kawowa yanzu ya cika kaso 97 da ɗigo 99 daga cikin alƙawarin da ya yi wa al’ummar jihar Yobe. Wanda duk da a matsayin mu na yan Adam, mun nazarci waɗannan alƙawarun kuma mun gansu a aikace, waɗanda su ka haɗa da dawo da hawa mashin mai ƙafa biyu, gina kasuwanni zamani a manyan garuruwan jihar Yobe, inganta tsarin kiwon lafiya fiye da kowane lokaci. Sannan uwa uba da sauya fasalin harkokin ilimi a wannan jihar tamu. Idan za a tuna, jihar Yobe ta na ɗaya daga cikin jihohin Arewa Maso Gabas da ta ɗanɗana kuɗarsu a hannun Boko Haram, matsalar da ta kassara al’ummar wannan jihar tare da mayar da hannun agogo baya a fannin ci gaba. Har wala yau, masu hikimar magana sun ce: cika alƙawari sai ɗa. Saboda haka Gwamna Buni ya cika alƙawarin da ya ɗauka kuma muna addu’a Allah ya saka masa da alheri. 

Baya ga haka kuma, matsalar tsaron Boko Haram ta kawo cikas a tsarin ilimi a wannan jihar, sun ƙona makarantu kuma sun kashe ɗalibai da malamai da dama a jihar Yobe wanda wannan ne ya jefa fargaba da tsoro a zukatan malamai, iyaye da ɗalibai kansu. Misali hakan ya faru a GSS Dapchi, FGCC Buni-Gari, Kwalejin Aikin Noma da ke Gujba, Mamuɗo, da Potiskum da sauran su, wanda ko shakka babu babban ƙalubale ne ga harkokin ilimi. Sannan lamarin ya jawo wasu iyaye sun janye ya’yansu daga makarantu a wannan jihar zuwa maƙwabtan jihohi irin su Bauchi, Gombe, Jigawa da makamantan su, inda wasu har Jamhuriyar Nijar sun kai yaransu karatu. Amma zuwan gwamnatin Alhaji Mai Mala Buni an samar da sabbin tsare-tsare masu ma’ana a fannin farfaɗo da harkokin ilimi. Musamman irin yadda ya ayyana dokar-ta-ɓaci a harkar ilimi. Wanda ko a wannan makon da ya gabata duniya ta ga ƙwarewar da ya nuna na kafa gidauniyar bunƙasa ilimi a Abuja al’amarin da kwalliya ta biya kuɗin sabulu. Sannan da samar da kasuwanin zamani a Damaturu, Gashuwa, Potiskuma, Nguru da Buni-Yadi. Gina gidajen 3600 a faɗin jihar Yobe tare da sauya fasalin harkokin kiwon lafiya da bunƙasa aikin noma da makamantan su.

Waɗanne abubuwa ne kake ganin sun taimaka wa Gwamna Buni wajen samun nasarori?
Ɗaya daga cikin dalilan da ya sa Gwamnan jihar Yobe, kuma shugaban riƙo na jam’iyyar APC na kasa, Hon. Mai Mala Buni ya samu nasarori a duk abin da ya tinkara a rayuwa, su ne kasancewar sa mutum ne mai girmama ilimi tare da fahimtar duk wanda ya yi mu’amala da shi. Sannan kuma mutum ne wanda Allah ya ba shi kaifin basira da zurfin tunani haɗi da hangen nesa. Haka kuma dattijo ne mai halin dattaku. Domin ya karɓi riqon APC a lokacin da ta faɗa rikicin cikin gidan da ya yi kusa durƙusar da ita. Wanda bisa irin wannan kaifin basira tare da zurfin tunani da girmama fahimtar kowa, ya ba shi damar sake dawo da jam’iyyar hayyacinta, cikin ƙanƙanin lokaci. Yayin da ya rinƙa bin mambobin jam’iyyar APC waɗanda aka ɓata wa rai har gida yana lallashin su cikin dadadan kalamai. 

Ya rinƙa bin manyan jam’iyyar har gida ya na lallashin su a matsayin su na waɗanda suka yi ƙoƙarin kafa ta, a ce da su za a rusata ba. Wannan salon ya yi amfani da shi wajen sake haɗa kan APC daga kowane lungu a ƙasar nan. Wanda yanzu duk dan jam’iyyar APC baya shakku dangane da hoɓasar Hon. Mai Mala Buni kan nasarorin da ya samu a matsayin shugaban riƙon, wanda ya samar da cikakken haɗin kai da fahimtar juna tsakanin yan jam’iyyar APC da ‘yan Nijeria baki ɗaya. Haka kuma kasancewar sa tsohon sakataren APC na kasa ya ba shi damar fahimtar wasu daga cikin matsalolin da take fuskanta, baya ga ilimin da yake da shi a siyasa tun daga matakin gunduma 1992 (Councilor) zuwa matakin da yake a kai na shugaban riƙon jam’iyyar na ƙasa, a hannu guda kuma Governor jihar Yobe. Wanda ko shakka babu ba kowane mutum ne; shi kaɗai, zai gudanar da waɗannan muhimman ayyuka cikin nasara ba. 
Baya ga wannan, Governor Buni ya yi amfani da hikimomin da Allah ya bashi wajen gudanar da jam’iyyar APC a matakin kasa tare da tafiyar da mulkin jihar Yobe cikin nasara.

Wanda ya samar da ci gaban da wannan jihar ba ta taba ganin makamancin shi ba, ta fuskancin ilimi, kiwon lafiya, kasuwanci da farfaɗo da tattalin arziki, bayar da kulawa ta musamman ga matasa da ayyukan noma. Wanda a jawabin Gwamna Buni bayan rantsar da shi ya ayyana dokar-ta-ɓaci a harkokin ilimi, wanda ya ba shi dama wajen karkata akalar zuwa ga bunƙasa shi ta hanyar gina sabbin makarantu tare da gyara waɗanda suka lalace da sauya wa tsarin ilimin fasali daidai da zamani kuma da buƙatun al’umma. Gina cibiyoyin kiyon lafiya sabbi a kowace gunduma da ke daɗin jihar Yobe, gina manyan asibitoci tare da daga darajar wasu zuwa na ƙwararru, samar da isasaun likitoci da ma’aikatan jinya da a jihar. 

Bugu da ƙari, Gwamnatin Buni ta samar da sababbin tsare-tsaren kiyon lafiya don ma’aikatan jihar Yobe da talakawa tare da samar da motocin ɗaukar majinyata daga yankunan karkara zuwa birane don sauƙaƙe wahalhalun da ake fuskanta. Baya ga gina hanyoyin mota don raya ƙauyuka da birane tare da inganta harkokin zirga-zurgar ababen hawa da dakon kayan amfanin gona zuwa kasuwani. Gwamna Buni ya yi amfani da hikimomin da Allah ya ba shi wajen tafiya kafaɗa da kafaɗa da matasan jihar Yobe, wannan ya zo ne ta la’akari da ya yi cewa matasa su ne ƙashin bayan ci gaban kowace al’umma, sannan da kasancewar su shugabanin gobe. Haka kuma sanin kowa ne jihar Yobe ta na ɗaya daga cikin yankunan da suka sha fama da matsalar tsaron Boko Haram, al’amarin da ya fi shafar matasa, wanda samar wa matasa aikin yi tare da Sana’a zai taimaka gaya. 

Tun bayan ƙirƙiro jihar Yobe ba a taɓa samun gwamnatin da ta tallafi matasa kamar ta Gwamna Mai Mala Buni ba, wanda a zahiri mu matasa muna godiya an gina mu sosai. Gwamna Buni ya raba wa daruruwa jarin Sana’a, wasu an taimaka musu da gidaje wasu kwangila, don su samu jarin sana’o’in da za su dogara da kansu. Sannan in takaice maka, a halin da ake ciki yanzu, akwai daga cikin irin wadannan matasan waɗanda Dubai suke tafiya sayo kaya su kawo nan kuma yanzu haka suma sun tallafi wasu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *