Zawarci ba lasisin fitsara ba ne

Daga AMINA YUSUF ALI

Barkan mu da sake haɗuwa a wani makon. Sannun ku da jimirin karatun filinku na Zamantakewa a jaridar Blueprint Manhajarku mai farin jini. A wannan mako zan so na yi magana a kan zawarawa da barazanar da suke fuskanta.

Da farko dai wace ce bazawara? Bazawara ita ce wacce ta rabu da mijinta ta hanyar sakin aure ko kuma wanda ya mutu, ko ma wanda ya ɓace. Ƙasar Hausa kamar yadda muke gani a halin yanzu, ta zama tamkar shalkwatar yaye ƙanana da manyan zawarawa har ma da dattijai. Ba sai na kawo dalilan da suke jawo yawaitar mace-macen aure a ƙasar Hausa ba a cikin wannan rubutun. Amma insha’Allah ina da niyyar kawowa a wani rubutu a gaba.

Amma abinda za mu lura shi ne, mutuwar aure ta yawaita sosai a ƙasar Hausa. Ta yadda da wuya ka iya nuna wani mutum guda wanda zai iya bugar ƙirji ya ce ba bazawara a danginsu ko guda ɗaya. To ba wani abu nake son faɗa a wannan mako ba illa yadda zawarci ya zama dandalin bajekolin fitsara a wajen wasu mata. Da kuma barazanar da yake haifarwa. 

A ƙasar Hausa da zarar an ce ga bazawara, maza marasa kirki sun yi rubdugu don kawai su a wajensu garaɓasa ta samu. 

Haka wasu matan marasa kirki. da zarar mace aurenta ya mutu ko mijinta ya mutu, wata ba ta bari ta ƙarasa ko iddarta ba ma sai ka ga ta ɓalle da bushasha. Tuni su ma ƙadangarun bariki kamar da ma kaɗan suke jira. Sai a zo a yi mata rubdugu kamar Allah ya aiko su. Wasu su zo da niyyar fasiƙanci sak, ta hanyar amfani da damar cewa yanzu fa tana cike da kewar namiji. Wasu kuma su zo da sigar nuna mata kuɗi da abin Duniya, idan kwaɗayayya ce kun ga ai sai ta afka. Wani kuma da niyyar aure zai zo mata, amma sai ya yi amfani da son auren da take yi ko son da take yi masa ya shigar da buƙatarsa. Kafin ka ankara sai ka ga matar da take kamilalliya mai tsoron Allah lokacin da tana gidan miji, yanzu ta zama tantiriyar ‘yar Duniya ta buga misali. To me yake jawo haka? 

*Kwaɗayi: Wasu matan akwai kwaɗayi da son burga da gasa da ƙawaye. So suke su haɗa kansu da sauran ƙawayensu ‘yammata da zawarawa masu kuɗi ta fuskar kwalliya da ado da sauran abubuwan rayuwa. Sai dai kuma ita ba sana’a ko nema ta iya ba. Don haka, za ta yi ƙoƙarin yadda za ta samu kuɗaɗen yin bushasha don burga. Shi ya sa sai ka ga sun fara bin mazajen banza don su samu kuɗaɗen da za su biya waɗancan buƙatun nasu. A haka bazawara ko ta Allah ce, kwaɗayinta zai sa su kuma mazajen su yi amfani da damarsu don ganin an yi ban gishiri, in ba ki manda. Daga nan kuma idonta ya buɗe, wata ko aure sai ta ƙi yi saboda bariki ta riga ta buɗe mata ido. Tana ganin ta riga ta rungumi a binda ya fi aure a hannunta.

Amma ‘yaruwa kina tuna tsufa kuwa? Lokacin da kyawunki da surarki ba za su birge su waɗancan ƙadangarun barikin ba? Sannan kina tuna mutuwa da makomarki bayan kin mutu. Haka kada ki manta ko bayan mutuwa kin bar zuriya a baya. Wanne tarihi kika bar musu wanda da su da sauran al’umma za su tuna ki da shi?

*Rashin kulawa daga tsohon miji ko danginsa. Mun zo zamanin da da zarar an saki mace to har yaranta ma an saki. Sai ka ga ubansu ko danginsa dukka ba abinda ya sha musu kai da yaranta ko ita. Wata ma mijin mutuwa ya yi. Kuma ba lallai ne kowanne mutum idan ya mutu a ce ya bar wa iyalinsa wani abu ba. Amma sai ka ga gabaɗaya dangin uba saboda rashin zumunci an watsar da yaran ɗanuwansu. Wannan uwar idan iyayenta ba su da ƙarfi haka za ta yi ta faɗi-tashi tana samar da abinda za su rayu tare da yasnta. Ga ci da sha, sutura, ilimi, lafiya da sauransu.To irin waɗannan mata idan ba a samu masu tsoron Allah ba, ai ba hanyar da ba za su bi don samar wa yaransu rayuwa ba, ko halas ko haram.

Zawarawa da dama sun afka cikin irin wannan ƙangi na rayuwa. Sai ka ga mazajen banza sun yi amfani da wannan raunin sun yi alƙawari fitar da ita daga ƙangi idan har ta amince da su. Kuma ba kowacce ke iya tsallake wannan siraɗin ba. Kuma daga ta fara su ɗaya, ta tsaga ta ga jini, shikenan. Da wuya ta daina idan ba ikon Allah ba.

*Wasareren iyaye: Iyaye suna mantawa tare da wasarere da ɗiyarsu mace bazawara. Sun manta ita tana jin tana da lasisi za ta iya aikata dukkan abubuwan da budurwa ba ta ƙoƙarin aikatawa. Shi ma wannan rashin sa idon na saka zawarawa cin karensu babu babbaka. Ya kamata iyaye su kula da haka. Sannan su tallafa mata. 

*Rashin haƙuri: Wasu matan da ma Allah ya halicce su da ɗabi’ar rashin haƙurin iya zama ba tare da aure ba. Daga ƙaddarar zawarci ta samu waɗannan mata, sai idonsu ya rufe. Kawai su su yi wani aure. To a garin son auren sai su iya faɗawa hannun ɓata-garin maza waɗannda za su yi amfani da son auren nata su keta mata haddi. Wasu zawarawan kuma da ma ko ba auren suke da niyyar yi ba. Kawai za su yi amfani da kowacce irin dama don samun biyan buƙata. 

*Mazan banza: Kamar yadda na faɗa a baya, maza ma suna taka babbar rawa wajen tsunduma zawarawa a harkar banza. Maza da yawa sukan zo wajen bazawara saboda suna ganin ta taɓa aure kuma tana da sauƙin yaudaruwa. Sukan yi amfani da zaman da ta yi na tsahon lokaci ba aure kuma sun san rai da jini ba za ta kasa kewar aure a ranta ba. Idan kuma da ma kwaɗayayyiya ce, ko kuma tana cikin mawuyacin hali na babu, to abin ya zo masa da sauƙi. Sai ya yi amfani da dukka makaman nasa guda biyu ya yo zabarin hankalinta ya cutar da ita. Zamani ya zo da maza wai ba za su taimaki bazawara don Allah ba sai don suna sonta ko don suna buƙatar wani abu a wajenta. Sai ka ga bazawara idan mai tsoron Allah ce, sai ka ta tagayyara. Ba wanda zai kawo mata ɗauki don an san ba za a samu komai daga wajenta ba. 

*Ƙara’i: Akwai mata masu son ƙara’i. Da zarar mijinta ya mutu ko sun rabu shikenan harka ta buɗe. Duk wata fitsara da take sha’awar yi a baya aure ya yi mata shamaki, to yanzu za ta ɓalle ta. Duk irin kayan da take son sa wa a da, yanzu za ta saka su. Kafin ka ce kwabo saliha ta zama tantiriya. Irin waɗannan matan da yawa su suke kashe aurarrakinsu da kansu. Don sun yi kewar rayuwar ‘yanci daga takurawar da suke ganin aure yana yi musu. Wata ma sha’awar ganin ƙawayenta zawarawa ne yake sa wa ta ji ita ma tana begen ta shaƙi iskar ‘yanci kamar su. 

*Zuga: Wasu zawarawan kuma zuga daga ƙawaye ita ke jawowa su faɗa harkar bariki ka’in da na’in. 

Amma jama’a su sani, ba dukka aka taru aka zama ɗaya ba. Akwai zawarawa sosai na kirki masu tsoron Allah waɗanda halin da suke ciki bai sa zuciyarsu ta yi rawa ta karkata ga saɓa wa Allah ba. Irin waɗannan su ne masu kunyata shaiɗan la’ananne. 

Waɗanda muke magana su ne waɗanda suke ganin zawarci ya ba su lasisin yin duk abinda suka ga dama ba tare da an gane ba. Tunda suna ganin ba rubutawa za a yi a goshinsu a ce sun aikata mugun aiki ba. Ko da aure za su ƙara kuma ba su da fargabar budurci kamar yadda ‘yammata ke tsoro kada su je a gane sun yi wani abu kafin su yi aure. Su da ma an riga an san sun yi aure. Duk wanda aure su da ma ya san ba budurwa zai samu ba.  

*Kawar da damuwa: Wasu zawarawan kuma damuwa tana yi musu yawa matuƙa, har ma su dinga neman mafita don sauƙaƙa damuwar zuciyarsu. Masu magana sun ce, idan ruwa ya ciwo mutum, ko takobi aka miqo masa cafkewa zai yi. Don haka, dan ba ta yi sa’a ba su ma za su iya cin karo da waɗancan maza ko ƙawaye da za su kawo mata mafitar shiga Duniya.

Ina mafita? 
Mafita iyaye su duba girman Allah da amanar ‘ya’yansu, su dinga barin yaransu na karatu ko koyon wata sana’a wacce za ta tallafa musu a rayuwa.Tunda ba wanda ya san gaba ko ya san gawar fari. Kada aure ya mutu ko miji ya mutu ta rasa tudun dafawa ta faɗa hannun waɗancan ɓata-gari. Haka iyaye su dinga sa ido kan ‘ya’yansu mata zawarawa fiye da yadda za su sanya wa ‘yammata. Sannan idan da hali su tabbatar sun sauke mata wahalhalu da damuwar rayuwa da suke  addabarta. 

Hakazalika, al’ummar ƙasar Hausa a daina ɗaure wa mazaje gindi wajen bar wa mace ragamar yaranta. A daure a dinga tallafa wa mata idan an rabu da su da yara. Kada miji ya yi wasarere da wannan haƙƙi. Haka ‘yanuwa da dangi a daina kau da kai idan ɗanuwanku ya watsar da yaransa kawai don ya rabu da uwarsu. Ku ma kun haifa, kuma yaranku mata za su iya zama zawarawa watarana. Idan an gyara abun kowa zai amfana.

Haka waɗanda ɗanuwansu ya mutu ya bar mata da yara su daure su yi zumunci don Allah kaɗai ba don suna sonta ko neman wani abu gurin matar ba. Su kuma maza masu irin haka su sani, su ma fa sun haifa kuma Annabi SAW bai yi ƙarya ba. Zina gado ce, idan ka yi da wata dole kai ma a yi da matarka ko ‘ya ko ƙanwa da makamantansu.

Ke kuma ‘yaruwa ki tattara hankalinki mutuwar aure ko ta miji wata babbar jarrabawa ce Allah ya saukar miki. Wacce idan kika yi wasa za ta iya zame miki silar raba ki da rahamar Allah. Haka idan kika haye, za ta iya zamar miki silar samun rahamar Allah. Ki tabbatar kin tara hankalinki kada ki bari ruɗin Duniya ya ɗebe ki. 

Yayin da kike zaman gidan miji, kada ki sangarce ki ce wai ke shikenan ba za ki nemi sana’a ko aikin yi ba. Sana’a tana da matuƙar muhimmanci ko don saboda zawarci wanda ba a sa masa rana. Idan da sana’arki ko yaya za ki iya rufa wa kanki asiri. Rashin sanin madogara shi ne yake jefa ki a kowacce irin damuwa da fatara da talauci har wasu miyagun maza su yi amfani da wannan damar don jefa ki ga halaka. 

Sannan kuma ki ji tsoron Allah. Ki kama kanki. Duk abinda Allah ya yi za ki samu, ko kin bi maza, ko ba ki bi ba, za ki samu. Sannan kwaɗayi Hausawa sun ce, mabuɗin wahala. Ba inda zai kai ki sai taɓewa. 

Sannan kuma kada garin dole sai kin yi aure ki gayyato ɓata-gari cikin rayuwarki. Idan lokaci ya yi fa shi auren nan dole ki yi shi. Idan kuwa lokacinki bai yi ba duk nacinki sai kin haƙura. Don haka ki bi a hankali kada garin nema da son aure ido rufe ki faɗa hannun ‘yan sari. Waɗanda za su yi amfani da damarki su dama kuma su bar ki cikin takaici da nadama. Domin akwai nadama mai tsanani ga wanda ya kauce hanya yana sane.

Allah dai ya datar da mu ya yi mana kyakkyawan ƙarshe. Makaranta masu kira da saƙon tes ko imel muna godiya da addu’a da shawara da kuma ƙarfafa mana gwiwa. Allah ya saka da alkhairi ya bar zumunci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *