Aikin albashin Naira 270,000 na ajiye na koma gyaran takalmi a zamance – Abubakar Sadik Umar

Daga Ibrahim Hamisu, Kano

Malam Abubakar Sadik Umar wani haziƙin mtashi ne ɗan baiwa da ya ke gyaran takalmi a zamanance a cikin ƙwaryar Birnin Kano. A hirarsa da Wakilin Manhaja, Ibrahim Hamisu a Kano, za ku ji irin yadda tsohon ɗan takarar Gwamna na Jihar Kano ya bayyana irin yadda ya ke gyara wa manyan mutane a Nijeriya takalmansu da kuma yadda ya ke biyan ma’aikatansa albashin Naira 350,000 a wata. Ku biyo mu.

Za mu so ka gabatar mana da kanka?
Sunana Abubakar Sadik Umar. An haife ni a shekarar 1973, a ƙaramar hukumar Gwaram, ta jihar Jigawa. Na yi makarantar Firamare a Tarauni. Sannan na yi Sakandire ta Government commercial Wudil, jihar Kano. Daga nan na je Kaduna Polytechnic Na yi Diploma, na je Jam’iar Abuja na karanci ilimin aikin Banki wato Accounting. Sannan kuma na yi takarar gwamnan jihar Kano a 2019 karkashin jam’iyyar PPC. Na yi aiki a Bank of North, na yi aiki a Kamfanin Fansho, sannan na yi aiki a Ma’aikatar Shari’a ta tarayya.

Wacce sana’a ka ke aiwatarwa?
Sana’a ta ita ce gyaran, takalmi. Amma gyaran Takalmin da nake yi, amma ba  irin wanda aka saba da shi ba. Domin tunda muka taso, mun san akwai daukawa. Duk da yake ni ma dukanci nake yi, amma a inda nawa ya sha bambam shi ne, ni na haɗa abubuwa da yawa. Kamar gyaran takalmi da canja shi daga wata kalar zuwa wata kalar, sannan muna iya karɓar naka, sai mu ba ka wani.


Haka kuma nan gaba kaɗan, yiza mu fara ba da haya. Misali, za ka je biki na fita kunya, ko za ta je biki na fita kunya, sai ta zo mu ba ta takalmi da jaka ta je ta yi bikinta ta dawo mana da shi. Ko  misali, Sallah ce ta zo ba ka da halin saya wa yara takalma a wannan shekarar, sai ka zo mu hayar maka da takalma ka je ka yi bikin sallarka ka dawo mana da su. 

Ta yaya sana’ar gyaran takalminka ta sha bambam da sauran?
Ta inda tamu ta sha bamban da sauran shi ne, kowa ya sani cewa, mai gyaran takalmi ba ya sayar da takalmi. Amma mu muna sayarwar. Kuma ba sabo muke sayarwa ba. Wanda ka gaji da shi, shi za ka kawo mana, mu gyara, mu sayar maka. Ko kuma takalminka ya mutu, ka yanke ƙauna da shi, sai ka kawo sai mu farfaɗo maka da shi, ya dawo kamar sabo. Haka Jakar mata ko belt da duk wani  abu da ya ke fata ce ko Leda ko kujeru da sauransu. Duk abinda suka yi komai lalacewar da suka yi, mu za mu gyara shi. Wani ƙarin bambancin da muke da shi da dukawa shi ne, mu Injina ne muke amfani da su, ta yadda duk abinda muke so mu saita shi za mu yi, mu saka shi a Inji ya mayar maka abinda kake so, ya mayar maka.

Me ya ja hankalinka, ka kafa wannan masana’anta ta gyaran takalma?
To, wannan sana’a dai ba gadonta na yi ba. Hasali ma dai gidanmu da  ‘yanuwana na kusa da na nesa duk ma’aikatan gwamnati ne, babu ɗan kasuwa. Ni ma na yi aiki a Banki shekara 11. To ni abinda na lura shi ne, na gane cewa ina da wata baiwa. To kuma idan ka gane kana da wata baiwa, to ya kamata ka yi amfani da ita, Kullum ina jin takaicin cewa na zauna a ƙarƙashin wani, yana ɗaukar albashi yana ba ni. Sai nake ganin me zai hana ni ma na samar wa wasu ayyuka?

Yanzu ka ga lokacin da na bar Banki abinda ake biyana shi ne Naira dubu ɗari biyu da saba’in N270,000. To amma yanzu da muke maganar nan da nake da kai, ina da ma’aikata da nake biyansu duk wata N350,000. To ka ga bayan  ni na ‘yanta kai na daga karɓar albashi, kuma ga shi na kafa kamfanin da shi kuma yake biyan albashi da ya kusa ɗaya da rabin da ni na riƙa karɓa. Kullum ni abinda nake fahimta shi ne, abokanmu na kudu suna yi mana gori cewa, mu kamar kaska ne. To jin cewa ana ce mana kaska ne, ya sa na yi tunanin cewa to  bari mu zo mu ma mu bai wa  matasanmu aikin yi. Maimakon mutum ya tafi kudu yana acaɓa da wankin takalmi da sauransu, kuma idan sun tashi suna yi mana izgilaci. Hakan ya sa na ce bari zan ɗauki sana’ar shu shaina na mayar da ita ta zamani. Ta yadda duk wanda ya zo ya gani zai yi sha’awa. Kuma Alhamdulillahi yanzu daga sanda muka fara  idan na gaya maka irin mutanen da suke zuwa suna kawo mana gyara da wankin takalmi, wanda wasunsu a da sai dai su kai Amurka, Indiya, Turkiyya, Italiya a gyara masu Takalman. Amma yanzu cikin ikon Allah, mu suke kawo wa. Kuma mun ɗauko shu shaina waɗanda suke yawo a gari, sai ka ga muna bai wa mutum albashin dubu 30 zuwa dubu 40.

A ina ka koyo wannan sana’a?
To a gaskiya ni mutum ne mai ƙirkire-ƙirkiren abubuwa. Don yanzu idan na gaya maka abubuwan da nake rubutawa, za ka sha mamaki. Domin duk wata sana’a da ake yin ta a gargajiyance zan iya ɗaukar ta na mai da ita ta zamani. Kuma kar ka ce rana tsaka nake yi, a’a rubutu nake yi. Yanzu wannan harkar takalmin da nake yi, na kai shekara huɗu da rabi ina rubuta hikimar kafin mu fara aiwatar da shi a aikace. kuma yanzu haka ma, ina da sana’o’in da nake rubutawa, akwai wacce idan na kammala ta, sai dai ƙasashen Afirka makotanmu sai sun zo sun nemi wannan abun.

Yaushe ka fara?
Kamar yadda na faɗa, tun ina aikin gwamnati na fara rubututawa. Amma da fara aiwatar da tsare-tsaren kusan shekaru 2 kenan. Amma da fara aikin gadan-gadan a ranar 6-11-2020, ka ga  watan gobe na cika shekara 1 kenan.

A ina ka samu injinan da kake amfani da su?
Wasu injinan na yo odarsu ne daga ƙasashen waje, wasu kuma ni na rubuta, na faɗi yadda nake so su zama, na baiwa mutanemu, suka ƙera min su.

Mutum Nawa ne a karkashinka? 
Yanzu dai aƙalla akwai mutum 15 da muke aiki tare da su. Baya ga mutane da yawa da muke sayen kayan aiki a wajensu, irin su zare da gam da ma waɗanda suke kai mana kaya da sauransu. Waɗannan a ƙalla za su kai kamar mutum 50.

Daga lokacin da ka fara zuwa yanzu, waɗanne irin nasarori za ka iya cewa ka samu?
To, Alhamdulillahi daga lokacin da na fara zuwa, yanzu aƙalla mutanen da suka zo suka kawo mana aiki, sun fi mutum 3,000. Na biyu, muna da kafofin sada zumunci, kafar su facebook, Tiwita, Instagram, Website da sauransu. Mutane da yawa suna shiga, suna ganin abubuwan da muke yi. Kuma gaskiya na yi mamaki yadda duniya ta karɓi abinda muke cikin ƙanƙanin lokaci. Kuma duk wani mutum da ka sani mai matsayi da kake  tunani a nan Nijeriya babu wanda ba a kawo min takalminsa na gyara ba. Mutum biyu ne kawai zan iya cirewa, wato gwamna da shugaban ƙasa. amma idan ka ɗauki sanatoci, ministoci, sarakuna, haka nan mata ‘ya’yan gwamnoni, ‘ya’yan ministoci duka suna kawo mana gyaran takalmi. Ka ga wannan babbar nasara ce.

Kuma za ka ga cewa, duk wanda ya zo ya kawo mana aiki, sai ya kawo mana wani. Kuma daga jahohi daban-daban  ana kawo mana aiki kuma suna jin dadi. Wata babbar nasarar ita ce, yadda na samar wa da mutane da suke zaune ba su da abin yi aiki. Na ɗauko su, na raya su, na ba su abin yi. kuma idan ka duba kusan shekaru 20 ina aikin gwamnati, amma a yanzu cikin ƙanƙanin lokaci, na shiga inda ban taɓa tunanin zan shiga ba. Gaskiya na gode wa Allah a kan wannan mafarki nawa, da ya zama gaskiya.

Waɗanne irin ƙalubale za ka iya cewa ka samu daga lokacin da ka fara zuwa yanzu?
Eh to ƙalubale bai wuce wani ya sayi takalmi ya tafi bai biya ka ba.  Amma ni gaskiya, na fi kallon nasara a kan ƙalubale. Wani ƙalubale shi ne, da ina da kuɗin da so nake na bai wa aƙalla mutum 30 aikin yi. Kuma ina tabbatar maka da cewa  idan da wadatattun kuɗi da zan iya samar wa da mutane 5,000 aikin yi. 

Mene ne kiranka ga masu hannu da shuni da gwamnati a kan samar wa da matasa aikin yi?
Kirana ga masu hali shi ne, da su faɗaɗa tunaninsu, su riƙa saka dukiyarsu don ganin sun janye cincirindon waɗannan matasa da ba su da aikin yi. In dai har ni ka]ai da ba ni da komai zan samar wa da waɗannan matasa aiki yin, idan yanzu masu arzikinmu za su zo, su ɗauka, su yi irin waɗannan abubuwa, da tabas ni ina ganin shi zai kawo mana tsaro da zaman lafiya. Domin duk ranar da ɗan wani bai yi barci ba, ɗanka ma ba zai yi ba. Sannan kirana  ga matasa shi ne, bai kamata ba mutum ya tsaya ya ce wai sai ya yi karatun boko zai rayu.

Wannan abin ya wuce, kuma babban kuskure ne. Kuma ka ga ni dangina na uwa da uba babu ɗan kasuwa a ciki, dukkansu ma’aikatan gwamnati ne. Amma haka na ɓalle, na ‘yanta kaina. Don haka, ya kamata matashi ya tashi  ya yi  karatu don ya haska gabansa, amma ba don ya nemi aiki a gurin gwamnati ba. Kuma a lura, duk masu kuɗi a Nijeriya da jihar Kano za ka ga cewa ba ma’aikatan gwamnati ba ne, ‘yan kasuwa ne. Don haka su lura Duniya yanzu  ba a yayin aikin gwamnati.

Mun gode
Ni ma na gode ƙwarai da gaske.