Ranar Malamai Ta Duniya: Malamai na cikin wani hali a Kebbi

Daga Jamil Gulma a Kebbi

Ranar ranar 5 ga Oktoba na kowacce shekara aka tsayar a matsayin Ranar Malamai ta Duniya, inda a wurare daban-daban na faɗin duniya ake gudanar da bukukuwa da taruka da kuma lakcoci dangane da abin da ya shafi aikin koyarwa, inda a waɗansu wuraren har ma akan karrama waɗansu haziƙan malamai da suka cancanta.

Nijeriya ma ba a bar ta a baya ba wajen murnar zagayowar wannan ranar, sai dai ba wani abu na a-zo-a-gani da ake ganin an aiwatar bayan ranar ba a karatu illa malamai da ɗalibai suna zaune a gida.

Wakilin Manhaja a Jihar Kebbi ya zanta da waɗansu malamai da suka nemi a sakaya sunayensu bisa ga dalilan jin tsoron kada a ci zarafinsu ta hanyar riƙe albashinsu ko kuma sauyin wajen aikin da sai malami ya kwammace ya bar aikin da zuwa inda za a jefa shi, inda kusan duk maganarsu ta zo ɗaya akan rashin kyautatawa ga malamai da kuma irin riƙon sakainar kashi da wannan aikin na koyarwa ke fuskanta.

Malam Mu’azu Idris Argungu, wani tsohon malami ne a matakin firamare, wanda ya fito ya bayyana wa Manhaja cewa, ya soma aikin koyarwa a shekarar 1981 zuwa 2015, inda a lokacin da ya soma aikin yana karɓar Naira 145 a matsayin albashi kuma ya kan yi buƙatunsa a wadace. Amma bayan tafiya ta yi tafiya a sannu-sannu abubuwa suka soma lalacewa a ɓangaren koyarwa, wanda ya sanya malamai suka riƙa ƙaurace wa aikin, saboda rashin samun haƙƙoƙinsu daga gwamnati.

Idan aka yi la’akari da inda aka fito, za ka ga malami yana da ƙima a idon ɗalibi saɓanin yanzu. A baya malami idan ba zai zo makaranta, ba sai ya rubuta a rubuce da kuma dalilin raahin zuwansa ba, to amma yanzu siyasa ta shigo ta ɓata komai, babu malamai ƙwararru, sai dai kawai wani ɗan siyasa ya ɗaure wa wani ɗan shaye-shaye ko ɗan bangar siyasa gindi, babu azuzuwan karatu da kayan aiki ballantana haƙƙin malamai.

Yanzu haka a Jihar Kebbi gwamnati ta kasa biyan haƙƙoƙin malamai da suka haɗa da kuɗaɗen hutu da ƙarin girma. Idan aka ɗauki malami a mataki na bakwai, haka zai ƙare aikin a albashin matakin na bakwai har sai bayan ya ajiye aikin, wato ya yi ritaya, sannan a saka masa kuɗin matakin da ya ajiye aikin a riƙa biyan sa fansho. Haka zalika shi ma biyan fanshon ma ba ƙaramin bala’i ba ne a wajen malami, idan ya ajiye aikin.

Wani magidanci, wanda da ya ke da ’ya’ya huɗu a makaranta mai zaman kanta, Muhammadu Salisu, ya bayyana cewa, ganin irin malaman da a ke ɗauka aikin na koyarwa ne bai gamsu da shi ba, shi ya sa ya ƙi kai yaransa makarantar gwamnati. Bayan rashin ƙwararrun malamai, sannan kuma akwai halin ko oho da gwamnati ke yi wannan aikin na koyarwa, wanda shi ne ke sanya sai ka ga yaro ya kammala firame ko sakandare, amma bai san komai ba.

Ya yi kira ga gwamnati da ta mayar da makarantun horon malamai, waɗanda idan aka yi sa’a martabar malamai da ilmi za ta farfaɗo.

Hon. Muhammadu Magawata Aliero shi ne Kwamishinan Ilmi na Jihar Kebbi, wanda ya zanta da Wakilin Manhaja ta wayar tarho, inda ya bayyana cewa, Gwamnatin Jihar Kebbi a ƙarƙashin jagorancin Sanata Atiku Bagudu ta taka rawar gani sosai a ɓangaren ilmi, saboda shekarar da ta gabata ta ɗauki malaman sakandare 2,000 duk da ya ke dai ba za su isa ba, amma dai yin haka ya taimaka sosai wajen rage matsalar a wurare da dama.

Ya ce, an kuma gina tsangaya shida a garuruwa Argungu, Koko, Dakingari da Birnin Kebbi. Haka zalika an gina makarantun Fulani makiyaya (nomadic) 45 a faɗin jihar, wanda ba shakka kowa ya ga alfanunsa, don sun rage ya rage yara masu gararamba a titina barkatai.

Ya ƙara da cewa, bayan wannan gwamnati ta samu rahoton makarantun da ke cikin manyan garuruwa sun fi yawa, saboda haka gwamnati ta ɗauki dukkan sunayen malamai da wuraren da su ke aiki kuma da sunayen makarantu, don tantance makarantun da ba su malamai. Kuma a cewarsa, yanzu haka a na nan a na shirin canjin wuraren aiki na kai malamai inda babu malamai da yawa.

Kwamishinan ya ƙara da cewa, gwamnatin jihar tana nan tana shirin farfaɗo da martabar ilmi ta hanyar ɗaukar hanyoyin da duk suka kamata, sai dai ya ce, wannan aikin ba na gwamnati kaɗai ba ne; har da iyaye su ma suna da rawar da za su taka wajen ganin yaransu suna zuwa makaranta. 

A ƙauyen Kwalaye da ke Ƙaramar Hukumar Mulki ta Arewa, Wakilin Manhaja ya zanta da wani mazaunin garin, inda ya bayyana masa da cewa, yanzu haka malami ɗaya ne a makarantar ƙauyen kuma shi ma ɗan ƙauyen ne, yana mai cewa, duk da ya ke babu aji ko ɗaya, amma sun yi aikin kai da kai suka yi rumfar kara a matsayin ajin karatun ɗaiban.

Bugu da ƙari, a mafi yawanci sai dai mahukunta jihar sukan bai wa yaransu ko kuma bargar siyasa kwangilar zagaye makarantu ko wani gyara da ba shi da muhimmanci a maimakon a ɗauki malamai, saboda a kowace shekara sai waɗansu malamai sun ajiye aiki ko rasuwa ko kuma samun wani aikin da ya fi na koyarwa ko cikar shekarun ritaya, amma sai a bar wannan gurbin a banza.