Yadda batun kama ɗan Shah Rukh Khan bisa zargin tu’ammalli da ƙwayoyi ya zama

Daga AISHA ASAS

A ranar 3 ga watan Oktobar wanann shekara ofishin kula da miyagun ƙwayoyi ta Ƙasar Indiya, wato NCB, ta damƙe ɗan shahararren ɗan wasan kwaikwayon Indiya Shah Rukh Khan da laifin tu’amalli da miyagun ƙwayoyi.

Ofishin ya damqe shi ne a bakin taikon Mumbai, inda su ke gudanar da sharholiyarsu a cikin wani jirgin ruwa. Rahoton ya bayyana cewa, Ɗan na Shah Rukh ba shi kaɗai ne hukumar ta samu damar damqa ba, domin dai bikin na jin daɗi ne suke gabatarwa wanda ya ɗauki dubban matasa ‘yan’uwansa. Duk da cewa an tabbatar da cewa gayyatar Aryan Khan aka yi, ba shi ne uban taron ba.

Tuni dai wannan hukumar ta kwashe ɗimbin matasan ta isa dasu ofoshinta don gudanar da bincike kan miyagun ƙwayoyin da ta samu a cikin jirgin dasu ke shagalinsu a ciki.

A kwanakin baya ne aka yi raɗe-raɗin Aryan Khan na shirin zama jarumi, inda ake tunanin zai gabatar da ‘KAL HO NA HO’ kashi na biyu tare da ɗan Saif Ali Khan. Sai dai wata majiya ta tabbatar da kasancewar labarin shata-zube ta sanadiyyar kalaman baban nasa da ya ke cewa, “Ɗana ba shi da niyyar zama jarumi, domin ba shi da baiwar a tare da shi, kuma shi kansa ya fahimci hakan. Sannan ya sanar da ni ba ya son shiga harkar fim, saboda a kullum za a riƙa gwada bajintarsa da ta mahaifinsa.”

Sai dai duk da haka an tabbatar Aryan ma’aboci son sharholiya ne wanda ake ganin abin a matsayin gado.

Tuni dai wannan hukumar ta yi amfani da wayar Arya da wasu daga cikin abokaninsa, don zaƙulo masu hannu a miyagun ƙwayoyin. A wani rahoto da ya fito a jaridar ‘india today’ ya bayyana cewa, Ɗan na Jarumi Shah Rukh Khan ya samu tsayin shekara huɗu yana kwankwaɗar ƙwayoyi, har a zaman da yayi a Dubai da UK bai daina ba. Don haka hukumar ta tuhumi Arya da shan ƙwayoyi ne kawai, kasancewar ba a samu ƙwayar a tare da shi ba a lokacin kamen.

Wannan al’amari dai ya janyo cece-kuce tare da ruɗani a wannan masana’antar. Kasancewar mahaifinsa madubin dubawa a cikin masana’antar ya sanya kowa ke tofa albarkacin bakinsa. Kamar dai yadda aka sani, a cikin ko wace masana’anta akwai masoya da kuma maqiya. Hakan ce ta kasance ga Shah Rukh, da yawa sun tayashi alhini tare da jajanta masa, yayin da waɗansu su ka yi amfani da wannan damar don cin zarafinsa.

Fitaccen ɗan wasan ya samu kansa a jayayya tsakanin masoyansa da kuma waɗanda ke ganin abin da ɗan nasa yayi ba a ƙasa ya ɗauka ba. Kamar dai yadda fitacciyar jaruma Sherlyn Chopra ta bayyana cikin wani tsohon bidiyon da ta sake sakin sa, na wata tattaunawa da ita da aka yi can a shekarun baya. A cewarta “na girgiza matuƙa a lokacin da na ga miyagun ƙwayoyi a fatin da Shah Rukh ya shirya.

Har sai da na yi tsamanin nayi ɓatan kai ne. Na ga matan jarumai suna shaƙar kokin a banɗaki, a gaban madubi. A wurin naga kowa na shan abin da ya masa daɗi na daga miyagun ƙwayoyi. A lokacin da na hange Shah Rukh Khan da abokaninsa, na bar wurin cikin hanzari, domin bana son a alaƙantani da wannan aika-aika. A nan ne na fahimci cewa, ƙwaya ita ce bikin murna a Bollywood. Idan har ba za ka gabatar da ƙwaya a biki ba, to fa ba za ka samu jarumai a wurin ba.” Da wannan ta ke ganin barewa ba za ta yi gudu ba, kuma a ce ɗanta ya yi rairafe.

A wani vangare wasu jaruman sun nuna alhininsu tare da kai ziyara gidan jarumi Shah Rukh Khan don jajanta masa wannan iftilla’in da ya sameshi. Salman Khan, Alvira Agnihotri, Maheed Kapoor na cikin jerin jaruman da suka wanke ƙafa suka isa gidan Shah Rukh don jajanta masa. Duk da cewa wata majiyar ta tabbatar da jajen Kajool, Deepika Padukone, Rohit Shetty da kuma darakta Karan Johar ga jarumin.

Shah Rukh khan da Aryan

Wasu jaruman kuwa sun jajanta wa jarumin ta hanyar fallasa na su tu’amalli da miyagun ƙwayoyin. Kamar yadda jarumi Sanjay Dutt ya tabbatar wa manema labarai cewa, babu irin kayan maye na duniya da bai sha ba. Prateik Babbar shima ya bayyana cewa ya fara tu’amalli da miyagun ƙwayoyi tun yana ɗan shekara 13.

Wannan fallasa da wasu da yawa suka yi kan alaƙar su da ƙwayoyi ya bawa mutane damar canza kallon da suke yi wa masana’antar, ganin cewa masana’antar ta cika da ma’abuta shaye-shaye. Hakan ce ta sa ake ganin kaɗan ne daga cikin masana’antar ta Bollywood ne kawai basa shaye-shaye. Da wannan dalilin ne ya sanya masana’antar ta zama wani dandali na miyagun ƙwayoyi.

Kamar yadda Kangana Ranaut ta faɗa a lokacin da take bayyana tata alaƙar da miyagun ƙwayoyi, inda tace, kaso 99 bisa ɗari na masana’antar suna tu’amalli da miyagun ƙwayoyi. Ta kuma nemi jama’a a shafin Tuwitta da su nemi Ranveer Singh, Ranbir Kapoor, Ayan Mukerji, Vincky Kaushal da su bada jininsu don yin gwajin miyagun ƙwayoyi. Wannan bayyanin na ta ya biyo bayan surutan da akayi bayan fitar bidiyon da ta fitar da take fallasa kanta a matsayin ‘yar ƙwaya. Inda take cewa “na gudu daga gidanmu, sannan na zama jarumar fim cikin ‘yan shekaru, kuma na zama ‘yar ƙwaya.”

Yanzu haka dai Aryan na taimakon hukumar a binciken da take na gano masu hannu a waɗannan ƙwayoyin, kuma ya rubuta bayyanansa kan lamarin tsayin shafuka huɗu.

Da wannan bayyanan zan iya cewa masana’antar Bollywood na iya zama ta farko a masana’antun fina-fina da suka fi tu’amalli da miyagun ƙwayoyi. Wannan kuwa ba ƙaramar barazana bace ga masu tasowa a yanzu a masana’antar, domin dai kamar yadda muke gani, matasan yanzu sun fi na baya rashin hankali da kamun kai. Hakan zai sa su ruɓanya abin da magabatansu suka aikata matuƙar ba a yiwa abin tubkar hanci ba.