Ko ka san sakin aure guda biyar mafi tsada a duniya?

Labarin rabuwar Bill Gates da Melinda ya mamaye kafofin watsa labarai a ranar 3 ga Mayu. Wannan ya ba mutane da yawa mamaki, musamman ma bayan auren shekaru 27.

A yayin sanar da rabuwar tasu a shafin Manhajar Twitter, inda ma’auratan sun ce za su ci gaba da aikin haɗin gwiwar da su ke yi a gidauniyar Bill da Melinda Gates, wacce ke ɗaukar nauyin shirye-shiryen kiwon lafiya a duniya, daidaiton jinsi, ilimi, da sauran abubuwan.

Wannan ba shine farkon babban saki da za a sanar ba, domin a qasa ga wasu saki 5 mafi tsada a duniya:

Angelina Jolie da Brad Pitt – Dala miliyan 100:
Mutane sun shiga ruɗu a lokacin da labari ya ɓarke a watan Satumbar 2016 cewa Angelina Jolie ta nemi saki daga Brad Pitt bayan shekaru 11 suna tare. Bayan rabuwar su, lauyan ‘yar wasan ta ‘By the Sea’, Robert Offer, ya ce, shawarar da ta yanke na rabuwa don kwaciyar hankalin iyalinta ne. Brad ya fitar da wata sanarwa tasa ba da jimawa ba, yana gaya wa Mutane cwa, “Na yi matuƙar baƙin ciki da wannan, amma abin da ya fi muhimmanci yanzu shi ne kwanciyar hankalin ‘ya’yanmu.”

Ma’auratan, waɗanda suka raba yaransu shida, an ruwaito cewa, sun kashe sama da dala miliyan 1 a kuɗin shari’a kawai yayin da suke ƙoƙarin sasantawa, wanda hakan ya sanya sakin zamo wa daya daga cikin shari’ar saki mafi tsada a tarihin Hollywood. Kodayake har yanzu ba a cimma matsaya ba amma ana tsammanin Brad ya ba Angelia dala miliyan 100.

Tiger Woods da Elin Nordegren – Dala miliyan 110:
Biyan kuɗin saki da Tiger Woods ya yi ga tsohuwar matarsa Elin Nordegren na iya zama dala miliyan 110, a cewar HuffPost. Wata majiya da ke kusa da lamarin ta ce Elin na son isassun kudin da za ta kula da rayuwarta ta jin dadi, amma ba ta yi ƙoƙarin ɗauke shi a kan kowane dinari da za ta iya ba. A watan Afrilu na 2011, Elin ta ba da rahoton cikakken kula da ’ya’yansu akan dala miliyan 750.
Tiger ya yarda da cewa yana da al’amuran da yawa, kuma ma’auratan sun yanke shawarar saki bayan shekaru shida tare a cikin 2010.

Michael Jordan da Juanita banoy – Dala miliyan 168:
Bayan rabuwar aurensu, Juanita a gwargwadon rahoto ta karɓi yarjejeniyar saki kan dala miliyan 168, wanda har yanzu yana ɗaya daga cikin mafi girma a tarihin wasanni. Michael Jordan da Juanita banoy sun gabatar da takardar saki a 2002 bayan sun yi aure kusan shekaru ashirin. Ma’auratan sun yi ƙoƙari su daidaita bambance-bambancen su na tsawon shekaru huɗu kafin su ba da sanarwa game da rabuwarsu a 2006. Ko a yau, yarjejeniyar sakin Michael Jordan da Juanita banoy ana ɗaukarsu ɗayan mafi tsadar rabuwar aure na kuɗi a tarihin wasanni.

Rupert Murdoch da Maria Torb – Dala biliyan 1.7:
Attajirin nan mai yaɗa labarai Rupert Murdoch da ‘yar jarida Maria Torb sun yi aure tsawon shekaru 31 kuma suna da yara uku tare. Amma ma’auratan suna da bambancin shirye-shirye game da lokacin da Murdoch zai yi ritaya, kuma sun amince da rabuwar aurensu a 1998. Babu wani cikakken bayanin rabuwar auren, amma ana raɗe-raɗin cewa Maria ta karɓi dala biliyan 1.7.

Dukansu bangarorin biyu kamar sun ci gaba da lafiyar da rayuwarsu, domin Rupert ya auri Wendi Deng kwanaki 17 bayan kisan auren, yayin da Maria ta auri William Mann watanni shida bayan da aka ruwaito a cewar Jaridar ‘Economic Times’.

Jeff Bezos da MacKenzie Bezos – Dala Biliyan 38:
A watan Afrilun 2019, mai kamfanin Amazon, babban dillalin yanar gizo a duniya, ya ce, a cikin shigar da qara cewa, kashi 4 na fitattun hannayen jarinsa ko miliyan 19.7 za a yi rijistarsa da sunan MacKenzie Bezos bayan amincewar kotu na rabuwar aurensu.

Ma’auratan sun sanar da shirinsu na yin saki a cikin sanarwar haxin gwiwa ta Manhajar Twitter a watan Janairu, lamarin da ya sa wasu suka damu cewa Jeff Bezos na iya faɗawa cikin rage ƙarfin kamfanin Amazon ko kuma shi ko MacKenzie za su zubar da wani babban matsayi a kamfanin.

Ba abin mamaki ba ne cewa sakin dala biliyan 38 ya sanya MacKenzie a matsayi na 4 a jerin mata masu kuɗi na Duniya.
A halin yanzu shine kisan aure mafi tsada a duniya, amma har yanzu Bill da Melinda Gates ba su iya yin nasara ba. Wannan na zuwa ne bayan wata magana da ake zargi da tsohuwar mai gabatar da labarai ta Fod News, Lauren Sanchez, ma’auratan sun kawo ƙarshen aurensu na shekaru 25.

Kuɗin da aka kashe na Bill da Melinda Gates ba a ba da sanarwar sakin ba tukuna, duk da haka, yana iya zama mafi tsada.