Sai Yaushe miji da mata za su gane zaman aure taimakemeniya ne?

Daga AMINA YUSUF ALI

Barkan mu da saduwa a filin Zamantakewa na jaridarku mai farin jini ta Manhaja. A wannan mako muna tafe ne da bayani a kan yadda ma’aurata suka gaza fahimtar zaman aure, zaman taimakekeniya ne wato cuɗe ni, in cuɗe ka. Wato aikin gayya ko ‘team work’ da ingilisi kenan. A makon da ya gabata, mun bayyana yadda mata suke nuna damuwa da ƙorafi idan maza sun tafi sun bar su da wahalhalun gida. Wannan na nuna rashin uzuri ne domin ko dai sun tafi nema ko akwai dalili. Duk da dai akwai masu yawon mara amfani. Zaman aure sai dai mu ce kawai Allah ya iya mana. A sha karatu lafiya.

Kamar yadda Hausawa kan ce: ‘Hannu guda ba ya ɗaukar jinka’, haka al’amarin yake. Musamman ma idan aka duba zaman aure a yau da tarbiyyar yara. Dole sai wancan ya kama can, wannan ya kama can. Hanyoyin da za a bi don samun wannan haɗin kai da taimakekeniyar da za a kai ga nasara sun haɗa da: 

Haɗin kai tsakanin mata da miji: Haɗin kai yana da matuƙar muhimmanci. Hasali ma shi ne ya sa muke ganin auren wasu ƙabilu yana daɗewa saɓanin na Hausawa. Haɗin kai shi yake kawo taimakekeniya. Ka haɗa kai da matarka ko matanka domin samun kwanciyar rai cikin gida.

Haka tausayawa ma ita ma wani jigo ne a cikin taimakon. Idan ba a tausaya wa juna, ba yadda za a yi a taimaki juna. Kamar idan mace tana da ciki, dole aikin gida zai mata wahala. Ko ba ka taya ta aikin gida ba, to ka taimaka ka ɗauko mata mai taya ta ko ‘yar aiki ko a danginka ko nata. Idan ba ka da halin mai taya ta, kawai sai ka yi ƙoƙari ka rage mata wasu ayyukan da ba su zama dole ba don ta dinga samun hutu.

Misali kamar kana zaune ka ƙwalla mata kira ta kawo maka ruwa ko ka dawo tsakar dare ka tashe ta ta dafa maka wani abu, ko kai ruwan wanka da sauransu. Kamar da azumi ma, ka yi ta kawo mata abokai shan ruwa tana bautar girki. Ɗanuwa wannan ba dole ba ne. Idan da wadata ma za ka iya oda ka bar ta ta huta.

Mun san a farkon kusan kowanne aure, ma’aurata suna cike da shauƙin soyayya. Kawunansu a haɗe suke. Kowa yana Allah-Allah ya faranta ran ɗan’uwansa ta hanyar taimaka masa. Wani angon ma ba zai bar mace ta shiga kicin ita kaɗai ba, sai ya taya ta. To amma daga zarar gumu ta yi gumu, sai kuma a fara samun rabuwar ra’ayi. Da rashin son waccan taimakejeniyar. Kuma abin dariyar shi ne, a lokacin da shekarun auren naku suke tafiya, a lokacin kuma kuke ƙara buƙatar haɗa kai da taimakon juna.

Wajen kashe ku]i ma ana samun rashin jituwa. Ya kamata mace ma ta dinga taimakowa da abinda ya sawwaƙa idan tana da shi. Sannan kai ma kada a bar ta ita kaɗai da nauyi don musulunci bai ce haka ba.

Ke kuma duk da ba ke kike nemowa ba, ki ɗauki duk wani abinda ya kawo da muhimmanci. Kada ki yi masa wasarere da kayan abinci a sace ko a ɓata. Ki guji yin almubazzaranci a kan kayansa. Ki zama mai tattali kamar ke kika saya.

Sannan wasu lokutan maza suna da wani abu. Ita mace ita ke yin girki da kula da sauran abubuwann gida. Amma idan ya tashi sayayyarsa kayan girki ko na gida, kawai sai dai ya sayo ya kawo. Ba zai saurare ta ba sam. Kuma ita ta san abinda ya fi kyau da ƙarko a cikin kayan aikin gida. Wannan ma rashin haɗin kai ne.

Haka akwai tarbiyya kada a sakar wa uwa ita kaƙai. Uba ma Allah ya ɗora masa ba ita ɗaya ba. Haka wasu iyayen mata idan miji ba ya nan, ba sa iya taɓuka komai da yaransu. Sun bari sun raina su. Su ma ya kamata su ƙara dagewa.

Haka akwai lokaci. Duk da dai dukkanmu muna da lokacin da muke yin abubuwa. Ba tsari a ce mijinki yana fita da sassafe ki kasa tashi ki shirya masa abincin safe mai kyau wai saboda bacci. Sai ki ga wani namiji da sassafe zai fita ya dinga sayen ƙosai ko abinci bayan yana da halin yadda za a dafa masa a gida. Ko shayi ya kamata a ce an ]an tafasa masa da daddare ya sha da safe. Wata ko yaranta ba ta da lokacin yi musu abincin makaranta. Haka za su fice da yunwa sai dai a ba su kuɗin makaranta. 

Har yanzu dai muna batun lokaci. Kai ma namiji, duk yadda aiki ya cunkushemaka, samu lokacin iyalinka. Ka wuni aiki a ofis, maimakon ka dawo gida ka ba ta nata lokacin, sai ka ci abinci, ka yi wanka, ka sake ficewa majalisa ko wani wajen. Ba kai za ka dawo ba sai dare. Ka sani wannan lokacin yana da matuƙar mahimmanci a kan haɗin kai tsakaninka da kai da iyalanka. Sai ka ba ta lokaci sannan za ka san damuwarta, ka san me gidan naka ke ciki, da sauransu.

Ka ɗauki gidan aurenka kamar kamfaninka da kake so ya bunƙasa. Hakan ba zai faru idan ba a yin tarurruka daga lokaci zuwa lokaci tsakaninka da ma’aikatanka masu gudanar da shi? To shi ma gidanka kai ne manaja. Sai kana bibiya da tuntuɓa don tabbatar da komai na tafiya yadda ya kamata.  Haka ka sani, rashin ba mata da ‘ya’yanka lokaci yana rage muku shaƙuwa da nesantar da ku da juna.

Girmamawa da yaba wa juna shi ma yana ƙaro haɗin kai tsakanin ma’aurata. Ki yaba wa ƙoƙarinsa a kan abinda ya kawo. Allah ne kaɗai ya san irin wahalar da ya sha kafin ya samo wannan abinda ya shigo da shi. Amma ya ba ki, kin raina. Ko kin ƙi gode masa. Da gode masa kika yi ai da ya fi samun ƙwarin gwiwar nemo wani ya kawo miki.

Kai ma ka tausaya kuma ka yaba mata. Aikin gidan nan ba sauƙi ba ne. Wallahi mata na ƙoƙari. Ko rainon nan fa aiki ne babba. Ko da azumi ka dubi yadda kowa ke neman wajen sanyi don ya sarara. Amma su mata sanda azumi ya fi wahala gab da faɗuwar rana, lokacin suke fitowa su durfafi wuta gadan-gadan. Wannan ya isa abin tausayi. Kuma abin a jinjina musu. Shawartar juna: shi ma yana daga cikin abinda yake ƙaro haɗin kan ma’aurata. A ba wa kowa dama a nemi shawararsa kafin a yanke hukunci a wani abu.

Sannan kuma a dinga tallafawa da ƙarfafar juna a al’amuran zaman tare. An san mace Allah ya ɗora wa kula da gida da yara da sauran aiki.  Mance da masu ba da fatawar cewa shi yin girki ba dole ba ne. To idan ba ki yi ba wa zai yi? Shi zai baro sana’a ko aikin da yake yi ya dinga miki girki da raino? Kuma idan ya jaɓe a gida bai fita ya nemo ba, me za ku ci? Haka idan ya fita, ko ma ya yi tafiya wani garin, wajibi ki kula masa da kanki da dukiyarsa da gidansa da ‘ya’yansa da komai ma nasa.

A zamanin Annanbi SAW mata sun taɓa yin taro a kan yadda maza suke tafiya da akasarin lada. Suna zuwa masallatai, suna zuwa jihadi, amma mata suna gida. Manzon SAW ya bayyana musu cewa, ai su mata Allah ya haɗa musu dukkan wannan bautar da maza suke yi ya dunƙule musu shi gabaɗaya a zaman aure. Idan ba sa nan, ya umarci mata su tsare wa mazajensu kawunansu da dukiyoyinsu sai Allah ya ba su lada kwatankwacin na mazan su ma. 

Haka kai ma miji, nauyin gida naka ne. Ci, sha, sutura, lafiya, da sauran abubuwa. Ba wani zame-zame kai Allah ya ce ka yi. Ko da matarka miloniya ce, sai dai ita ce ta sauke maka ta yafe. 

To amma fa duk da haka, ba za a ce kawai don wannan nauyin shari’a ne a kan mutum ba a ce dole hakan zai yi. Kamar yadda na faɗa, aure fa zaman taimako ne da taimakekeniya. Ba wai a ce kawai shikenan wani ba zai iya taimaka wa wani da ɓangarensa ba. Misali, mace idan tana samu, za ta iya taimaka wa mijinta ta rage masa wasu wahalhalun na gida. Musamman idan ba shi da ƙarfi sosai.

Haka zalika, shi ma miji zai iya taimaka wa mace da aikin gida musamman idan aikinsa na nema yana ba shi rarar lokaci sosai. Meye a ciki, Yayana? Ka  taya ta wankin yara haka, ko wankan yara, ko dai wani abun. Ita ma ta samu ta rage wahalar da take ciki. Hakan yana ƙara muku soyayya sosai.

Don haka, abinda ya kamata ma’aurata su yi shi ne, sai a haɗa ƙarfi da ƙarfe su tabbatar da rayuwar auren su ta yi ƙarko. A manta da zargi da nuna wa juna yatsa da ganin baiken juna. Kowa na ganin ɗayan ne da laifi ba shi ba. Idan aka fahimci ba aikin mutum ɗaya ba ne sai an yi taimakekeniya sannan za a samu abinda ake so, sannan za a ga komai ya yi dai-dai.

Domin a je, a dawo dai, bori ɗaya kuke wa tsafi. Manufarku guda ce ta samun nasara a rayuwar aurenku. Amma sai ka rasa dalilin da miji da mata ko kishiyoyi za su dinga adawa da juna, maimakon haɗa kai. Wannan ƙarfi da lokacin da za ku  yi amfani da su wajen yaƙar juna, ku haɗa shi wajen tallafa wa juna sai ku ga Allah ya dube ku ya sa albarka a rayuwarku kuma ya ba ku nasara.