Tattaunawa ta musamman da Sheikh Nazifi Alkarmawy

Daga BILKISU YUSUF ALI

Sheikh Nazifi Alkarmawy fitaccen malami ne kuma limamin masallacin Juma’a, sannan marubuci, wanda ya yi fice wurin faɗakar da al’umma kan su tausaya wa mata, su kuma kyautata mu su. Wannan ya ƙara wa malamin farin jini, musamman a wurin mata iyayen giji, inda za ka yi ta ganin wani sashe na wa’azuzzukansa yana yawo a kafofin sadarwa. Wakiliyar Blueprint Manhaja, Bilkisu Yusuf Ali, ta samu tattaunawa da shi. Ga yadda hirar ta kasance:

Za mu so mu ji tarihinka.
Sunana Sheikh Muhammad Abdulwahid Muhammad Nazifi ɗan Shehi Muhammad Auwal da aka fi sani da shehu Malam Ƙarami ɗan Shehu Malam Khidru. Ni Bakano ne kuma Batijjane, an fi sani na da Alƙarmawy. An haife ni a Kano a unguwar Cheɗiyar ‘Yan Gurasa Jakara da ke Ƙaramar Hukumar Dala. Mun yi karatu a gida nan wurin Malam Babban a Alƙur’ani da littattafai, sannan mun je wurin wasu malamai kamar dai yadda ya ke a manyan gidajen malamai. Malamina na farko shi ne shaihina, Shehu Malam Ƙarami. Nan na yi karatun ulumul islamiyya tun daga Ahalari da Ƙawa’idi da Iziyya; mu na cikin Risala ya yi wafati. Bayan wafatinsa sai babban yayanmu, halifansa, ya ci gaba. Sannan tun yana raye ya kai ni wurin amininsa wani babban malamai Shehu Abdulmajid na shehu Malam Salga shi ma na je na yi karatu a wajensa ina tare da shi har ya yi wafati. Akwai Shehu Malam Abdullahi da aka fi sani da Shehu mai sunan Malam akwai Shehu Malam Saleh Muhamudu Sanka akwai Shehu malam Hamza ɗan Liman malam Ishaƙa Ƙanƙara malam Aminu Sanda a Jakara. Duk da suna da yawa amma dai waɗannan sune a farko kuma muna tare da su har rasuwarsu.

Na shiga makarantar Firamare ta Annahadatu a Gwammaja sai makarantar Aliya na yi sakandare na zarce da karatu na samu Diploma a Bayero, na yi digirina nan ma a Bayero duk a ɓangaren Arabiya. Daga nan sai na shagala da rubuce-rubuce da koyarwa. Na yi rubuce-rubuce da yawan gaske misali. Ma fi yawan rubuce rubuce na na sira ne wato tarihin Annabi Muhammad (SAW) da yabonsa

Sira na rubuta alfairul midrar fi zikiri fara’idu nabiyyil mukhtar, Risalati sa’adati wanda shi yana magana ne akan falalar maulidi, farhul a hibbati fi madhi sayyidil ummati, alfiyyatil nazifiyya baito ci ne dubu a kan yabon Annabi, dhiya’ul fu’adi shi ma babban littafi ne shafinsa dubbai ne, a Arabiyya kuma akwai littafina wanda project ne na makaranta amma saboda kyansa da karvuwarsa ya zama an buɗa shi ana amfani da shi ako ina jami’oi shi kuma akwai wani littafi da Shehu Ibrahim ya yi baitoci ne kan fanni tasrifi na ilimin Arabiya wannan baitocin na yi bincike akai na yi tahalili da tasirif fakkul aglal, Annailil ta shauwuf ila haƙa’iƙi ilmul tasawwuf wanda yake magana akan tasawwuf duk littattafana an yi shi a kan tijjaniya. Akwai ma wani littafi tafsiratul ihwani bi mahiyatu ɗariƙatul Ahmadu tijjani da ya tare duk hukunce- hukuncen duk ɗariƙar Shehu Ahmadu Tijjani da abubuwa na alkhairu wannan littafin hatta a zawiyar Shehu Ahmadu Tjjani a Maroko an sa shi an karanta shi. A yanzu muna ta ƙoƙarin fassara shi da Hausa da Turanci. Ina da littafi sun fi ɗari wasu an kammala wasu ba a kammala ba.

Me ya ja hankalinka ka yi ire-iren waɗannan litattafai fiye da ɗari?
Na farko dai akwai sha’awa ina jin daɗin na ga ina rubutu. Sai na biyu Babu rubuce rubucen da yawa musamman a abin da ya shafi sufanci don hala ake samun shigar wasu abubuwa da ba dai-dai ba, don haka ma muka yi shawarar yin su da Hausa don ci gaban al’ummarmu burinmu dai kowa ya amfana.

Ka fita waje don karatu?
Ban taɓa zuwa ko ina karatu ba duk karance-karancena da neman ilimin a anan Kano na yi su.

Ziyara fa?
Na je garuruwa daban daban, na je ziyarar shugaba sallallahu alaihi wasallam na yi hajji na je Maroko ziyarar Shehu Ahamadu Tijjani na je Libya mun je Senegal da Ghana da Niger da Chadi da Mali, gaskiya dai duk garuruwannan na Afrika mun je ziyara wani buɗe masallatai ko wa’azizizzka da tarurruka kamar na mauludi da sauransu.

Waye muƙaddaminka?
Shehu nawa mahaifina shehu Malam Ƙarami shi ya ba ni ɗariƙa tun tuntini. Sai kuma tsari irin nasu watarana za a yi zikirin juma’a sai ya kirawo ni ya kira wannan halifan nasa ya ce min ya yi min tajdidi. Wannan da na gani bayan ya yi wafati shi ya koma Shehina a wurinsa na yi komai na yi tarbiyatul azkar.

Mene ne Tarbiyatul Azkar?
Duk wanda ya yi tarbiyatul azkar za ki same shi ma fi biyyaya ga Allah amma in har ki ka sami saɓanin haka to ba a yi ba ne duk wanda ya san Allah biyayya yake yi masa ba ya yin kowanne abu da zai saɓa masa komai ƙanƙanta.

Ya ka ke ganin Faira?
Faidha wata falla ce ta samu shi ne samun komai cikin falala na zahiri da baɗini. Shehu Tijjani mai ɗariƙar Tijjaniya shi ya faɗa ya ce Faila za ta zo kwararar alheri zai zo amma ta wasƙar annabi ta hannun jikansa shi kuma Shehu Tijjani ya ce ba za ta bayyana ba yanzu a hannunmu sai bayan mun shuɗe za ta zo a hannun ɗaya daga cikin almajiranmu. A ƙarshe ta bayyana a hannun Maulanmu Shehi Ibrahim shi ne ma’abocinta magana ce kuma sirri ne ba fararre ba kuma voyayye ba bin da ake nufi shi ne bin Allah da samun cikakken imani da kamalar bin Allah da kiyaye sunnonin manzan Allah sannan za a samu komai cikin sauƙi duk abin da ake gani cikin sauƙi falalar fairadha kenan faira alheri ne da bin Allah duk lokacin da aka ga wani abu wanda ya saɓa wa bin Allah ba sunnar Annabi a ciki to shaƙiyanzi ne wannan amma ba faira ba ne maƙiyan faira ne suke sharri

Ya ka ke ganin muhimmancin haɗin kai?
Haɗin kai yana da matuƙar muhimmancin ko da kuwa tsakanin waɗanda suke da bambancin ɗariƙu ne bare wanda ku ke ɗariƙa ɗaya. Amma kin san duk abin da aka bar Allah a ciki sai ki ga irin waɗannan saɓani na gittawa, haɗin kai da rashin soyayya ya samu. Abin da Shehu ya tabbatar mana duk wani saɓani ba a yin sa cikin Allah ko cikin manzon Allah ko cikin Shehu kana son Allah ina son Allah kana son manzon Allah ina son Manzon Allah to me ya kawo saɓani? Don haka in aka ga saɓani to ba kan Allah da manzo ba ne sai kan duniya da shaiɗan su ke haddasa rigingimu. a tsakanin Tijjanawa da ƙadirawa duk babu wannan yanzu babu dalilin da zai sa baƙadire zai ce ba ya son Batijjane domin yana son Shehinka y a yarda da shi kai ma kana son shehinsa ka yarda da shi kuma waliyyin Allah ne irin shaihin ka. Kai a ɗaya ɗangaren yanzu duk wannan saɓanin ya kau kowa ya gane sunna ake son ɗabbaƙawa ita kowa ke bi sallah da duk al’amura na addininmu iri ɗaya don haka rigimar me za mu yi?

A wa’azuzzukanka ka na yawan karkata kan a tausaya wa mata me ne dalili?
Ana so a tausasawa mata domin mata sune tushe sune suke samar da alheri ko matsala sannan Annabi Muhammad (SAW) yana cewa zuciya tana son duk wanda ya kyautata mata don haka in an kyautata wa mata to su kuma za su kyautata idan aka kyautata mata za ta yi biyayya za ta yi soyayya ga miji idan ta yi biyayya Allah zai jiɓanci lamarinta don haka za ta haifi ‘ya’yaye gyararru masu albarka maza da mata. Wannan tushen ake manta na samun al’umma ta gari don haka dole mu ce a girmma mata a kyautata musu. Manzan Allah sallahu alaihi wasallam abin da ya umarce mu kenan a rinƙa wasilcin alheri ga mata a yi musu alheri a nusar da su abin da zai amfanar da su a kawar da su akan abin da zai cutar da su, don mata suna da rauni guda biyu suna da rauni a ahankali sannan suna da rauni a addini suna da rauni a jiki misali in an yi wa namiji bulala ɗari ya shanye to qila in an yi wa mace ta rasu saboda jikinta yana da rauni yar alallaɓa ce.

Hatta a itatuwa akwai mata za ki ga ƙatotuwar bishiya za ki ga an fara sararta tuɓus-tuɓus sai ki ga nan da nan an gama to wannan mace ce amma sai ki ga ‘yar bishiya ƙarama amma a ɗau lokaci ana sara sai an ji jiki kafin a gama wannan namiji ne. Kin ga rauni na jiki rauni na addini namiji cikakken wata yake yi yana addini amma mace tana samun giɓi lokacin al’ada haka a batun hankali mace tana da rauni ƙarfin rai ɗan ƙaramin vacin rai sai ta shiga damuwa. Shi yasa ake son a kai mace wurin jin daɗi idan ta samu mijin da ba ya tausaya mata marar imani yau ya ɓata mata rai, gobe ya ɓata mata rai, sai ta fara fargaba ‘yar shekara ishirin in dai za ta yi shekara da rabi a ɓacin rai in kin ganta za ki ce yar shekara hamsin ce, tsofewa take yi, ta fattatake ta fita hayyacinta. Amma in ki ka ga mace tana samun kulawa ‘yar shekara hamsin zuwa sittin sai ki ce ba ta fi talatin da ‘yan kai ba saboda akwai nutsuwa da kulawa. Don haka sai ta mace a jin daɗi haƙƙin na al’umma ne don a samu al’umma ta gari. Amma ki ga an samu ‘ya’ya dolaye daƙiƙai suna shaye- shaye da ɗauke- ɗauke ba sa ganin mutuncin kowa sai rigima in aka tona mijinta bai mutuntata ba ba ta ji daɗinsa. Amma in ya mutuntata ta aka samu akasin haka to ba ƙaramar baƙar ƙaddara ce ba. don haka tunda al’umma Muhammadiyya ake so ta zama gyararriya to labudda ne sai an tabbatar an kula da mata. Haka saki kullum muke ta cewa a yi haƙuri Annabi Muhammadu (SAW) y a ce karya mace shi ne saki don haka wa zai so a karya shi.

Abin da ya ke wajibi shi ne mutum ya saita matarsa akan biyayyarsa babu wanda a ka ce a bi shi amma Allah ya ce ‘ya’ya su bi iyaye kuma idan uba yana son ‘yayansa su samu alheri zai ce ku bi ni ku yi min hidima wannan sirri ne shi da ‘ya’yansa. Amma Shehi zai ce da almajirai ku bi ni ku yi min hidima?ko ko wani oga? Amma shi miji an faɗa masa ya faɗa wa matarsa ta bi shi kada ta saɓa masa ya faɗa mata akul ki ka saɓa min ki ka ha’ince ni don yanzu yanzu Allah zai tarwatsa lamarinki da abin da kika haifa don haka haƙƙin miji ne ya saita mace sannan ta yi haƙuri. In har miji fa bai zama uba ba to bai zama cikakken miji ba, sai miji ya riƙi matarsa kamar shi ya haife ta idan kuma mace ta yi biyayya to za a dace. Duk mai bayaewa Allah ba ya hana shi muradinsa.

To akwai wata sana’a da ake yi?
Ai ni babbar sana’ata ita ce koyarwa sai kuma sallah ga masallacina nan na juma’a ni nake ɗaukar nauyin komai ni ko kuɗi da ake bayarwa na limamai ban taɓa karɓa ba ba na so. Na san kuma akwai falalar Allah kuma ina rubuce rubuce na littattafai ana kai su ko’ina a duniya kuma akwai makaranta tawa ta gida. Gidan nan duk inda ki ka ɓullo makaranta ce ina da makaranta ga dai ta zaure wadda muka gada ga kuma ta Ƙur’ani ana nan ana yi ga kuma makarantar zamani wadda na sa sunan Hajiyarmu markazil ƙarmawi. Markazul dirasatil arabiyya lil Sayyada Hajara cikin makarantar akwai nursery da firamae da sakandare sannan akwai masallaci da muka saka wa sunan Malam Ƙarami wanda muka gina almajirai daga koina daga garuruwa daban-daban sanna ana almajirci dai dai gwargwado hatta yara suma suna ta ƙoƙari yarona Halifa shi ma yana da makaranta wadda ya sa da sunana Alnazif Acadamia.

Me ne burinka na rayuwa?
Burina na gama da duniyar nan lafiya zuciya ta sadu da abin da take buqata Annabi Muhammadu (SAW) ina da littafi ya kai ɗari amma a ɗarin nan kusan dukkansu Manzon Allah ne a ciki don shi ne a zuciya babu abin da take so irin manzon Allah ma fi yawan maganat annabi ne ni ba abin da nake jin daɗi kamar Annabi ni ba ni da buri ko sha’awa sai ta Shugaba Sallallahu alaihi wasallam.

Fatanka fa?
Fatana shi ne Allah ya ƙara mana lafiya ina da rubuce- rubuce da na fara ban gama ba ina son na kammala su, duk da dole za mu bar wani ba mu gama ba sai dai a ƙara sa maka muna fatan abin da mu ka fara ’ya’yanmu su ƙarasa ma na.