Kano: Bichi za ta rabauta da ginin zamani na makarantu huɗu

Spread the love

A fannin cigaba da ɗora ayyukan alheri na raya ƙasa da gina al’umma dake ta wanzuwa a Ƙaramar Hukumar Bichi ƙarƙashin wakilcin Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar yankin, Alhaji Abubakar Kabir Abubakar Bichi, ya saka ɗambar sabunta ginin wasu makarantu huɗu a garin Bichi.

Jami’ar Yaɗa Labarai ta yankin, Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo, ta rawaito, marakarantun sun haɗa da; GASS Sabon Layi, Ciranci Science and Mathematics Primary School, Makarantar Firamare ta Ɗanzabuwa da Makarantar Firamare ta Saye, kuma dukkan waɗannan makarantu tuni aka fara gudanar da aikin.

Makarantun za su samu ingantaccen ginin zamani mai kyau da ƙarko da kuma kayan koyo da koyarwa tamkar makarantar Hagagawa Special Primary School da Ɗanmajalisar Tarayyar ya zamanantar a kwanakin baya.

Sakataren Sashen Ilimi na yankin, Alhaji Ishaq Muhammad, ya bayyana irin wannan aiki da Ɗanmajalisar, Alhaji Abubakar Kabir Abubakar yake kaiwa a ƙaramar hukumar, haƙiƙa zai taimaka wajen cigaban ilimin yaran yankin tare da bunƙasar garin Bichi baki ɗaya.Ya kuma ce, duka makarantun huɗu da aka fara ayyukan sabunta su, ana sa ran kammala su a cikin watanni shida.

“Wannan ɗanmajalisa namu mai albarka, muna masa godiya; Allah ya saka masa da alheri ya ƙara masa buɗi ya ƙara ba shi kujerar da ta fi wadda yake a kai! Alfarmar Sayyadina Rasulillahi SAW a bisa taimakon da yake wa Ƙaramar Hukumar Bichi.” Alhaji Ishaq Muhammad.

Kazalika, ya ce, kamar yadda aka san mutanen Bichi da kishi da ƙwazo, ya bayyana kyakkyawan haɗin kai da aka samu tsakanin Ɗanmajalisar, da Shugaban karamar hukumar, Alhaji Hamza Sule Maifata ya haifar da bunƙasar garin fiye da zato duba da jajircewar Shugaban ƙaramar hukumar wajen tabbatar da cewa an gudanar da aikin da Ɗanmajalisar ya kawo cikin nasara.

“Wannan aiki bai gama cika ba sai da ƙoƙarin Shugaban Ƙaramar Hukumar Bichi, Alhaji Hamza Sule Maifata, domin ya tsaya tsayin daka wajen tabbatar da wannan aiki da aka kawo, an fara shi. Sannan da injiniyoyi suka zo ya karɓe su hannu bibiyu, kana ya haɗa tim na jami’an tsaro tare da mu Hukumar Ilimin Baiɗaya na Ƙaramar Hukumar Bichi, muka tabbatar da an yi aikin rushe waɗannan makarantu guda 4 da za a sabunta, an gama.

Yanzu haka an fitar da fawundeshan kodayaushe za su fara ɗora bulo; saboda haka muna gode musu muna musu addu’a Allah ya ƙara haɗa kawunansu ya tallafi hannayensu domin bunƙasar cigaban Bichi”, Alhaji Ishaq Muhammad.

By Babaji

Leave a Reply