
Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne a Jihar Zamfara, sun yi garkuwa da ɗalibai guda bakwai na makarantar Polytechnic ta Tarayya da ke Ƙaramar Hukumar Ƙauran Namoda bayan sun kai hari gidansu da ke kusa da unguwar Low-Cost a cikin garin Ƙauran Namoda.
Shugaban ƙaramar hukumar, Mannir Haidara Ƙaura ne ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce jami’an tsaro sun fara gudanar da ayyukan ceto domin tabbatar da dawowar ɗaliban cikin ƙoshin lafiya.
Wani dalibi mai suna Ibrahim Ahmad ya bayyana cewa ɗaya daga cikin waɗanda aka sace ya tsere daga hannun masu garkuwar, yayin da dalibai shida da suka haɗa maza uku da mata uku suke cigaba da zama a hannun masu garkuwa da mutanen.
A wani ɓangare kuwa, ƙungiyar Concerned Citizens of Ƙaura Namoda ta nuna damuwa kan taɓarɓarewar tsaro a yankin, tana mai zargin wani shugaban ‘yan bindiga da aka fi sani da Kachalla Bello Ɗan-Sadiya da jagorantar hare-haren.
Kungiyar ta kuma tunatar da wasu hare-haren sace mutane da suka gabata, ciki har da sace manyan malamai biyu da wasu mazauna yankin, tana mai tambayar dalilin da ya sa har yanzu ba a samu nasarar kubutar da su ba.
Rundunar ‘Yan sandan jihar ta tabbatar da sace ɗaliban ta bakin Kakakinta, Yazid Abubakar, inda ya ce jami’an tsaro sun ƙara ƙaimi wajen gudanar da aikin ceto wadanda ɗaliban.
