Ba ni da masaniya a kan takarar Abba – Ɗahiru Mangal

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Ko alama bani da masaniya alkan wannan takararta Abba, hasalima bana ra’ayin wani daga cikin ahalina ya shiga siyasa, kawai dai babu yadda za kayi idan Allah yayi tsarinsa

Waɗannan kalamai sun fito daga bakin hamshaƙin ɗan kasuwa kuma jigo a jam’iyar APC, Alhaji Ɗahiru Barau Mangal da yake tsokaci akan takarar ɗaya daga cikin ɗan sa Barista Abba Ɗahiru Mangal.

‎Yace “Allah ne ya ƙaddara wannan yaro shine za’a bawa tikitin takarar nan to ni babu abinda zanice face ince masa sai dai Allah ya yi masa jagora,”

‎Mangal yayi fatan idan Allah ya bashi kujerar Allah ya dafa masa yadda zai jagorancin al’umma har ya gamsar dasu duk da munsan Allah ne kaɗai ka iya yima ɗan Adam dai-dai.

‎Alhaji Ɗahiru Mangal ya ce “yadda al’ummar Katsina suke nuna masu goyan bayansu muna fatan hakan ya ɗore kuma baza kuji kunya ba”,Inji Mangal.

Barista Abba Dahiru Mangal ya zama ɗan takarar kujerar majalisar wakilai a Katsina ta tsakiya a ƙarƙashin jam’iyar APC.

Bayan gudanar da sasanci wanda ke kan kujerar Hon Sani Ɗanlami da shi da wasu yan takara suka bar ma Barista Abba.

By ukarofi